NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 170 of 223

zaka sami macen da zata iya riƙe maka ɗanka da amana ne sama da Zeenatu?". ya mayar da ƙwayar idonsa kan Hajiya, murya a ƙasa yace. "dan Allah Hajjah ki bar min zancen wannan yarinyar, mene haɗin daddawa da kunu?...ni ko banyi wani auren ba zan iya kula da Arif, dan shi ɗaya dai Allah na tuba". Hajjah ta bishi da harara, Bibi(Kakarsu Akila) tace da shi. "ai ni yanda na fahimci take-takenka Suhail so kake kaje ka auro wacce ba jinin sarauta ba. ba kuma zamu lamunta ba, kasan da wannan". yace,"amma Bibi fisabilillahi shikenan sai ace dan kai ɗan sarauta ne auren bare ya haramta a gareka, a wanne hadisin ko ayar aka ce haka?...magana ta gaskiya ni bana son Zeenatu ba kuma zan aureta ba, kuma ni ba ƙaramin yaro bane da za'a min dole a wajen aure, like i said zanyi breaking record for sure". yana faɗin hakan ɗacin da ke ƙasan zuciyarsa na haskawa a saman fuskarsa. "to in haka ne ka koma ka nemi auren ita yarinyar da ta asirceka mana...". Maama tayi maganar, bata kai ga ƙarasawa ba yay saurin cewa,"wa ɗin?". tayi guntun murmushi,"ah tou Suhail wadda tayi asiri akan samun soyayyarka ai masoyiya ce ta haƙiƙa, dan haka a shawarance kawai kaje ka nemi aurenta yanzu tun da ta tuba, kuma ina baka tabbacin zaka sami tsantsar soyayya daga gareta kamar yanda ta nuna maka, ni naga hakan a ƙwayar idonta ta cikin vedio call ɗin da akai da su, kuma ƙwarai haƙiƙa zata kula da Arif". yay guntun murmushi na takaici,"ai ko matan duniya sun ƙare babu abin da zanyi da wannan abar kam, kima daina wannan zancen Maama, haƙurin da nayi ma ban hukuntata ba wallahi darajar Maryam taci". "to yanzu dai ai an faɗa maka kuma kaji, wata ɗaya kacal Mai Martaba ya baka...kuma Suhail Zeenatu kawai zaka aura muyi farinciki da aurenka". ya dubi Bella da kyau sannan ya taje gemunsa da yatsunsa, kana ya miƙe tsaye yana zira hannu a aljihu da nufar hanyar fita yana faɗin,"ni dai na faɗa zanyi breaking record, kamar yanda ba zanyi auren zumunci ba haka matar da zan auro bata da alaƙa da sarauta, idan ta zama mallakina ta sami wannan jinin". Bella ta bishi da faɗin,"ka jima ba kai breaking record ba Suhail...zamu gani mu da kai wa ya isa da wani". a hanyar lambu ya tarar da Jawad, suka wuce ɓangrensa tare. inda yana shiga ya sami baiwar da ke aiki a ɓangarensa tana jera kayan abinci a saman dining. tana ganinsa ta zube ƙasa tana miƙa gaisuwa, ya amsa mata fuska a sake sannan ya wuce bedroom nasa ya bar Jawad anan parlo. ya ɗau kusan minti goma sha biyar kamin ya fito, a parlon ya sami Jawad na ma Arif wasa wanda aka ɗauko shi daga makaranta, ganin ɗan nasa yay smiling ɗin da haƙoransa suka ƙi rufuwa, dan matuƙa yana son Arif da tausayinsa. Mamansa ta rasu tun a ranar da ta haife shi dan ko ganinsa ba tayi ba ta amsa kiran ubangijinta. shekaru huɗu kenan da rasuwarta har yau kuma ya kasa ƙara aure saboda Arif, ya kasa mantawa da ita, gani yake tamkar yaci amanarta ne idan yay tarayya da wata macen, kuma yana ganin kaman duk wadda zai aura ba zata riƙe masa ɗa da amana ba, haka ɗan ba zai ji daɗin zama da ita ba...tun bayan rasuwar matarsa Sanah bai ƙara jin son wata ƴa mace ba sai akan Maryam, wadda kawai yaji yana kwaɗayin ya mallaketa kuma zuciyarsa tayi masa amanna da cewar yarinyar zata iya kula masa da Arif gwargwadon yanda yake buƙata, duk da yasan cewar ita ma Maryam ɗin rainonta ne zai yi, to ashe ita ɗin ba rabonsa ba ce. a hankali ya rufe idonsa for a while sannan ya buɗe ya kira sunan Arif din, Arif ya sakko daga kan cinyar Jawad ya tafi wurin mahaifinsa da gudu shi kuma ya ɗauke shi ya rungume shi ajikinsa yana ta sumbatar fuskar yaron. kuma sai hoton lokacin da Maryam ke yiwa Arif wasa ta cikin vedio call ya haska masa a cikin kai, ya rumtse idonsa sosai yana mai jin wani abu na taso masa. "muje ayi wanka sai ai lunch ko?". yace da yaron yana shafa kwantacciyar sumar kansa, Arif ɗin ya ɗaga masa kai. "ehh Abbi ina jin yunwa dama". "baka ci abinci a school ba?". "ba zan iya ci ba idan babu kai". ya faɗa yana shagwaɓe fuska. nan Suhail ya juya zuwa bedroom ɗinsa yana cewa da Jawad. "Yaro kayi aure ka haifa kaima kaji irin abin da ake ji". Jawad ɗin na shafa wayarsa yace,"me ake ji dama?". "Jawad wani irin abu ne da ba zai fasaltu ba". murmushi Jawad yay sannan yace,"soon nima zanyi, Maryam na ke jira...ina so tayi hankali ne kamin nayi requesting ma ta abin da ke zuciyata". Suhail ya waigo ya dube shi da tambayar. "me kake nufi da tayi hankali?, kana nufin zaka ce Maryam bata haɗa hankalin da za ace wani ya mallaketa?". "no ba haka nake nufi ba, just i can't take her bulshit. you know well an raini yarinyar nan da shagwaɓa, kuma har yanzu ban manta da abin da ta min ba wancan ranar...". "ohh idan na fahimci inda zancenka ya dosa za ka aureta ne saboda kai ramuwar gayya". Jawad ya murmusa yana miƙewa. "ko kaɗan, kawai dai". "kawai dai me Jawad?". "Suhail you will not understand, so faɗa maka ma ba ya da amfani". "shikenan, amma ka sa ni, aurenka da ita sai dai idan babu n
🏠