shi a ɗakin amma yaƙi bani dama, lokacin nan da Yagana ta fita nace masa. "Ya Kabiru inata maka sannu baka amsa ba". bai responding nawa ba har sai dana tambaye shi sau uku tukunna yace da ni,"sannu indai daga bakinki ne bana sonta, ba sannunki kaɗai ba, ganinki ma ba so nake ba". furucin nasa kuma daya sani a damuwa ya ɗaga hankalina a lokaci ɗaya.
"ki tashi kuje gida ki wanka, zuwa anjima sai ku dawo bayan kun huta". maganar Ummi ta dawo dani daga duniyar tunani, nace da ita,"Ummi ni ba sai naje ba, Yaganan dai ta tafi". "haka za ki zauna kina tsami da warin asibiti?". sai Mami tace,"barta zuwa anjima ma tafi tare, zanje ganin gwamna nan da 12". Ummi tayi knodding kanta kawai tana ci gaba da karanta takardar da suka amso daga wurin likita akan ciwon Ya Kabiru. kuma barin kallona da zanyi daga kanta muka haɗa ido da Mami wacce ke magana a wayar da ke kare a kunnenta, tayi min nuni da cinyarta na tafi na zauna akai inata farin ciki, zaman nawa ya zama lokaci ɗaya da gama wayartata, tasa hannu ta juyo da fuskata tana goge min wani abu da ban san mene shi ba, a yayinda a gefe guda gangar jikina da ruhina ke daɗa tsargawa da so da ƙaunar mahaifiyata.
"dilla tashi, sai kin karya ma ta ƙafa". Alhassan yay maganar cikin ɗagowa kaman zai fizgoni, na turo bakina gaba kamin nace wani abu Mami ta rigani da cewar,"sai kasa ta tashi ai tun da ƙafar taka ce". ban san lokacin da dariyar ta suɓuce min ba ina kallonsa tare da haɗa masa da gwalo.
Mami kuma tace,"gyara zamanki da kyau Autata, cinya taki ce bata kowa ba".
Yagana da ke yafa mayafi za su tafi ta taɓe baki da cewar,"goɗe goɗe da ke akan cinya ko kunya". nace,"Yagana bafa a taki na zauna ba". "yo kice ma za ki zauna akan tawa ki gani". sai kuma ta juya kan Mami da cewa,"wannan ƴa taki dai ba halin ƙwarai gareta ba, dan haka kar ki nuna ma ta son da zai sa ta sangarce, wahala za ki sha wurin tanƙwarata, ko da yake anan dai albasa tayi halin ruwa". na kalli Yagana na ɓalla ma ta harara saboda jin haushin maganarta ta ƙarshe, sai ta murmusa kunci da cewa,"Allah na kaɗai na ke tsoro, dan haka Maryama dai-dai na ke da hararki wallahi, ni Rakiya ba, da ni kike zancen, ai akwai ranar ƙin dillanci". harar tata dai na kuma yi bance ma ta komai, su na gabanin fita a ɗakin tace da Ya Kabiru,"kai kuma Malami ka daure ka zama namiji ka tashi haka, ni ba zai yiwu na dinga zaman jinyar asibiti ba, jiya haka naita faman tsartar da yawu kamar wata me ƙaramin ciki. saboda haka ka warware dan tafiyar nan tawa da ka ga nayi ba zan dawo ba, iyakaci na ke maka aiken sannu...idan kuma na biya Amarya ta zo ta dinƙa jinyarka ne to?." ta ƙarasa zancen nata tana ƙunshe dariyar da ke neman fitowa, shi kuma yace,"in dai kin shirya yin takaba ki aikota ai ba wani matsala bace Hajiya Yagana". sai ta dawo daga baya tana cewa,"au kai na manta ban faɗa maka ba, wannan ja'irar yarinyar ta min alƙawarin kujerar makkah fa, ka ma ta godiya idan ka gama ciwon bakin akanta."
da haka ta juya ta fita, har ta fita kuma ta dawo tambayar yace ko dai shi direban ba irinsu Mami bane shi ma ba ya jin hausa, dan indai shi ma irinsu ne to gwara a haɗata da dutse ta tafi ta san ta tafi da wanda bai san me ta ke ba da hujjah.
Ya Amadu da ke tsaye ya girgiza kai da cewa,"muje dan Allah kar ki cika mutane da magana". "ah toh Amadu idan ba za ka iya da maganar tawa ba ka toshe kunnenka mana ina dalili anan, haka kawai Allah ya tsagan baki kace ba zanyi magana ba...ni dai wannan hali naka na ba ni takaici, banda cuta ce da ba'a ƙaunarta ai sai nace dama kaine a maimakon Kabirun, haba sai kake takura min kamar wani Babana".
shi dai tafiyarsa yay ya barta a wurin, bayan yace da Alhassan ya taso su tafi tare, kuma Alhassan ɗin na zuwa wucewa ta gabanta ta riƙo rigarsa da cewar,"kai zagalo tsaya, Allah ya sa ni wannan tsayin naka tsoro yake bani, bari nayi gaba sai ka biyoni a baya". daga ƙarshe dai gaba ɗaya har ni akai tafiyar.
kuma abin da bamu sa ni ba da ni da Yagana da Ya Kabiru da ke kwance, shi ne, Mami ta saya mana sabon gida anan Saye ɓangaren masu kuɗin anguwar, ashe tun bayan saukarmu a ƙasar tasa aka nema ma ta gidan, kuma abin da ta bari su Baba suka kwasa a tsohon gidanmu ƙalilan ne duka ƴan abin da ba'a rasa bane da suka zama na amfanin dole.
gidan flat ne me kyau da part daban daban, dan ɓangaren su Inna Zulai daban, na Baba daban, ni da Yagana a ɓangare ɗaya, sai mazan gidan ma aka haɗasu ɓangare ɗaya kowa da ɗakinsa, Ya Kabiru da Ya Amadu kawai part nasu daban daban, tsohon gidan kuma tasa an bige shi ana gyarawa tace Baba sai ya zuba ƴan haya a ciki.
duk wannan bayanin sai a yanzu da muka taho Ya Amadu ke bamu shi, adu'a da sa albarka kuwa da Yagana keyi ma ba zai faɗu ba, dan tun kamin mu ƙarasa gida tace da Alhassan,"kai Zagalo kira min gyatumarka na ma ta godiya". shi da bai san me tace ba sai ni na karɓa wayar na kira ma ta ita.
nima sai da muka ƙarasa gidan na shiga godewa Mamina da naga haɗaɗɗan ɗakina da yanda aka ƙawata shi