NOVEL SHARES -
zauna anan kan kujerar da ke compound ɗin suyi hira ko ya samu ya ɗebe kewa. da suka zauna hirar tasu duk akan kasuwancinsu ne, inda yake daɗa ba su shawarwari akan harkar business. hirar su ke amma gaba ɗaya hankalinsa ba'a kansu yake ba yana bakin gate, yana jiran shigowar motar Ahmad amma shiru shiru gashi har ƙarfe takwas da rabi saura.
ya buɗe baki zai ce da Lukman ya kira shi a waya kenan sai ga horn ɗin motar, har motar ta shigo ta faka bai sami natsuwa sai da ya ga Basma ta fito daga motar, tukunna ya haɗe murfin idonsa ya rufe yana sauke nauyayyar ajiyar zuciya. ta cikin hoton abin da ke haskawa acikin duhun idonsa yaji Basma a kusa da shi ta kamo hannunsa da faɗin,"Ya Kabir yau kaji sauƙi ka fito?". ya buɗe idonsa ya sauke a kanta da murmushin da a kallo ɗaya zaka gane da wani ɓoyayyan abu a tattare da shi. "na sami lafiya Basma...ya akai ku ka daɗe?". "Yaya ce bata da lafiya muka wuce asibiti". da mamaki ya ke dubanta da tambayarta,"rashin lafiya kuma? ina ce lafiya ƙalau ku ka fita?". "ehh Yaya ai ko acan ma sai a hanyarmu ta dawowa ne ƙirjinta ya fara ciwo, kuma da muka je asibiti likita yace asthma ce". "what?". yay tambayar muryarsa na amayar da tashin hankalin a cikinta. kafin Basma ta kuma cewa wani abu sai ga Ahmad yazo ya wuce da Maryam ya ɗaukota a hannunsa. da lokacin da yay azamar miƙewa tsaye zuwa san da ya faɗa part ɗin Yagana har yay tsaye a bakin gadon da Maryam ke kwance duk bai sa ni ba. tun da yay tsaye a bakin gadon kallon fuskarta yake da wani abu da ke tsargawa ajikinsa from head to toe. bacci ta ke peacefully, sai numfashinta da ke up and down da sauri sauri, yana kallon laɓɓan Ahmad da ke yiwa Yagana bayanin abin da ya faru amma baya jin maganar da yake a cikin kansa, da ƙarfi kuma ya cije leɓensa na ƙasa ganin yanda hannun Ahmad ɗin ke cikin nata yana murza ma ta tafin hannu a hankali. sai ya rumtse idonsa da ƙarfin gaske ba tare da sanin lokacin da ya ɗauko wayarsa daga aljihu ba ya dannawa Abdurrahim kira ba, kuma bugu 1,2,3 ya ɗaga. daga can ɓangaren Abdurrahim ya shiga yi masa tsiya yay saurin dakatar da shi. "Abdurrahim ya isheka". "to sarkin matsifa ya akai?". "Abdurrahim bana so tafiyata ta wuce tsakanin gobe da jibi". abin da yace da shi kenan ya kashe wayar, sannan ya ɗora ƙwayar idonsa akan Ahmad da fuskarsa ke nuna tsantsar damuwa.
da sassarfa yasa kai ya fice daga ɗakin, halin da ya ke ciki a yanzu ya mantar da shi ciwon da ƙafafunsa ke masa, sai dai yana zuwa parlo bugawar da zuciyarsa keyi ta tsaya cak ganin Nawwara, bata lura da shi ba a san da tazo wucewa ta gabansa sai ji tai an fizgo hannunta da ƙarfi ta dawo gaban mutum ta tsaya, hucin zafin numfashinsa na sauka saman fuskarta, inda shi kuma idonsa ke kulle yana ƙara matse hannunta da ƙarfin gaske tamkar zai ɓalla mata ƙasusuwa, jikinsa kyarma kawai yake yi, ƙoƙarin janyota jikinsa yake ya rungume, wataƙila ya sami sauƙin raɗaɗin da zuciyarsa ke yi masa a ɗumin jikinta.
*Ethiopia, Masarautar Baharar.*
a cikin tangamemen parlon, wasu tsaffi ne su huɗu zaune a ƙasan carpet ɗin da aka malale a saman tiles ɗin parlon, sun ɗora hannayensu akan tumtum ɗin da ke aje a gefensu, yayin da wasu dattijawan Mata guda uku ke daga kan kujera a zaune, sai Suhail da ke kan tashi kujerar shi ma yana mai kaɗa ƙafarsa guda ɗaya, idanuwansa a kulle yana ci gaba da sauraron abin da Bella ke faɗa masa na ga me da saƙon mai Martaba akan aurensa da Maryam.
*Plss vote,share&comment.*
[7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
_Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._
*(41)*
_"Aure! Aure dai! ana nufin babu aure tsakaninsa da Maryam?, yarinyar da ya saka a ransa tun bayan rasuwar matarsa Sanah, to me yasa ma za ai masa haka?"._ zancen zucin da Suhail keyi kenan tun a lokacin da ya kai maganar yana son ya auri Maryam gaban Mai Martaba, kuma har zuwa yanzu da Bella ke ƙara isar masa da saƙon Mai Martaba ɗin na cewar dole ne ya haƙura da batun auren Maryam saboda ƙarfaffan dalili.
"Suhail ko kana son ji ko baka son ji Maryam ta haramta gareka, ka zama uba a gareta wajan shayarwa tun da har kunsha nono ɗaya kai da mahaifiyarta...dan haka the charpter close kar na ƙara jin zancenta daga bakinka...ka nemi wata macen kawai". Bella ke maganar cikin ɗaga murya me fitar da sautin faɗa.
ya buɗe ido ya kalleta haɗe da sauke dogon numfashi. maganar mahaifiyarsa ta ratsa ta cikin baƙin cikin da yake ji a zuciyarsa. "ni ban san ma dalilin da ya sa baka son Zeenatu ba wallahi, yarinya me hankali da tarbiyya, ga ilimi, tana sonka ba wai bata sonka ba amma sai watsi kake da lamuranta...tukunna ma kana tunin