NOVEL SHARES -
e min ta zuba masa, na shiga ba shi abincin yana karɓa bisa dole, cikin ɓacin rai dan ga hakan nan ya haska a fuskarsa.
abin da bata sa ni ba shi ne, Kabir ƙara maimitawa zuciyarsa yake yi cewar babu wani abu da zai so a rayuwarsa ya kasa sadaukarwa da ɗan'uwansa, ƙanensa Ahmad, ko menene shi, kuma duk girman abin nan, sai dai idan Ahmad ɗinne da bakinsa ya furta masa cewar ba ya so ɗin ya haƙura.
*Plss Comment,Vote&Share.*
[7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
_Shafin Sadaukarwa ne gareku FITATTU BIYAR FANS GRP, ina matuƙar jin daɗin yanda kuke bibiyar wannan labarin da yanda kuke ƙarfafa min gwiwa, I love you so much Allah ya faranta muku._
*(39)*
idan har zai iya bada rabin jininsa ga Ahmad saboda kawai son da yakewa ɗan'uwansa, to ba ya ganin akwai wani abu da Ahmad zai biɗa a rayuwarsa yaƙi ba shi damar samu matsawar hanyar samar masa bata fi ƙarfinsa ba.
hoton wani lokaci can baya ya shiga haska masa a cikin idonsa, lokacin da ya ke shekara 22 a duniya, Ahmad kuma na 21, wannan lokacin da su kai accident kan hanyarsu ta dawowa daga makaranta, Ahmad ya sami rauni sose da har saida aka buƙaci jini, a wannan lokacin kuma Malam ba shi da kuɗin da za'a saya ledar jini har guda uku, aka kuma gwada duk wanda ya dace a gwada acikin siblings nasu amma babu jinin wanda yay daidai da na shi sai shi da Malam, shi kuma Malam a lokacin babu damar a ɗebi nasa kasancewar ba shi da cikakkiyar lafiya, dan haka ya zagaya ba tare da sanin kowa ba, ya fasa bankin ƙasarsa ya bada 20k sannan ya roƙi likita aka ɗebi nasa har leda biyu aka sakawa Ahmad, duk da cewar likita ya gargaɗe shi akan zai iya samun matsala idan aka ɗibi jininsa da yawa haka tun da shi ma jinin ba isarsa yay ba, yace ba shi da damuwa idan har ɗan'uwansa zai sami lafiya, shi zai iya sadaukar da rayuwarsa ma akan Ahmad.
kuma tun da aka ɗebi jininsa ikon Allah ne kawai ya rayar da shi, amma yasha baƙar wuya, dan da taimakon Allah da taimakon Gwaggo da tai ta sayar da abubuwanta ana siya masa abincin da zai dinƙa ci na ƙarin jini, tukunna lafiya ta samu gare shi, kuma har yau, har kwanan gobe babu wanda ya san da cewar akwai jininsa a jikin Ahmad...to idan har zai ba shi jini a lokacin da shi ma ba isarsa yay ba, mene a rayuwarsa zai kasa sadaukar da shi gare shi? babu! babu shi ba'a halicce shi ba, ya sa ni babu wanda ya san da cewar Ahmad na son Maryam, kamar yanda ita ma Maryam ɗin bata san da hakan ba, haka kuma shi ma Ahmad ɗin bai san da cewar ya fahimci soyayyar Maryam a tare da shi ba, kamar yanda hakan ta kasance, kamar hakanne zaisa ya zame kansa daga zuciyarta da tasa, ba tare da ya bari kowa yasan dalilin hakan ba, ai dama shi bai taɓa furtawa kowa cewar yana sonta ba illa Akila balle har hakan ya zam masa wani babban ƙalubale, Allah ya sa ni yana sonta, amma akan ɗan'uwansa tabbas zai iya haƙuri ya zama me juriya akan rashinta, zai bar masa ita, wannan alƙawarinsa ne matuƙar yana nunfashi, sai dai idan shi Ahmad ɗinne yace ya fasa, zai ta ɓoyewa Ahmad wannan Son da bai san ya nayiwa Maryam ba kamar yanda shi ma ya ɓoye masa nasa sai shi ne ya fahimta.
ɗigar ruwan hawayen da ya sauka bisa cinyarsa ne ya katse dogon tunaninsa, ya juyo da ƙwayar idonsa gareta yana mai kallon fuskarta da laɓɓanta da ke magana cikin muryar kuka, mai shaida wani rauni daga ƙasan zuciya.
"Ya Kabir dan darajan Allah kai min afuwa akan laifin da na maka bisa kuskure, wallahi tallahi banyi da gangan ba, ko me nayi banyi da sanina ba, dan Allah kayi haƙuri na tuba ba zan ƙara ba, amma ka daina fushi da ni haka...Ya wallahi zuciyata har zafi ta ke min akan hakan, ka kalla fa yanda ta ke motsawa a irin kumburin da tayi." na ƙarasa maganar ina masa nuni da ƙirjina daidai saitin zuciyata, sai kawai ya tsurawa saitin zuciyar tawa ido, daga can ƙasan ƙwayar idonsa yana hango irin yanda zuciyarta ke harbawa da irin yanda salon tasa ke harbawa.
ita ya kamata ta ba shi haƙuri ko shi ya kamata ya bata haƙuri?, shi da ya saba mata da sonsa, kulawarsa, damuwarsa tun bata san kanta ba, ƙwarai ya san zata shiga damuwa, damuwar da ko kaɗan ba ya jin daɗinta, yana ƙoƙarin danniya ne kawai da kauda kai gefe.
"Ya Kabir dan Allah". na ƙara faɗa ina kama kunnuwana da karayar da kai gefe, gami da yin narai-narai da idanuwa ina ƙoƙarin fashewa da kuka. sai kawai ya rufe ido for a while kamin ya buɗe ya saukesu a saman fuskata da na kwaɓe baki irin na shagwaɓaɓɓu, wanda hakan ba ƙaramin burge shi yay ba, dan saura kaɗan ya saki murmushi amma sai ya danne hakan, ya sake kauda kai kamar bai ji me na ke cewa ba koma bai san da zuwana wurin ba.
ganin ba shi da niyyar saurarena kawai sai na yunƙura zan miƙe cikin rashin ƙwarin jiki da jin daɗi, ga mamakina kamin na kai ga miƙewa sai naji ya riƙo hannuna, na waigo a hankali ina dubansa, still idonsa naga inda yake kallo, yatsunsa ne kawai acikin naw