, komai anyi shi da favorite colour ena white and blue, ɗakina na kallon na Basma sai na Yagana dake daga can ɓangrenmu, tamfatsetsen parlonmu kuwa ba'a magana.
dan haka ina fitowa daga wanka na baje akan lafiyayyan gadona dan huta gajiya, sanyin Ac sai ratsani yake, maimakom baccin da na ke saka ran zanyi sai na kasa, wani tunanin na daban ya shiga cikin kwanyata, tunanin da ke neman hargitsa min lissafi.
_shikenan komai yazo ƙarshe, sirrikan sun bayyana, komai ya warware, sabuwar rayuwa ta fara..._
*Bayan Wani Lokaci, Qatar, Turakar Mai Martaba.*
Almustapha da Imam(Joseph) tare da Ibrahmi(Obi) su ka shigo cikin turakar. su ka ƙarasa har gaban Mai Martaba inda suka zube a ƙasa gaba ɗayansu su ka kwashi gaisuwa, Mai Martaba ya amsa tare da sanya masu albarka, da kuma ƙarayi musu adu'ar tabbatuwa acikin musuluncin da suka karɓa a kwanakin baya da suka shuɗe, a wancan ranar da Almustapha da Major suka je asibiti, bayan dawowarsu gida ne an gama bikin mutuwar Madam Gloria da Madam Merry, Almustapha yazo har kano ya ɗauki Malam da Malam Liman suka je can abuja, su ka riske Major inda Malam Liman yay masa wa'azi me ratsa jiki, kuma da ya ke yana da rabo, a washe gari ya kwashi ƴaƴansa da jagorancin Malam Liman su ka zo har nan Qatar ya karɓi musulunci daga hannun Sarki Shaik Samim bin Hamad wato sarkin Qatar mahaifi a wurin su Aaliya.
yanzu haka Major yaje ƙasa mai tsarki inda ya fara ɗaukan darasi na ilimin addini a wajen Shaik Mufti Mahek, sai muyi musu fatan Allah yasa rabon ya kai su har aljannah.
Hirar da Mai Martaba ke yi tasa ce shi da Almustapha, sai Ibrahim da ke sako baki jefi-jefi, kuma su na tattaunawa ne musamman akan wata ma'aikata da Mai Martaba yake son mallakawa Alhassan ita, yake so Almustapha ya shige masa gaba a harkar, tun da shi Alhassan ƙaramin yaro ne, har yanzu da sauransa, duk da cewa idan ka ganshi ba zaka ce masa mai shekara goma sha takwas ba, zaka ce ya bawa shekaru ashirin baya, kuma yaron akwai hankali dan halinsa ma na manya ne, zai iya yin abin da ba ma lallai wani babban yayi ba.
gaba ɗaya cikinmu babu wanda ya san da musuluntar Daddy da sauran ƴan'uwana, sai bayan da aka sallami Ya Kabiru daga asibiti, ranar da Mami da Ummi su ka dawo Qatar, a wayar da suka yo ne suke shaida mana da duk abin da ya faru, daga baya kuma Alhassan ke tsegunta min zaman sulhun da Abi yaywa Mami da Daddy, sai dai ko kusa Mami tace ita dai abin da ake tunanin zai faru tsakaninsu ba zai taɓa yiwuwa ba. damuwa ta haska ƙarara a saman fuskata na buɗa baki nace da shi,"amma kai mene view ɗinka akan hukuncin Mami na ƙin amincewa auren Daddy?, ni dai gaskiya zan so ace ta haƙura suyi aurensu, ko dan Allah ya ƙara rufa mana asiri".
da ya ke Alhassan A ne, ya saki wata siririyar dariya kamin yace,"ke ki kwantar da hankalinki, batun cewan ma Mami bata son auren Daddy daga baya ne, dan ba kya wurinne, amma da tsab idonki zai hango miki kwantacciyar soyayya a idanun junansu". ban san lokacin da na saki dariya ba, har ina kifawa akan kafaɗar Yagana da ke kusa da ni, nace da shi,"kai dai baka da kunya, iyayenka ma baka bari ba".
dariyar ya ke shi ma yace,"hmm to ai bari kiji na ba ki labari, ranar da Daddy zai tafi saudia ina kallonsa da yamma ya tarfa Mami yana lallashinta, na faɗa miki ya koma kaman ƙaramin yaro fa a gabanta, ita kuma sai wani yauƙi ta ke tana cewa wai ita sai ta rama wahalar da rayuwarta da yay, ke ba ki kalla a yanda ta ke maganar ba sak ke idan kina shagwaɓa, ni kuwa na riƙe haɓa nace ikon Allah, ni da Ummi da Akhy Almustapha muna gefe muna musu dariya". a wannan karan dariyar da nayi har da dukan Yagana, ba kuma wai ina sa ni ba, amma ƴar tahalikar nan sai ji nayi ta ɗale min gadon baya babu shiri na miƙe daga kusa da ita.
still ban bar dariyar ba nace,"ina jinka ci gaba da bani ina sha". yace,"gulmawuya to naƙi na ƙarasa". "ah yi haƙuri Yayana na kaina". a wannan lokacin murmushi yay mai sauti, yaci gaba da bani labari cikin nishaɗin da muke ciki.
"ba ki san me ba, da naga Mami na neman wahalar min da gyatumi ta sa shi kuka sai naje na kutsa a tsakaninsu, ke ba ki kalla wani abin dariya ba lokacin da suka ganni, sai ga Daddy na susar ƙeya wai naje na ɗauko clipper nayi masa aski ance masa na iya aski ni ke yiwa Abi ma, ni kuwa nace masa ai Mami ce uwar ɗakina, ita ta koya min dan haka idan da gaske me kyau yake so to su sulhunta kansu a daren nan gobe a ɗaura musu aure, a tare su ka sakar min ranƙwashi fa, Mami har da murɗe min kunne saboda nace idan ba tsayuwar sulhu su ke ba to a faɗa min gaskiya...ina faɗa maki ma Abi yace da Daddy ya dawo daga umara za'a ɗaura aurensu, ita kuma Mami tace bata yarda ba, ya za'ai sai da za'ai bikin ƴarta kuma ayi nata, Ammi kam tace to ki zauna idan anyi na ƴar taki ta sami ciki ta haihu ayi naki...ni dai ina cin dariyar drama, Malama ki baro wannan ƙauyen kawai kizo a dinƙa yi a gabanki ba kike kirana ina ba ki labari kuma ba kya biyana ko sisi".
na kai hannu na goge ƙwallar da ke nem