bai hanasu bayyana ba, ta ko'ina bata yi kama da mutanen ƙauye ba, dan komai nata tsab. Bai san lokacin da murmushi ya suɓuce masa ba tunawa da yanda ta-ke tsiwarta har yaji inama kar ta daina ya sami damar ci gaba da kallonta.
Jin yayi shiru bai amsa gaisuwar da nayi masa ba yasa na ɗago kaina daga duƙen da yake, na sake gaisheshi dan ta iya yiwuwa a ɗazun baiji ni ba saboda muryata da ta ɗan sarke, ya amsa gaisuwar tawa ta biyu acikin taushin muryarsa me daɗin ji. Na fakaici idonsa dake kallon gefe wurin dana aje butoci zai ɗauka, kyawun halittar fuskarsa dana gani ne yasa na tsaida idona akan kwantacciyar sumar gashin kansa da babu hula, irin sumar da kana gani kasan ta buzaye ce. Na miƙe tsaye da sauri gudun karna tafka abun kunya ya kamani ina kallonsa, dan nasan halina na bada kai, a yanda nake da matuƙar son ganin abu me kyau banƙi nayi zaman daɓaro ba a wurin ina kalle shi. Na kama gefen mayafi ina ce masa,"Ya Kabiru ɗin baya nan sai dai ka jira shi yanzu zai dawo babu jimawa, amma Inna tace ko kirashi a waya za kayi, kuma wai a ƙaro maku ruwan alwalar ko ya isa haka?". Bai amsani ba sai bayan da ya kwance tsadadden agogon da ke hannunsa, wanda ni ban taɓa ganin irinsa a fili ba, sai me shigen kamarsa dana taɓa gani a hannun Obi abokin Ya Amadu, ya miƙo min agogon yace na riƙe masa, na rissina na karɓa da hannu biyu, tukunna yace,"babu damuwa zamu jirashi ya dawo ai, dan tunda muka iso garin nan na keta kiran wayar tasa bata shiga. Kicewa Inna mun gode, ruwan alwalar ya ishemu ai mu biyu ne kawai". Na amsa shi da to, naci gaba da tsayuwa ina jiran ya kammala alwalar da yake na ba shi agogonsa da ya bani riƙo, ko da ya kammala alwalar ya miƙe tsaye dubansa akaina, na tari nunfashinsa da miƙa masa agogon, yana saka maɓallin hannun rigarsa yace na shiga da shi gida na ajiye masa, idan suka shigo gaida su Inna zai amsa, sannan ya tambaye ni sunana nace masa "Mairo". Yace, "Maryam dai ko". Nace "a'a Mairo dai". Yace, "to ai shikenan Mairo sannunki, ke ƙanwar Kabiru ce?". Na ɗaga masa kai alamar ehh, Sannan na juya na tafi, ina ji yana kiran abokinsa me suna Jawad da ya zo yayi tasa alwalar lokaci ya ƙure, ko kuma shi yayi tasa sallar ya barshi, dan ya lura idan yana wannan wayar tasa baya la'akari da tafiyar lokaci.
Da shigata gida tunda na faɗawa su Inna za'a shigo a gaishesu ban zame ko'ina ba sai cikin ɗakin Gwaggo, na taka kujera na ɗauko wata kwallar ajiyarta da ke saman sif, na saka agogon aciki sannan na rufe na mayar. A tsakar gida kuwa tuni an shimfiɗa tabarma da babbar sallayar Baba wadda me anguwa ya bashi tsaraba dawowarsa daga saudiya, aka soka turare ɗan tsinke a jikin garu.
Mun gama cin dambun acca da Inna Zulai tayi mana shi a abincin dare, dambun yayi daɗi sosai, ina bakin rariya ina wanke hannu muka jiyo sallamar mutane, ban bar wurin ba sai sanda na gama kuskure baki, lokacin yaran gida duk sun gaishesu kowa ya koma ɗaki. Naja ƙafafuna na tsayar lokacin da idanuwana suka yi tozali da ɗan iskan saurayin ɗazu da ya ciwa Adawiyya mutunci, a raina nace shi kuma me ya kawo shi gidanmu?, kar dai ƙarata ya kawo, ko kuma tare suke?. ajiyar zuciya na sauke, ban yarfar da ruwan hannuna ba sai da nazo saitinsa, tukunna na wuce naja kujera na zauna, ina jinsu su na ta ɗan hirarrakinsu, su na faɗin ai ƙilama zasu kwana ne anan, domin basa son tafiyar dare, kuma kusan sun sauka ne a hanya tunda inda zasu sauka gobe yafi kusa da nan. ni dai Alla Alla nake Gwaggo ta tsagaida da maganarsu ita da buzu na amayar da abunda ke cikina ko na samu na huta.
Aiko shiru na gimlawa a tsakani na kada baki nace, "Gwaggo wai dama ƴan birni na cin arziƙin Ƴan Ƙauye ne? Ai ce nake a yanda suke jin kansu sunfi ƙarfin nan". Gwaggo ta wani juyo ta min wawan kallo, kanta kai ga magana Inna tayi caraf tace,"Mairo shiga ɗaki ki ɗauko musu mukullin ɗakinsu Kabiru". Oho dai duk korar da za'a min maganata dai ta isa in da nake so taje, kuma ko mutum yace zai fasa kwana a gidan ya dai yi alwala da ruwan gidan, ya kuma yi sallah a dakalin gidan, ya kuma shigo har cikin gidan ya zauna.
Ina shiga ɗakin Gwaggo na tarar da Adawiyya zaune gaban fitila tana rubutu a littafi, ni na manta ma da wani Home work sai yanzu, ta bani hannu muka kashe tana faɗin,"daɗina dake iya yaɓa magana". Nayi mata banza na hau gadon ƙarfenmu na kwanta, ba bacci nake ba sai dai nayi shiru ne kawai, a samana naji mutum tsaye ce nake ma ko Gwaggo ce dan haka nayi saurin rufe idona dan bana son ƙara haɗuwarmu sai gobe, kamin nan nasan ta huce da abunda nayi. Ni'imtaccen tafin hannun da ba zan mance da irin ni'imarsa ba dukkuwa da cewa sau ɗaya ne ya taɓa taɓani, naji an ɗaga kaina daga saman hannuna dana kwanta akai an maida min saman filo, na rumtse idanuna sannan na buɗe saboda yanda ɗumin hannun ke ɗumamamin jiki da wani irin yanayi. Na turɓune fuska na juyo cikin tsiwa ina cewa da Kulu,"wai ke Ba Gwaggo tayi min tsakani da ke ba". Naga ta kafeni da ido tana kallona, na murguɗa mata bak