NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 165 of 223

baccin kuka tayi, ba sai ka maketa ba ta shiga taitayinta". Kabir ya motsa leɓensa yace,"da kake magana cikin ɗaga murya wani ya hukuntata kaima ai ba iyawa za kai ba...yanzu dai kawai idan zaka fita ka fita da su, kasan dai daga ita har Basma ɗin ƴan auta ne ƴan alallaɓa, dan kowacce ita ɗaya ce a wurin Mamanta". Ahmad na ɗan ɓata fuska yace,"ni ba ruwana da wani ɗan Auta...fita dama zanyi in sun fito mu tafi tare, in sunyi delay kuma nayi tafiyata". ya faɗa yana miƙewa tsaye, ba dan yaso tashin ba, dan da niyyar ya huta ya shigo ɗakin Kabir ɗin, haka kuma ba dan ya shiryawa fitar ba, ba kuma dan yay niyyar kaisu shopping ɗin ba, sai dan wannan kwanciyar, kwanciyarta ajikin Kabir, kuma dama yana so ya faɗawa Kabir ɗin, yana so ya tuna masa cewar Maryam ba muharramarsa bace, ya kamata ya gyara kusancinsu. "na manta, ɗazu Yayan Inna yazo ya shigo dubaka kana bacci, yana maka sannu". Ya faɗi hakan kamin ya ƙarasa fita daga ɗakin, kuma ba tare da ya ji amsawar Kabir ba, sai dai a yanda ya fita ɗin fushi da ɓacin rai na haskawa a saman fuskarsa, wanda a ganin farko ga mai saurin fahimta zai gane cewar kishi ne tsagwaronsa ba komai ba, kuma Kabir da ya gane hakan sai ya murmusa kuncinsa kawai yana girgiza kai. Allah ya sa ni, tun a doguwar ajiyar zuciyar farko da ta sauke, da kuma numfashin da ta shiga saukewa daga baya, yaji ba zai iya tashinta daga baccin ba, dan daga yanda ta ke yinsa yasan baccin yay ma ta daɗi, kuma shi kansa ya sa ni, ba wani baccin daɗi ta ke ba within these days, dan waccan ranar yana jinta da Alhassan tana faɗa masa cewar ita nutsuwa a tare da mutum biyu ta ke, Maminta da Ya Kabir ɗinta, kuma a yanzu duk basa kusa da ita, saboda haka ne baccin bata yinsa a daɗin rai sai dai ɓarawo ya ɗauketa. sai ya lumshe ido ya jinginar da kansa ga pillow da akasa masa ta baya, kamin wucewar awa guda Maryam ɗin ta farka, farkawar tata kuma tazo daidai da shigowar Zulai ɗakin, inda ta nufi wajen da room heater ke ajiye ta kunna bayan ta ajiye flask ɗin abincin da ta shigo da shi. "Ba sai ka kira waya kace azo a kunna maka heater ɗin ba, ɗakin duk ya ɗau sanyi". "ai Inna sanyin ba ya wani ratsani ne shi yasa". "lallai lafiya ta isheka, to da Ahmad ya shigo yay maka gashin ko ya?". "a'a Innah". "to ka shirya dan lokacin yin gashin ma ya wuce". ta faɗa tana buɗe toilet ɗin ɗakin ta shiga. tana shigar na ɗago kaina daga kirjinsa na shiga magana a hankali ina cewa,"lokacin da Inna da Ƴaƴanta ke neman yafiyarmu akan laifukan da suka aikata mana wanda bamu sa ni ba, kai da kanka kace na yafe musu, rayuwar nan ba komai bace, ubangiji ma muna masa laifi yay mana afuwa, balle kuma a tsakaninmu ƴan Adam...to dan me ni ba zaka yafe min ba Yayana?". sai dai abin da ƙwayar idonsa ta nuna min a lokacin shi ne, na tashi na basa wuri. ina miƙewa Inna na fitowa daga toilet ɗin, ta ƙaraso da robar ruwan zafi a hannunta ta ajiye, sannan ta umarce ni da shiga toilet na ɗauko ma ta towel. bayan na kawo ne ta ke cewa dani,"ke ni ai na manta ma Yayanku Ahmad na kiranki". murya a ƙasa na amsa da cewan,"to Inna". sannan na juya na fita daga ɗakin, dama ko babu kiran Ya Ahmad ba zama zan ƙara yi ba bisa dalilai biyu, bana iya zama a san da ake masa gashin karayarsa, kuma ba zanci gaba da zama ba alhalin ya nuna bai son ganina, kuma ba zai ƙara ganina ba a part ɗinsa ba insha'Allahu. a compound na tarar da Ya Ahmad ya fito daga part ɗinsa, ya bini da wani mugun kallon da yasa nayi saurin ɗauke idona daga barin kallonsa. "saƙon da na aika miki ne bai isa gareki ba?, Maryam kin koyi wata rashin kunya ko, me kike nufi da hakan?". ya faɗa cikin muryar faɗa, ni dai baki kawai na tura gaba nayi part ɗinmu, ni faɗansa na ci min rai, ya fiya jarabar masifa, idan yana so ya daki mutum kawai sai ya takali laifi ya ɗora maka, shi yasa ranar nan da Jamila ta kai ƙararsa wurin Baba naji daɗi, ta ko'ina Ya Kabir ɗina yafi shi daɗin sha'ani, yanzun me na masa da har yake kiran na koyi rashin kunya. ina shiga parlo na gamu da sababin Yagana wadda ke tsaye bakin ƙofar ɗakina tana jiran dawowata, ta riƙe ƙugu sai karkaɗe karkaɗen ƙugu ta ke yi, tana jefa min harara tace, "yauwa Uwar masu Sharri barka da dawowa, dama dawowarki nake jira ai kowacce wacce...kamin na juye miki masifar tawa, ina da ina kika je kika yanka min mugun sharrinki me hawa kai, kamin gurin shi Uban nawa da kikai ƙarata wurinsa". da shirunta da dariyata suka haɗu a lokaci ɗaya, ban ankara ba ta ƙwala min ludayin hannun Nawwara da ta karɓa, na sa ki ƙara ina ja da baya ina sosa wurin. "ni dai Rakiya iyakar tsayin rayuwata ba'a taɓa min sharrin da ya kai naki ba, ban san haka kika girmama a wajen yiwa mutum sharri ba Maryam Guntsi, munafuka ai da kin faɗa min kina da wannan mugun halin da tuntuni na raba hanya da ke". ni dai dariyar ma da nake ta hanani jin ba'asin wannan bambamin da takeyi, da ta kai maƙura da dariyar tawa sai ta wawuri takalmin Basma tayo kaina da shi, ni kuwa na art
🏠