NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 166 of 223

a zan fice da gudu sai karaf mu kai karo da Ya Ahmad na ƙumu da ƙirjinsa. ta ke yaja wani dogon tsaki ya hauni da faɗan rashin nutsuwa, da kuma cewar na wuce na ɗakko mayafina ko yay tafiyarsa ya barni, na ɗago na kalle shi da son jin inda zamuje sai dai banzan kallon da ya wurga min yasa ni gimtse maganata nayi ɗakina. na bar Yagana da faɗin,"Allah yaji ya gani ba zan iya ba, ina dalili haka kawai ina zaman lafiya Yarinya zakije ki ƙunduma min sharrin wai na hanaki fita shufin, kai jama'a kuji wani mugun ƙulli...yanzu tsakani da Allah idan wannan maganar ta kai kunnan Uwarta ai sai tace min butulu, saboda naga ta gina mana ƙatoton gida shi ne zan azabtar ma ta da ƴa ta hanyar hanata shaƙatawa, to ai akwai Allah yana ji kuma yana gani, shi zai saka min...ke Basma tsakaninki da Allah yaushe waccan abar tazo tace min zaku je Shufin?, dan Allah ma yau ni na haɗu da ita ne banda ɗazu da zata fita, to amma kinji yarinya saboda baƙin sharri taje tacewa Kabiru wai na hana akaita shufin, kiji zancen nema min masifa a wajen Uwarta da bata barin ta kwana...to ba zan iya ba gaskiya, ni dai Amadu idan kun fita da ita ka kaita can gidan ƴan'uwansu suci gaba da riƙonta acan kamin ita Akilar ta dawo, ba zai yiwu ta jazamin bala'i ba da mugun sharrinta tasa a ɗaureni, dama yanda take da gata nan ta ko'ina wannan uban nata da ba fuskar imani gare shi ba, ba zai duba tsufana ba zai sa sojoji su ɗaureni, Mairo dai yanzu ta zama annoba kam dan tafi ƙarfina, gwara ki tafi na samu salama...kuma sharrin da kika min kije da halinki na rashin kyautawa ban yafe ba". *Please Comment, Share&Vote.* [7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE* *(40)* "ke kuma Yagana gaki da kambaba zance". tayi lakato tana duban Ahmad da yay zancen kamin tace. "dama tunda ba Zulai akaiwa sharrin ba ai ba zai dameka ba, ni kuwa da na ke abar banza da wofi a wurinka Amadu ina na ke da darajar da zaka ɗaukar min mataki...to ko ba komai ka tuna ni na haifi Adamu kuma na shayar da shi". tayi hanyar kitching tana ci gaba da faɗin,"ni dai na faɗa maka kar ka dawo min da wannan abar, dan ba zan iya zama da masharranciya acikin gida ba, Allah yaso ba wani nake aure ba da yau tasa an damƙa min farar takarda". daidai fitowata daga ɗaki nace,"wai ni Yagana da kike ta faman wannan sababin sharrin me na miki ne?". maimakon ta ban amsa sai ta juyo ta banka min harara sannan ta ƙwalawa Nawwara kira tace tazo ta rufe ma ta ƙofarta idan mun fita. har kitchen na bita ina ce mata bata yi min adu'an fita ba tayi min shiru kamar wadda ke magana da kurma, sai da zan fita ne tace,"wanda yafi ƙarfinka ai yafi ƙarfin adu'arka". siriryar dariya kawai nayi kamin nasa kai na fice ina jin ƙara son Yagana a raina, da roƙon Allah ya daɗa ja min da ranta. "jiya naji wancan abin yana cewa tuwon dawa yake sonci, je ki tambayi Zulai idan ta sami dawar ta bani, in ba'a samu ba kuma na kira ubansa ya taho da ita". Yagana da ke wanke nama tana tsiyaye ruwan acikin sink ta faɗa. Nawwara tace,"Yagana wane waccan abin?". cikin ƙufula Yagana tace,"Ubana da waccan abar ta kai ƙarata wurinsa mana". Nawwara ta ƙyalƙyale da dariya tana cewa,"Hajiya Yagana ikon Allah, yau kuma Ya Kabir ɗinne wancan abin". Yagana ta wurga ma ta mugun kallo da faɗin,"kin wuce kinje min aiken ko sai kin gama ɗaukar maganar taki". Nawwara ta fito a kitchen ɗin still da dariya a saman face ɗinta, kuma tana jin Yagana na faɗin,"ƴan aiki da yawa suke a ƙauyen nan, dan haka zan koreki na nemi wata tunda naga kema mutunci bai isheki ba". Yagana ta idar da sallar la'asar Adawiyya tayi sallama cikin ɗakinta, ko da Yagana ta ganta sai ta ɗauki lazimin da ba tayi niyya ba, shiru shiru sama da minti ashirin bata katse ba, kuma dama taja musu kunne kar wanda ya ƙara zuwa ya ganta tana lazimi ya dameta da magana, shi yasa ko da Adawiyyan ta shigo sai ta nemi waje ta zauna zaman jiran idarwarta. Yagana kuma na sane taƙi sallamewar, sai can tayi gyaran murya ta kalli Adawiyya da cewa,"irin haka sai ki haƙura kije kya dawo, ba wai ki tasani a gaba ba kamar wadda tazo ɗaukar fansar bashin dana ci mata na hana." "ai naga dole za ki idar ne ba kwana za kiyi a hakan ba shi yasa na kafa na tsare ina jiran sallamewarki". "au toh, da wacce tsiyar kika zo?." "tsiyar arziƙi". "to ina sauraronki, mene dama?." Adawiyya ta sauko daga bakin drower ɗin da ta zauna ta dawo kusa da Yagana ta zauna, sannan tayi ƙasa da murya ta fara magana. "Yagana dan Allah dama akan maganar Ya Suhail ne. na rasa yanda zanyi da shi a zuciyata, duk da cewar na nemi yafiyar Mairo kuma ta yafe min amma wallahi ina mugun jin kunyarta, Yagana dan Allah ki taimaka min ki shige min gaba". ta faɗa tana kama hannun Yagana ta riƙe acikin nata. "to ina ce shi ma Suhail ai kun nemi yafiyarsa ɗin kuma yace ya yafe muku ko?, to mene kuma ya dami zuciyarki da shi?". Adawiyya ta karayar da kai tare da sake matsowa kusa da Yagana tace,"Yagana ki gane mana, har yanzu ina sonsa fa...". bata ƙarasa ba Yagana ta
🏠