ubansa, yace min ai ƴar da nake riƙo ne ta kai ƙarata wurin Baba Kabiru to su basa son haka na daina...maganin a zauna lafiya saina basu haƙuri, amma ai akwai Allah, gidan wani zata je idan sharri abinyi ne taci gaba ba, kaina har yanzu ciwo yake saboda ciwon abin".
Aminu yace,"Allah sarki, haƙuri za ki amma ɗan riƙo yana da wuyar sha'ani". "ka bari kai dai yau ai nayi danasani, ni tsorona ma maganar taje kunnen Uwarta ko Ubanta, dukansu kasan zuciyarsu a wuya ta ke yanzu sa saka a far min".
Kabiru ya katse mitar da cewar ta miƙo masa abincin yaci, ta ɗauko sai ga Zubaida ta shiga tana sanar mata tayi baƙuwa, nan ta tashi ta fita.
"ke ki kira min Nawwara". Kabir yace da Zubaida. sai bayan ya idar da sallar magriba ne Nawwara ta shigo ɗakin, lokacin Aminu ya har ya tafi, ta sa me shi yana kaiwa da komowa daga bango zuwa bango, yana taka ƙafa ɗaya da ƙyar. ta cikin madubin da ke kafe a bangon ɗakin da yake fuskanta yake hangota ta bayansa, tun lokacin da ta shigo ta tsaya har san da ta ke ce masa gata, amma kuma bai amsa mata ba kuma bai juyo ba yana dai ta kallonta ta cikin madubin da irin kallon da ya kasa fassara ma'anarsa a tare da shi.
maganar da ta ƙarayi ne yasa ya haɗiye wani guntun yawu a maƙogoronsa sannan ya juyo yana fuskantarta, yay tattaki ya ƙarasa zuwa inda ta ke, inda tazarar da ke tsakaninsu bata wuce inci huɗu ba. "Maryam fa?". har yanzu kanta na ƙasa tana wasa da yatsun hannunta tace,"Yaya ba su dawo ba har yanzu". sai kawai ya rumtse idonsa gam tare da ɗaga kansa sama yana jin wani abu me zafi na tsargawa ajikinsa. wucewar daƙiƙa biyu sannan yace da ita,"zuba min abinci". yana faɗa ya koma ya zauna kan kujera, ita kuma ta ɗauki plate ta zuba abincin kaman yanda yace sannan ta kawo ta ɗora akan table ɗin da ke gabansa. "Yaya shikenan?". yay shiru bai ce mata komai ba, ita ma bata miƙe daga duƙen da take ba, ya ɗauki spoon ya fara kai lomar tuwon bakinsa, duk zumuɗinsa na son yaci tuwon memakon yaji daɗinsa sai yaji wani ɗaci ya ziyarci saman harshensa, dan haka yay saurin maida spoon ɗin ya ajiye ya sauke ƙwayar idonsa biyu a tsakiyar kan Nawwara. "wa ya dafa abincin nan?". ta ɗago ta dubi yanda yake yatsine fuska kamin tace,"Yagana ce, wani abu kaji a ciki?". "ɗaci naji, may be ta haɗa da wani abun bata sa ni ba". a ladabce tace,"ƙila daga bakinka ne, tun da har baƙi ma sun ci kuma ba su yi ƙorafi ba". "ci". ya faɗa yana mai mata nuni da plate ɗin da idonsa. "Yaya bakinka ne kam, ni banji komai ba". ta faɗa bayan tayi spoon ɗaya. hannunta taji ya kamo wanda yasa tayi saurin ɗora ƙwayar idonta akan babban yatsansa da ke shafa kan fatarta, kuma kamin ta kai ga haɗiye yawun da ke maƙogoronta taji yace,"wannan ƙonuwar fa?". ƙirjinta na bugawa tace,"jiya ne manja ya zubo min". "kuma shi ne ba'ai treating ɗin wajen ba?". a shirun da tayi kawai ya fahimci bata gane me yake nufi da treating ba, dan haka ya ɗaga mata gira,"ina nufin me yasa ba kuje chemist ba". "ai naga kaɗan ne bada yawa ba, kuma ma Anty Maryam ta min tofi a wurin". ya saki hannun nata yana jinginar da kansa jikin kujera sannan yace,"shiga bedroom ena wajen gado ki ɗauko box ɗin first-aid". ta inda tasan first-aid box ranar da Maryam taji ciwo Ahmad ya naɗe mata hannun da bandage, dan haka ko da ta shiga ɗakin bata jima ba ta fito ta kawo masa. "zo ki cire min wannan". yace da ita yana mata nuni da zaren da aka naɗo hannunsa zuwa wuyansa, ta miƙe ta cire sannan ya miƙar da hannun nasa a hankali cikin ƙarfin hali da dauriya sai rumtse ido yake saboda zafi. gefensa ya matsa yace ta zauna, ta zauna a ɗarɗarce saboda wani baƙon al'amari da ta ke jin kanta aciki, kuma har ya fasa ƙunar ya shafa magani ya naɗe mata wurin bata sa ni ba, sai da yay magana tukunna tayi firgigit ta dawo daga duniyar tunanin da ta faɗa a lokaci ƙanƙane, kuma sai a sannan ta ke jin zafin ciwo.
"ki shirya gobe za ki fara zuwa school, da safe Mu'azzam zai kai ki, sai kiyi ƙoƙarin kammala ayyukanki da wuri". bata san lokacin da ta silalo daga kan kujerar ba ta zube gwiwoyinta biyu a ƙasa ta shiga yi masa godiya babu ƙaƙƙautawa har sai da ya dakatar da ita, tukunna ta miƙe ta bar ɗakin cike da farin cikin da ta ke jin tamkar an mata albishir da gidan Aljannah, Allah ya sani ita ma'abociyar son karatun boko ce amma iyayenta basu da halin da za su kaita makarantar boko, domin a samu a sakata a makatantar boko zuwanta aikatau na daga cikin dalilin amincewar mahaifinta, gashi yau Allah ya cika mata burinta tun ba ai nisa ba, dan haka har mutuwarta ba zata fasa saka Ya Kabir acikin adu'arta ba kuma ba zata taɓa mantawa da shi ba.
tun bayan fitarta yake jinsa wani iri, ga shi natsuwar da ya ke neman ya samu ta gagara, ya ɗauki waya yafi sau goma zai kira Ahmad amma sai ya mayar ya ajiye ya fasa kiran, dan haka domin ya sami sauƙin abin da yake ji ya ɗingiso ya fito shaƙar iskar waje, yana fitowa harabar gidan ya tarar da Mu'azzam da Lukman su na shigowa gidan, ya buƙaci da su