NOVEL SHARES -
haidar abin da ya faɗa ba. daga cikin wayar Akila tayi murmushi sannan tace,"naji, amma sai na gani daga ƙwayar idonka zan gasgata hakan Kabir...yanzu ya jikin nata?". ya ɗan rufe ido sannan yace,"nima ban sa ni ba, sai dai ki kira likitan nata ki tambaye shi". "wa ye likitan nata?". ta tambaya sautin murmushinta na fita. Kabir na ɓata fuska yace,"shi Ahmad ɗin mana". daga cikin jirgin da Akila ta ke tai dariya kaɗan kamin tace,"yaushe kuma Ahmad ya zama likita banda labari, naga ma karatunsa is not related to health ta ya za ai ya zama likita Kabir?". kamar me gunguni yace,"da a gabanki ya dinƙa rawar jikin checking ɗinta da zuba bayanan ciwon za ki kira shi da ƙwararran likita wanda ya amsa lambar yabo". bai bari ta kai ga wata maganar ba yace,"yau ɗin za ki dawo?". tace,"kamar na fasa dai, tunda nasan zaka bawa Maryam duk wata kulawa da ta dace". yay gajeran murmushin da shi ɗaya yasan ma'anarsa sannan yace,"Ummi ki dawo ki kula da ƴarki kawai, ni gobe ma zan bar ƙasar".
murmushi Akila tayi sannan taci gaba da masa bayani akan maganar da suke yi wadda ta zama musababbin kiran nasa. yay shiru na kusan minti biyar kamin ya amsa da,"tom shikenan sai kin dawo ɗin...hope jakar tsarabata daban da ta kowa?". "kai ma ka sa ni ai Kabir". da haka suka yanke wayar. daga bayansa yaji Yagana na faɗin,"ai Zulai nafi ƙarfin awa biyar tsaye anan wurin tun kamin hudowar rana, ni da ƙofar wajena amma anyi bake-bake an hanani shiga, kinga fa yanda ya wani bubbuɗe hannu ya kankame ƙofar, ni dai Rakiya ina ganin ta kaina a gidan nan, wai sunan gidan ɗana. ko da yake dama duk abin da yake ba mallakin ubanka ba dole sai an nuna maka iko da shi, Allah dai ya jiƙan Babana Manniru, da yana raye duk wannan walaƙancin na jikoki ba zan fuskance shi ba". girgiza kan Kabir ya haɗe da murmushin Zulai wadda tace. "ai Yagana bai san da zuwanki ba ne, ba ki kalla waya yake ba". "a'a fa Zulai ko bai da ido ta ƙeya ai yaji ajikinsa ina bayansa...ki bar mutum ɗan walaƙanci kawai, kuma wallah da Kabiru ba haka yake ba, ko dan yay kuɗi ne Allah masani...bai san ni bana maula ba". sai tayima Zulai nuni da kayan hannunta,"kuma fa kinga tsabagen ƙaunarsa da nake wallah ɗakinsa naje na ɗebo kayansa zan bawa Nawwara ta goge masa...amma sam ba ya ganin kyautawar da nake masa, ke dai ai kin auna arziƙi da kika haifi ɗan ƙwarai kamar Amadu". Zulai ta sake girgiza kai tana riƙe dariyarta, kamar ba jiya ne ta gama cewa Amadu bai da kyan hali ba amma yanzu shi ta ke cewa ɗan ƙwarai. ta karbi kayan hannunta suka nufi entrance ɗin parlon. "Baba Kabiru zan wuce dan Allah". tayi maganar da muryar ban tausayi. Kabir yana murmushi yasa kai cikin parlon, sai dai abinda idanuwansa suka fara tozali da shi ne yasa shi yin reverse babƴ shiri, ganin Ahmad da yay yana feeding Maryam harda wani goge ma ta baki yanata abu sai kace matarsa, yana juyowar ne Yagana na sako kai tasa hannu ta tura shi ya koma ciki,"koma ai dama ina so nayi magana da kai...muje ka faɗa min wannan halin miskilanci daga ina ya samo asali, idan kuma a hatsarin ka samo shi muje asibiti yanzu a cire shi daga kanka dan ba zan ɗauka ba".
ya cije fuska tare da dunƙule hannu kamar zai kai mata naushi, yanda ya fesar da huci daga bakinsa in da Yagana ta lura zata ce ko garwashi ne a bakin nasa, muryansa ya fito a ƙufule da faɗin,"ina da wurin zuwa ne fa Yagana". Yagana ta ɓata fuska tace,"Kabiru ka kalleni a matsayin Hajara ba Rakiya ba". maganar tata tasa ya koma ya zauna kan kujera ba tare da ya ko ƙara kallon dining area ɗin ba, don in ya kuma kai idonsa wurin yana jin zai iya yiwa Ahmad illa. daɗin da ya ji ma earpord ne a kunnesa duka biyu, duk da ba komai yake saurara ba amma hakan ya taimake shi, dan yana jin Ahmad na masa magana yay banza da shi tamkar bai ma san da shi a wajen ba.
sai da Basma tazo ta zare masa tana ƴar dariya tace,"Yaya anata magana fa". yay kamar da gasken dama bai ji ba, yace. "ban jiki ba Basma". "ai ba ni ba, Ya Ahmad ne". "ohh". ya faɗa yana waigawa inda ta masa nuni da shi, ya ɗan saki fuskarsa kaɗan kafin yace,"kai dama kana nan kasa naketa zaryar nemanka". ya faɗa yana ƙoƙarin danne zafin da ke tasowa daga can ƙasan zuciyarsa.
________________________________
Ƴan team ɗin Kabir kuci gaba da cewa Ahmad me ƙaton kai ku ga yanda zamu kwashe da ku🤨, wani yace Kabir ɗin ya bar masa da za ku wani ishemu da Maryam ta Kabir ce, to ba za'a ba shi ba ɗin can yaje ya ƙarata da halinsa🙄🙄._
*Please Vote, Comment& Share.*
[7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
_Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._
*(42)*
Ahmad na riƙe da hannun