an sauko min kamin nace,"ka faɗawa Mami ramuwar gayya da ɗaukan fansa aiki ne na yahudu da nasara, saboda haka ba su dace da ɗan musulmi ba ko kaɗan, manzon Allah da kansa yace kada muyi koyi da su. saboda haka ina roƙonta da tayi haƙuri ta yafewa Daddy nah...ai abin da ya faru a tsakanin rayuwarsu zuwa rayuwar Alhassan da Maryam ɗin da suka haifa wannan tsananin rabo ne da ƙaddara, ƙaddarar da babu wanda ya isa ya kauce ma ta, amma dan Allah tayi masa afuwa kar mu zama marayun ƙarfi da yaji".
yay nisa sannan yace,"ke me zai hana ki kirata ki faɗa ma ta". "Alhassan ni ban san me nayi ma ta ba, tun da ku ka koma bama wani long conversation da ita, kana kallo ma ai tun kamin ku tafi muka koma kamar wasu sirikai, duk yanda naso na keɓe da ita na mata magana bata bani dama". "kunfi kusa, ni da Ummina ido ne namu". ya faɗa, kuma kamin nace wani abu ya kuma cewa,"Ya sauƙin jikin Ya Kabir ɗin?". na sauke wata doguwar ajiyar zuciya sannan nace,"da sauƙi, kawai dai har yanzu ba ya taka ɗaya ƙafarsa...shi ma yace na fita a sabgarsa babu ruwana da lamarinsa, jiya ma saura kaɗan ya mareni shi yasa nace insha'Allahu in dai sunana Maryam tsakanina da shi ido".
kuma da haka muka ɗauki hirar makarantar da Mami ke nema min addimission a can Qatar ɗin, sati biyu kenan da zana aprivate waec ɗin da ta biya min, tace wai nayi girma da yawa a secondry, kuma tun da ina da ƙoƙari sosai ƙwaƙwalwata naja to kawai da waec ɗin nafi dacewa...ni kam sam idan muna waya da ɗan'uwana kamar kar mu rabu na ke ji, shi yasa duk na ƙagu Ummi ta dawo daga tafiyar da tayi muma mu wuce Qatar ɗin, dan Allah ya sa ni ina kewan kasancewa kusa da Mamina sosai.
*03:00am.*
"Yaya dan Allah ki saya min wannan takalmin". Basma da ke shigowa cikin ɗakina da na ke kwance ta faɗa tun bata ƙaraso inda nake ba. na ɗago ido na dubeta ina kallon ikon Allah, ita dai kullum na siya ma ta na siya ma ta, ta maidani kamar wata asusun bankinta, ga shi ni kuma ina bala'in son ƙanwata tilo ɗayan da Gwaggona ta tafi ta bar min. a yanzuma da ta ke shigowan kamanninta suka riƙiɗe suka koma min na Gwaggona, ban san lokacin da idona ya cika da ruwan hawaye ba, da kanta da ta lura da hakan tasa hannu ta goge min.
"Yaya za ki saya min ɗin?". ta ƙara tambaya tana marairaicewa, nayi ma ta shiru ina ci gaba da danna sabuwar wayar Mami da na karɓe ranar da za su tafi. wadda babu komai acikinta sai tarin hotunanta, kuma su suka zame min abin kallo a kowanne lokaci da nake tare da wayar, ko ma bana tare da ita hoton surar Mamina ba ya barin haskawa a idona.
"shikenan tun da ba za ki saya min ba na fasa shiryaku ke da Ya Kabir". ta faɗa tana ƙoƙarin sauka daga kan gadon ta fita, nayi saurin kamota ina cewa,"haba mana my little Sis, kin kalla na taɓa ƙin saya miki abu?, Allah kam zan saya maki yi haƙuri kinji".
sai ta noƙe ta juya min kai da cewan,"ni dai na fasa shiryaku, takalmin ma na fasa bana so". sai kawai na marairaice ma ta ina cewa,"haba lil sis, Gwaggo fa tace mu zama masu kula da junanmu". sai tayi murmushi tana ce min,"to kije ki ba shi abincinsa, na kalla yana jin yunwa kuma ya kasa ɗaga hannun". maganarta tasa na zuro ƙafata ƙasa babu shiri nayi waje, ina fitowa parlo na tarar da Ya Amadu da Yagana sai abokansu da suka zo yiwa Ya Kabiru sannu, na tsuguna na gaishesu sannan nayi hanyar fita, na sauka daga kan steps ɗin entrance ɗin parlonmu kenan sai naji Ya Amadu ya kirani. ko da na juyo sai na kalla kaman idonsa ba'a kaina yake ba, kiranma kaman ba shi yay ba, kawai sai na tsaya ina kallonsa, ya juyar da ƙwayar idonsa zuwa gefe tare da kasa tantance abin da yake kallo a wurin.
bata san ta ƙasan ido yake kallonta ba, gaba ɗaya ya kasa tantancewa, bai sani ba kyau ta ƙarayi ko kuma akasin haka, idanuwansa na kalle masa ne kullum kamar ana sauya halittarta, abu guda ya sani shi ne kowanne lokaci tana canjawa, a kowanne sakan ya ɗora idonsa sai yaga ta sauya kamar wahainiya.
a yau da tayi shigar english wears ɗin da ya taho ma ta da su daga lagos, tabbas idan a hanya ne ya ganta zata wuce ya wuce ne ba tare da ya shaidata ba, ya motsa leɓensa da murmushin da bata gane ba.
"Ya Ahmad". na kira sunansa ba da irin wancan sunan ƙauyen da na saba kira ba, dan Ummi ta hanani, tace yanzu mu ƴan gayu ne, dan haka duka sunan ƴan gidan ya sauya a bakina daga yanda na ke faɗarsu ada.
a tsakiyar fuskata ya sauke idonsa, yana ƙanƙance shi saboda hasken ranar da ke dallare masa ido. "Ya kamar naji kayi kirana". "ehh aiki zan sa ki ciki, kizo ki dafawa baƙin nan indomie, dukansu basa cin alala."
"Ya Ahmad ai Nawwara(ƴar aikinmu) na ɗakinta, dan Allah ka kirata...ni zanje Ya Kabir na kirana ne". wucewar daƙiƙa kamin ya gyaɗa min kansa, sannan na wuce na tafi zuwa part ɗin Ya Kabir, ina shiga na tarar yana ƙoƙarin yanda zai yi ya ɗauko spoon cikin ƙarfin hali, dan haka na ƙarasa gare shi da sauri, ba tare da na bari ya bani dama ba na tsaida hannunsa, sannan na matso da plate ɗin abincin da Basma tac