NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 171 of 223

umfashi ajikin Suhail tun da har na gane manufarka...ka gama tsara shirinka ni kuma na maka alƙawarin sai na lalata shi". Jawad ɗin ya motsa laɓɓansa yana wani killer smiling sannan ya fice bayan yace da Suhail ɗin,"na barka lafiya". *Qatar, cikin masarauta.* zaune take daga gefen wani ƙaton dutse da ke acikin ɓangaren masu yiwa gidan hidima, ta haɗa kai da gwiwa jikinta kuma sanye da uniform na bayin gidan, wannan uniform ɗinma aji aji ne kuma nata yana ajin ƙarshe na ƙasƙantattun bayin masarautar. gaba ɗayanta ta sauya tamkar ba ita ba, a halin da take ayanzu ita kaɗai tasan me ta ke ji, wannan wahalar ta kullum ta gaji da ita, gashi dai babu duka babu zagi amma bautar da take yi kaɗai yafi ace dukan nata ake kullum. tasa hannu ta goge guntuwar ƙwallar da ta cika idonta. bata taɓa tunanin ƙaddara zata wanzar da ita a cikin wannan yanayin ƙasƙancin da take ciki ba, domin bata lissafa hakan a cikin tsarinta ba ko kuma hasashen hakan, amma sai gashi tun da alƙalami ya riga ya bushe komai ya sauya mata, bata da ikon dawo da baya ta gyara lissafin tsarinta, balle labari yasha banba da wanda ake kai ayanzu. dama Larai ta faɗa mata, watarana zaren labarin shirinta zai sauya a yayinda akazo kan wata gaɓa da bata taɓa haskowa kanta ba, ashe kuwa hakan zata faru, za kuma ta kasance. wataƙila da ace tayi haƙuri ta barwa lokaci komai, da ta tsinci abin da sauyin mummunar ƙaddara zai kawo mata, wan nan lokacin na ganiyar da Malam da iyalansa suke kai ayanzu, kuma wataƙila inda tayi haƙurin ta tsinci ribar haƙurin, tun da Allah na tare da ita ba mantawa yay da ita ba, haihuwar dai! wannan haihuwar tabbas da tayi haƙurin taci gaba da adu'a wataran Allah zai bata in har tana da rabo, to yanzu gashi tayi biyu babu, ba wan ba ƙanen. lokaci guda wani abu yay tsalle ya harba allon ƙirjinta, ta sa ni, ba zata taɓa dawwama a haka ba dole wataran zata fita, duk da bata hango hakan amma tasan rayuwa zata iya rubuta hakan. zuciyarta taji ta matse, tayi saurin matse idnuwanta gam zuciyarta na harbawa da wannan sunan, wannan mutumin, wannan bawan da tunaninsa ke hanata sakewa a kowanne bugawar sakan na agogo tun kamin zuwan wannan lokacin. Kabir! Kabiru dai ɗan mijinta, bata san taya ba, bata san ya akai ba, ita dai kawai ta tsinci kanta cikin matsanancin son yaron a duniyarta, wanda ta ke jin kishi da baƙin cikin duk wanda ya raɓe shi ko da kuwa ace ƴan'uwansa ne, ta kuma sha alwashin haramtawa duk wata ƴa mace shi da sunan mallaka. kuma ko ayanzu bata janye ƙudurinta ba, in har akwai boka, Malam da bori a duniya tabbas sai ta mallaki Kabir, sai dai in bata raye, ba'a cikin nan ba, ko inda yafi nan matsi ne sai ta samarwa kanta Kabir, wannan alƙawarinta ne. _"Mami kar ku kaita kotu, dan Allah ta zama ƙasƙantacciyar baiwar masarautarmu, zuwa cikar wasu wa'adin lokuta da na shirya ta dawo ƙarshin ikona, ta zama mai min bauta"._ maganar Maryam a waccan ranar, wan nan lokacin da ake ikirarin za'a yanke ma ta hukuncin zaman gida yari ɗaurin rai dalilin allurar gubar da tayiwa Gwaggo, furucin ya shiga tariya a cikin kanta, sautinsa a cikin kunnenta.  baƙin ciki da takaicin halin ko'in kula ɗin da Maryam ta nuna akanta ya doki ƙirjinta, ko babu komai, duk da cewar ta ƙaunace ta ne ba don Allah ba sai dan biyan buƙatar kanta, amma ya kamata ace ta tuna da kulawarta da hidimtawarta gareta. ruwan da aka watso ma ta a jiki yasata yin firgigit ta dawo duniyar zahiri. a tsawace shugabarsu ta shiga mata magana. "dilla Malama miƙe kije kici gaba da aikinki". ta faɗi hakan tana jin tamkar ta kai mata duka saboda tsananin haushinta. "Amarya kike ne kowa?, ke wacce iriyar shashar mata ce ne wai, kullum sai anzo ance miki yi kaza yi kaza, gaba ɗaya ƙwaƙwalwan kifi yafi naki jaa...to wuce ga Sadauki can na jiranki, za'a kai ki aikin nome gonaki". maganarta da ban tausayi tace,"dan Allah ayi min afuwa, bana jin daɗi, ina ta fama da zazzaɓi tun jiya kuma bansha magani ba". Matar ta banka mata harara da faɗin,"ko ba zazzaɓi ba, to faɗawa wani ba ni ba...mtswww, kar ki ɓatan lokaci". tayi gaba ta barta anan tsaye tana cije fuska saboda yanda dukkan gaɓɓan jikinta ke mata mugun ciwo. a harabar wajen gate ta tarar da sauran bayin da za'a tafi da su, ta tsaya daga gefe tana matsa kwankwasonta da ke mata ciwo matuƙa, idanuwanta na daɗa ƙarewa kyawu da girman masarautar, ƙwarai rayuwa test and trial ce, yanzu duk wanda zai kalli wanda ke cikin wannan masarautar zai ce ba shi da wata matsala da zata kai shi ga damuwa a rayuwarsa ba, daular da suke ciki tafi gaban ta haifar musu da rashin jin daɗi, to amma sai dai ba anan abin yake ba, sun ɗanɗani ɗaci da baƙin ciki, sun gogi wani tabo da ba zai taɓa goguwa a garesu ba, in dai har da rai da kuma lafiya a kowacce rana da bugawar agogo sai sun tuna wannan ƙaddarar, wannan jarabawar ta ubangiji, haihuwar ɗan gaba da fatiha a cikin zuri'arsu. ta karkata hankalinta ga motar sojojin da ke shigowa jiniya na tashi, fadawa da sec
🏠