urities na kewaye motar har zuwa lokacin da ta sami waje ta faka, bata ɗauke kai a motar ba da mutanen ciki da take jiran fitowarsu, duk da tasan cewar ba zai wuce Major bane, don yawanci motarsa ce kaɗai ke shigowa jiniya ta karaɗe ko'ina. to amma duba da yanda mafi yawa dakarun gidan su kai kan motar zaka san akwai wani mai ƙafa na gidan a cikin motar. san da ta sosa kanta saboda ƙaiƙayi lokacin idonta ya sauka akan farar ƙafar da ke fitowa zuwa waje, take gabanta ya faɗi, tayi saurin ɗauke kai zuwa gefe, dan Allah ya sa ni Aaliya na mata kwarjinin da numfashinta ke katsewa a duk san da ta ganta.
ajiyar zuciya ta sauke a hankali tana kallonta ta gefen ido lokacin da ta fito daga motar gaba ɗaya ita da ɗanta da kuma Major ɗin da taji jiya su Sakina na raɗe-raɗin cewar sati na gaba za'a ɗaura auren Aaliya da Major, ita kuma Akila zata auri wani ministan health da ke saudia. kallonsu ta ke cike da burgewa da sha'awa, da ace tayi haƙuri tabbas da yanzu da duniyar Maryam ta sauya dole ita ma tata ta sauya zuwa cikar burinta, inda ace ta bar wannan soyayyar da ta kewa Maryam a matsayin ta gaskiya babu sirkin yaudara da a farar fuskarta da aka santa da ita, saɓanin baƙinta.
lokacin da Aaliyan tazo wucewa sai ta tsinci kanta da saurin zube gwiwoyinta a ƙasa ta shiga roƙon alfarma da magiya akan sassaucin irin wahaltuwar da ta keyi wajen bauta. Aaliya ta dubeta kaɗan tace,"bani da hurumi da matsalarki, ki nemi Maryam". daga hakan suka wuceta, Alhassan na jin tausayinta a ransa, domin a kallo ɗaya zaka ma ta ka gane tana garuwa.
"hankalina yayi can gaba ɗaya, na kasa samun natsuwa...ban san me yasa Akila ta hanani zuwa ba". Aaliya ke maganar da Major Mukhtar fuskarta na nuni da tsananin damuwar da ta ke ciki akan lalurar ƴarta da aka sanar mata tun a daren jiya.
cikin taushin muryar da ke kwantar da hankali Major ke lallashinta akan haƙuri da tafiyar da ta dage sai ta yi a yau zuwa nigeria. "kuma ki kwantar da hankali, kin ma fa ji muryar Daughter, kinga kuwa ai ta sami lafiya". tayi shiru for some seconds kamin ta ɗago raunannun ƙwayar idonta ta kalle shi tace,"but Major me ya kawo asthma a tare da Maryam?, bayan ni da kai babu wanda yake da wannan cutar". "your Excellency wata cutar ai ba gadonta akeyi ba, jarabawa ce kawai daga ubangiji". ta sauke numfashi da faɗin,"haka ne, Allah ya bata da sauƙi. amma Major ina so Maryam ta kasance a wurina sai dai ina jin nauyin Akila". yay murmushi kamin yace,"ita ma zata ji nauyinki ai, hakan zai sa ta bar mana ita mu tafi da ita gidanmu". Aaliya tasa hannu ta ɗan rufe fuskarta, yana murmushi ya sai ta camerar wayarsa ya ɗauketa saboda kyawun da tai masa a hakan.
"idan an ɗaura aure, ko Alhassan ya zauna anan, ko kuma na kai shi wata ƙasar". tayi saurin ɗagowa tana dubansa da son jin dalilin hakan. ya kai ƙaramin kofin shayi bakinsa, bayan ya kurɓa yace,"saboda na lura idan yana tare damu ba zai barni na sake da ke yanda nake so ba...ki kalla a hakanma yanda yabi ya sawa dukkan wani motsi namu ido". siririyar dariya kawai tayi bata ce komai ba.
"Almustapha zai wuce italy gobe ƙaro karatu". ya faɗa yana dubanta ta cikin reflection glass na cup ɗin. tana datsa nama da fork ɗin hannunta tace,"Imam fa?". ya murmusa leɓensa sannan yace,"burin Imam shi ne football, shi ma next tomorrow zai wuce england". ta ƙara tambayarsa,"ehen what about Ibrahim?". sai da ya ɗaga gira sama sannan yace,"kin manta yace ba zai baro saudia ba sai ya sauke alƙur'ani". ta tsayar da ƙwayar idonta cikin nasa da cewar,"zamu je can fa honeymoon, dan haka shi ma kamata yay ka tura shi da nisa...tun da na lura 1by1 so ake a nisantani da yarana". ta faɗa tana ɗan ɓata fuska kaɗan, yay dariyar da ta bayyanar da haƙoransa tare da kai hannu zai shafo fuskarta maganar Alhassan ta dakatar da shi. "Dad...". tsayuwarsa a gaban dining ɗin ta haɗe da dunƙulewar hannun Major yana cije leɓensa na ƙasa da kallon Aaliya ta ƙasan ido, a hankali ya furta."u see bah...ai dole ma na luluƙa wannan yaron da nisa". Alhassan yaja ɗaya daga cikin kujeran dining ɗin ya zauna, yana naɗe hannun jallabiyarsa yana faɗin,"be a little more patient...next week ne fa kawai". ya faɗa kamar ba da mahaifin nasa yake ba, yana mai janyo plate ɗin chicken burger gabansa. "kuma Mami shikenan haka ake fisabilillah, dan kin sami Dad sai kike mantawa da ni a duk time ɗin cin abincinki da kika san tare muke ci. duk da Dad ɗina ne but am little bit jealous". yay maganar yana kai fork bakinsa, ya kuma haɗe da ranƙwashin da Major ya bashi. Aaliya dai kallonsu kawai ta ke tana murmushi tattare da wani farin ciki a ƙasan ranta.
*Nigeria, Bichi.*
ƙafafunsa su ka hau kan step na ƙarshe na shiga cikin parlon, hannunsa ɗaya saƙale da waya ɗayan kuma na cikin aljihun rigarsa, yayinda pink lips ɗinsa na ƙasa ke cikin bakinsa yana tsotsa, yana mai sauraron maganar da ke fita ta cikin wayar.
"Ummi da gaske na ke miki". ya faɗa muryasa ta fita da amon da ba zai bada tabbacin s