NOVEL SHARES -
i na harareta, na ɗauki filon na jefar a ƙasa tukunna na koma nayi kwanciyata. Ina jinta ta miƙa hannu ta ɗauki bargon kwanciyarta dama lokacin baccinta ne yayi hakan ya shigo da ita ɗakin. Ina jin Adawiyya na cewa na rage Masifa, nayi mata banza, Sai Kuma ta hau yi min hirar sabon saurayin Sadiya, ina ta dariya saboda yanda ta-ke ta zuzuta muninsa, daga can tsakar gida naji Gwaggo na ƙwala min kira, na diro ƙirjina na dukan uku-uku na fita, tana daga cikin ɗakin girki na ƙarasa a ɗarɗarce, ta galla min harara sannan ta miƙo min kwanukan hannunta guda biyu, "shashashar banza ungo ni riƙe ki kaiwa baƙin nan, kuma ki basu haƙurin maganar da kika yi ɗazu dan sai su zata da su kike". "Gwaggo to ai dama da su ɗin nake, amma da wannan me ƙasumbar nake, Kina ganinsa ya sunkwi da kai ƙasa kamar mutumin arziƙi to wallahi ba ƙaramin mara mutunci bane...". Ban kai ga ƙarasa zancena ba tasa hannu ta gwaɓeni, ba kuma ta ƙara ce min komai ta fice ta barni. Sosai naji zafi dan sai da laɓɓana suka ca-ke da haƙori, na kuwa ɗau alwashin abincin nan dai ba zasu ci shi ba.
Zaure na nufa inda ɗakinsu Ya Kabiru yake, takalmi ɗaya na gani a ƙofar ɗakin, na kuwa sa ƙafa nayi fatali da shi gefe dan nasan bana wancan buzun bane tunda bashi nagani ɗazu a ƙafarsa ba lokacin da yake alwala. Kamar ma na juya na fasa shiga ɗakin, sai nayi tunanin Gwaggo zata iya ganewa banje ba, na ko shiga ɗakin babu ko sallama, kasancewar akwai wutar nepa wadda a ɗakinsu Ya Amadu ne kawai aka jona, sai ɗakin ya gauraye da haske, yana daga zaune bakin katifar Ya Amadu yana latsa waya, naji kamar na ƙarasa na juye masa abincin duka a jikinsa, saboda gaba ɗaya haushinsa nake ji. sai kuma na shiga laluban inda Buzu yake ban ganshi ba, kenan baya ɗakin. Na juya zan koma Jawad ɗin ya ɗago yana ce min,"mara kunya ya akayi ne, ba aikoki akai ba bismilla aje anan". Na juyo na ɓalla masa harara na murguɗa masa bakina kamar zasu cire, dariya kawai yayi yana dubana kamin yace,"ashe wuyanki dai kaurinsa da yawa yake, Rashin kunyarkin ba a iyaka waje ta tsaya ba har da cikin gida, to Allah ya shiryeki". Nace,"amin kaima kuma ya shiryeka yasa ka gane mace da daraja ta-ke ba sai wacce ta kawoka duniya kaɗai ba...kuma ko banza anji kunya wallahi tunda har akazo ƙauye gidan marasa ilimi cin arziƙinsu". A yanda yake kallona maganar kamar bata soke shi ba, kuma ƙarya yake wallahi.
Na fito cike da jin haushinsa, na tsaya a bakin ɗakin ina jiran dawowar Buzu, Can sai gashi ya dawo da waya maƙale a kunnensa yanata magana acikin harshen da ban san wane yare bane. Ya tsaya a gabana ina jin kallon da yake min ajikina, ni kuwa idona na ƙasa ina kallon ƙafata. "Maryam ya kika tsaya anan baki shiga ciki kin aje ba, Jawad ai yana ciki, Kawo na tayaki ɗaukar ɗaya".
Ina aikin ƙifta idanu na turo baki gaba na kuma haɗe gira wuri ɗaya, na ɗago ido na dube shi sannan nace, "ni dai ka min tsakani da wannan tsolon abokin naka. Allah kuwa ba ruwansa da ni". Murmushin da ya bayyanar da haƙoransa naga yayi, sai dai kasancewar zauren babu wadataccen haske sai banga yanda fuskarsa ta ƙawutu da kyawun murmushin da yayi ba. Bai yi magana ba na shuɗewar wasu sakanni sai aikin sosa siririn sajensa yake. "kaima bayansa kake bi ko, ai duk da ban ganku tare ba ɗazu nasan dai kasan irin ɗibar albarkar da ya yiwa Yayata tunda abokinka ne kuma zai faɗa maka...wama ya sani ko mugun halinku ɗaya kaine siffarka tafi siffantuwa da ta mutanen ƙwarai a fili". Ya kuma yin murmushi yana cewa,"au Maryam haka ma za ki ce". Na ɗan murguɗa masa baki,"ni ka daina ce min Maryam, Mairo sunana, da shi ne sunan da Babana ya raɗa min, idan baka iya faɗe ba sai ka haƙura". Sai naji ya kwaikwayi salon yanda nayi maganar yace,"ni kuma Maryam zance, sai dai idan na faɗa kar a amsa".
Su Inna duk sun wuce ɗaki lokacin dana dawo, saboda haka na wuce na mayar da abincin ɗakin girki, tukunna na wuce ɗaki. Inna Amarya harta kwanta, dan haka nima na nemi wuri na kwanta, da yaƙinin idan da Safe Gwaggo ta nemi ba'asin abincin dana dawo da shi zance mata dana je banga mutane ba acikin ɗakin, kuma na jira na jira basu dawo ba, kuma wutar ɗakin ta jogane balle na shiga na ajiye, itama ai tasan ina tsoron duhu.
[7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*MissAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
*7)*
rikicewa Kulu tayi da ganin Gwaggo wacce ke kallonta tun daga sama har ƙasa da son gano abunda ta-ke ɓoye mata, tsawon daƙiƙun da ba zasu haura biyu ba Gwaggo taja tsaki, ta bar kusa da ita ta ƙarasa bakin gadon da Mairo ke kwance tana faɗin, "Abu ne mafi sauƙi a wajena na kori mutum ya koma inda ya fito matsawar ba zai kiyaye sharuɗan da na ke gindaya masa ba...saboda na ɗaukeki ina taimaka miki ba yana nufin dole kema kice zaki taimaka min ba, ba kowa na yarda da shi ba dan haka ki daina raɓar min Ƴaƴa". Kulu dai da ke tsaye jiki a sanyaye sauraran Gwaggo da faɗanta kawai ta-ke,