kacin da tasa ni yi ma ta bincike ta gama buɗe min cikinta...ina Maryam ɗin?". ya ƙara tambaya a karo na biyu, kuma kafin Yagana tace wani abu na taso daga inda nake, ina takowa kamar wadda ƙwai ya fashewa aciki, irin takun tafiyar marasa gaskiya, irin takun tafiyar wadda ke tsoron amsar ɗanyan hukunci, kuma a lokacin dana ƙaraso bakin gadon, zan iya kiran kallo ɗayan da yay min da kallon tsautsayi, dan bada niyya yay ba, yay kallon ne bisa rashin sanin cewar ƙwayar idonsa zata sauka akaina ne.
"Ya Kabiru sannu". na faɗa muryarta na fitowa a hankali, da kuma rawar jikin da ban san ta mece ba, kuma sai naji sam babu daɗi da rashin amsa mini ɗin da yay, shin bai san a halin da nake ciki ba ne akan ciwon nasa? da har zai nuna halin ko in kula akaina, banfa iya bacci ba sai da Yagana tasa nurse ta min allurar bacci ta dole, amma har sanda aka min allurar ina zaune a gefensa, gefen wannan hannun nasa da nawa ke riƙe da shi da ban san lokacin da aka rabani da shi ba.
"naga kamar ruwan ya ƙare, ki cire masa tunda likita ya nuna miki yanda za kiyi ɗazu". Yagana ta faɗa a sanda ta juya tana faɗin,"Allah baka lafiya ya kuma bi maka hakkinka Kabiru, ba kai kaɗai ba dukanmu sai Allah yay mana sakayya tsakaninmu da waccan algunhumar matar Amarya, ƴar banza me kama da ƴaƴan birinya, tsinanna makirar mace, zamanta dai acikinmu kam ya ƙare, ƙwarai ta shammacemu kuma ta ɓata wayonta. wallah da muka je naso ofishin ƴan sanda nan naso an bani kulki na mummuƙawa ƴar banza a kafaɗa... kai bari nayi sallah naji masallaci na tayarwa".
na zagaya ta gefen inda aka saka masa ruwan, sai dai sam na kasa zare masa allurar da jininsa ya fara biyowa ta ciki kasantuwar ruwan drip ɗin ya ƙare, ba wai dan ba zan iya cirewar ba ne, a'a sai dan kawai ina jin ba zan iya cire masa ba, kaman zanji masa rauni ne, kuma bana so yaji zafin cirewar.
ganin jinin na ƙara fita da yawa na kai hannuna dake rawa kan butterfly ɗin, kuma kamin na kai ga ɗaga bandage ɗin sai naji ya riƙe hannuna ya ɗauke daga kai, ya juyo ya zare da kansa. sannan ya yunƙura zai miƙe daga kan gadon ya sauka ƙasa, sai nai saurin dawowa ta gaban nasa ina dakatar da shi cikin saurin muryar da ban taɓa yi ba wajen faɗin,"Ya Kabiru ƙafarka akwai ciwo, Dr yace karka taka". gaba ɗaya a wani kiɗime nayi maganar ina riƙe ƙafafun nasa na maida kan gadon.
ban kalle shi ba, amma a jikina nake jin irin kallon da yake bina da shi, kuma a wannan durƙusawar da nai sai naji ƙafafuna kamar an riƙe su, sam na kasa ɗagowa, sai kaina dake kallon ƙasan tiles ɗin, idona na zubar da hawayen da ban san dalilin zubarsu ba, abu guda da na sa ni shine ba zan taɓa yafewa kaina ba idan har na zama silar wanzar da ɓacin rai akan wannan fuskar ta Ya Kabiru.
wucewar kusan rabin sa'a kafin maganar Yagana ta haifar da kuzarin da ya gushe min lokaci baya kaɗan.
"ke ba kya sallah ne?". sai dana saka hannu na goge hawayen fuskata kan nace ma ta. "zanyi Yagana." tukunna miƙe na shiga banɗaki dan yin alwala.
ƙarfe goma saura su Ummi suka zo, kamin shigowarsu drivern Mami ne ya fara shigowa da manyan basket guda biyu kowanne shaƙe da manyan coolers na abinci, sannan Alhassan ya mara masa baya shima hannunsa riƙe da madaidaicin kwandon kaba da tarin fruites aciki. daga baya kuma saiga Mami da Ummi sun shigo, na miƙe da saurina naje na rungume Mamina ina ma ta sannu da zuwa, sai Ummi ta tsaya tana kallona a sanda ta harɗe hannayent tana jinjina kai, sai naji nauyinta ya kamani dan haka na sa ki Mami na tafi gareta ina murmushin dake bayyanar da haƙorana gaba ɗaya na rungumeta itama.
"a'a Maryam ki dai nuna min wariyar launin fatar kawai, na yarda zan ɗauka a hakan, ai daɗin abinma ina da Alhassan bake ɗaya bace". sai na ƙunshe fuskata ajikinta ina cewa,"to ai Ummi kece kika shigo daga baya, amma dake ne kika fara shigowa ke zan fara rungumewa kamin ita". tana murmushin itama tace,"ba wani nan ni ban tsaru ba". da haka muka kama hannun juna zuwa kujerar da zata zauna, na duƙa na gaisheta ita da Mami, Alhassan ɗin kuma dake hararata na murguɗa masa baki...Baba ma yace ai yaga alamar yanzu idona baya ganin kowa sai Mami kawai, dan yaga alama shima tun jiya na manta da shi, duk sai naji kunya ta kamani, dan cikinsu babu wanda ya faɗi ba dai-dai ba, yanzu hankalina gaba ɗaya na kan Mamina ne.
Alhassan ya yunƙuro zai ƙwalo min jarkar hannunsa akan murguɗa masa bakin da nai karaf idon Mami akansa tace,"ka buga ma ta sau ɗaya, ni kuma naita buga maka har sai kanka ya zama ƙwalele". gaba ɗaya akasa dariya har da Ya Kabiru dake amsar magani daga hannun Yagana. dariyar tasa kuma tasa ni jin daɗi, daɗin da har saida na motsa laɓɓana, sai dai kuma jikina yay sanyi sanda muka haɗa ido da shi naga ya ɗaure fuska.
karo na huɗu kenan tun daga farkawarsa, idan na gama fahimta a yanzu Ya Kabiru sam bai son ganina, fushi yake da ni, to laifin me na masa?, tambayar da bani da amsarta, kuma nai ƙoƙarin na sameta tun sanda ya zamana daga ni sai