a yatsun, ban san ya akai ba, sai na tsinci wani guntun murmushi a gefen leɓena.
ta yanda yake janyoni a hankali na fahimci me yake nufi, dan haka na koma na kuma duƙawa a gabansa, kaina a ƙasa nace,"Ya ka haƙura?". kai ya gyaɗa min alamar a'a. "Ya me yasa to?." nanma kafaɗarsa ya ɗaga ba tare da yay magana ba. sai kawai na tafi zuwa jikinsa na kwantar da kaina saman ƙirjinsa ina faɗin,"please Yayana, kai fa baka fushi, balle fushi da Maryam ɗinka...Yaya idan ma ba zaka min afuwa cikin ruwan sanyi ba to na yarda dan Allah ka hukunta ni ta wata hanyar amma bata wannan hanyar ba, fushi da ni! hakan na min ciwo a zuciya matuƙa." inda ace da dutse a kusa da ni zan iya cewa maganar da nayi da shi nake ba da Ya Kabir ba, dan duk sammakal, ni da za ace zai buɗe baki yace wani abu ko da da faɗa ne wallahi zanji daɗi fiye da wannan shirun da yake min.
abinka da mai ruwan ido akan Ya Kabir ɗina, sai kawai naji wasu hawayen da ban san da su ba sun shiga sauka, maimakon na tashi saina ƙara lafar da kaina a ƙirjinsa, yayinda kunnuwana ke juyowa yanda heart ɗinsa ke beating very fast. duk da ba ganinsa nake ba, amma a yanda naji hannunsa me ɗan lafiyar ya ɗago zuwa bayana, na fahimci wannan kewayenin da ya saba zai yi, amma sai naji ya dakatar da hannunsa ga kaiwa hakan a san da Ya Ahmad ya shigo ɗakin bakinsa ɗauke da sallama.
abu guda ɗaya kawai na sa ni a wannan sallamar tasa, shigowarsa ta haɗe ne a lokaci ɗaya da saukar ajiyar zuciyoyinmu, kuma yanda naji Ya Kabir ya doki ƙasan carpet ɗin a hankali nasan hannunsa a dunƙule yay hakan, tabbacin alamar ƙorafin rashin cimma abin da yaso yi.
"No Sir, i don't think that is all planned." yay shiru na ƴan sakanni kamin ya ƙara cewa,"Yes Sir, actually abin da ya faru a lokacin na fita, so i don't know ko after fita ne Joshua ya duba su, saboda tun da nace musu kace they should bering refference before you sign on the pappers suka ce sun haƙura da contract ɗin". ya kuma yin shiru na tsawon daƙiƙa guda kan ya ƙara cewa,"oak Sir i will see on it by tomorrow insha'Allah". "thank you too Sir, bye".
cewar Ahmad kenan yana kai ƙarshen wayar da ya shigo ɗakin yana yi, ya zura wayarsa a aljihu yana mai neman kujera ya zauna tare da cire hular da ke kansa ya ajiyeta a gefensa, sannan ya dubi Kabir da ke kallonsa tun bayan gama wayar tasa yace da shi,"Sannu, ya sauƙin jikin?". "da sauƙi, wannan hannunma naji ya daina tsamin kamar da". Kabir ɗin ya faɗa yana nuna masa hannunsa na dama da yatsunsa ke tsarƙe da na Maryam, wacce tun shigowar Ahmad yake cikiniyar ya zare yatsun amma taƙi bari.
"Dr Yusuf ɗinma ya kirani yanzu ba jimawa, yace zuwa dare zai shigo wai ayyuka ne sun masa yawa a office ne yau amma kayi haƙuri." "babu komai tun da dai lafiya, ni dama har ga Allah na gaji da zuwansa...ba son allurar nan nake ba wallahi". fuskar Ahmad ta washe da gajeriyar dariya kamin yace,"kai dai ka shiga uku, wai dan Allah sai yaushe zaka daina tsoron allura ne, haba sai kace ba Gentle Man ba". "to ai ba'a bar so bace Malami balle kace min ragon namiji". "kaima gashi nan ka faɗa da kanka ai". Kabir ya ɗan harare shi da cewar. "wai meke faruwa a office ɗin naku?". "ka bari kawai, wani company ne yake neman yasha damu, su na so mu haɗa partnership da su sai MD yay bincike akansu aka gano cewar kuɗaɗen bogi suke turawa, to bamu san wa yay musu signing ajikin takardar ba kuma exactly irin na CEO fa nake faɗa maka, alhalin shi ba ma ya ƙasar". Kabir yace,"tsananta bincike za ku yi, munafikin na cikin staff en...yauwa next week zamu fara exams kuma kasan na faɗa maka". "ehh ban manta ba ai, jiya ma munyi chart da Abdurrahim ɗin, amma insha'Allahu ma kamin time ɗin hannun naka zai yi normal ka sami damar yi, Allah ma ya taimakeka online ce".
shiru ya ratsa tsakaninsu, kuma a wannan shirunne Kabir ya lura da irin kallon da Ahmad ke bin Maryam da shi ta wutsiyar idonsa, Maryam ɗin da tayi bacci a yanda ta ke ajikinsa tun shigowar Ahmad, bai san wacce iriyar yarinya bace ita, son jikinta yay ma ta yawa sai kace mage, haka bacci sai dai in bata kishingiɗa a jikin mutum ba, tun da can ma haka suke da shi, da ta ɗan kwantar da kai a kafaɗarsa zata fara lumshe ido, kuma yana ganin hakan zai ce ta miƙe akan cinyarsa dan yasan ƙarshen zancen bacci ne, amma Gwaggo kam ɗaleta takeyi tace ita bata son wannan lalacin.
"ita kuma wannan fa?". tambayar Ahmad ɗin ta shigo ta cikin shirun da ya ratsa ɗakin yana mai masa nuni da Maryam.
"rigima mana". "me aka ma ta?". "shopping ta ke so akaisu ita da Basma, Yagana kuma tace a'a sai an kwan biyu saboda kashe kuɗinsu yay yawa, to kuma tazo nan tana ƙorafi nace taje ta sameka wai kaima haka zaka ce a'a, kuma kasan hali ai ba sai na ƙarasa maka ba". Ahmad ya sauke numfashi, bayan ya sosa gashin girarsa yace,"kai kake biye ma ta, ya kamata zuwa yanzu kasan yarinyar nan ta girma amma sai kai ta ƙara biye ma ta tana jin kanta kamar ƴar shekara 2 ko 3. kalla fa wata ƙatuwa da ita ajikinka wai sunan