a faɗi hakan ta juya dan ci gaba tafiya. sai a sannan taji yace,"where is Merry?". ba tare da ta tsaya daga tafiyartata ba ko kuma ta juyo ba tace da shi,"ni ƴata sunanta Maryam, kar ka ƙara kiranta da wannan ɗan iskan sunan tunda ba rainonka bace...kuma abin da ma zan sanar maka shine ka cire lissafin karɓarta dan ba abu ne da zai yiwu ba in har Aaliya na numfashi, kaji da kyau bada wai ba, wannan dai me zubin naka kana iya jansa ko daga yanzu domin shi na rayu da shi, ita kuwa yanzu ne zamu soma rayuwa tare".
***"magungunan da aka rubuta masa su na da tsada sosai, gasu nan ku hanzarta siyo su bada jimawa ba...kar ku ɗaga hankalinku da yawa saboda komai yazo da sauƙi...sai dai allurar da muka yi masa ce zata iya kai shi zuwa gobe, amma kar ku wani damu da rashin farkawarsa muna so ya samu hutu ne."
duk wannan bayanin na fitowa ne daga bakin Dr ɗin da ya gama duba Kabir a yanzu, yana isar da bayanan nasa ga Akila(Kulu) da ke tsaye tana sauraronsa, yayin da Yagana ke zaune a kan wata kujera daga can gefe tayi jugum ƙirjinta na luguden fargabar abin da likitocin zasu ce a ga me da Kabir duba da mawuyacin halin da yake ciki, kuma a duk wani motsi na zuciyarta tsinewa Amarya take.
Mairo kuwa na zaune akan kujerar da Akila ta tashi ta barta, idanunta na manne akan Kabir da ke kwance kamar matacce, da kuma farar shaddar da ke jikinsa wadda gaba ɗayanta ta ɓaci da jini kamar yanda shi ma fuskarsa ta ɓaci da jini a ɗazu kafin likitoci su gyara shi, an nannaɗe wurin ciwukan da bandage.
a wannan lokacin zuciyarta na bugawa ne da motsin fargabar halin da Ya Kabiru ke ciki, yayin da a gefe guda kuma kalaman Ummi akan Amarya ke yawo a cikin kanta, wannan Amaryar da ta ɗauka tamkar Gwaggonta, ta kasa yarda da kowacce kalma ɗaya bayan ɗaya da ke fitowa daga bakin Ummi akan ƙazaman abubuwan da Innarta ta aikata, amma kuma a san da Baba ya kira yana tabbatarwa da Yagana gaskiyar lamarin sai taji kanta yay ma ta nauyi, komai na cikin kanta ya ɗaure.
ta sa ni, ba ita kaɗai ba, koma wane zai iya dafa Alƙur'ani ya rantse wajen ƙaryata duk wanda zai zo da shaidar maganar makamancin abinda Amaryar ta aikata, amma wai sai gashi ita da kanta tayi silar ajalin Matar da ta ɗauketa ƴar'uwa, kuma ta jefa mutumin da akaf ƴaƴan gidan babu wanda ya kaishi bata girma, taɓa mata Gwaggo da tayi shi ne babban zunubin da ta aikata, kuma a yanzu taɓa mata Ya Kabir ya zama mafi munin kuskuren abubuwan da ta aikata a rayuwarta, za kuma tayi danasanin da zai zame ma ta mara amfani.
dan a yau tambarin laifinta ya kafu a zuciyarta ta hanyar da ba zai taɓa goguwa ba, tunda har ta haddasa faruwar wannan tashin hankalin, ta zama silar da Ya Kabir ɗina ke kwance a gadon asibiti cikin wannan mawuyacin halin, ta zama sanadiyar fitar wannan jinin da ke ɗaga hankalina tun ina yarinya, ko ƙaƙa jini ya fita a jikinsa ina kasa samun natsuwa balle irin wannan jinin da ya zubar me bala'in yawa.
sai kawai na rufe idona tare da kifa kaina a gefen gadon nasa, ta daidai hannunsa da drip ke shiga, na kasa ganewa, ni ban san menene wannan dunƙulallan abin ba da ya tsaya min a zuciya na game da Ya Kabir, abu ɗaya kawai na iya ganewa da fahimta shi ne ƙudurin da zuciyarta ta ɗauka akan Amarya, tabbas idan har ni ɗiyar Mami ce, ƴar da nake da gata ta kowanne fanni, to sai nasa Amarya ta wulaƙanta, wannan alƙawarina ne.
Shigowar Aaliya room ɗin yasa Yagana miƙewa da sauri tana tambayar yanda ake ciki game da binciken Amarya da akasa.
sai dai kuma Aaliyan ba jin me take cewa ba balle ta bata amsa, sai Amadu da ya shigo daga baya ne yake mata bayanin komai, har da shaida mata sakin da Malam yay mata, wanda tace hakan shi ne dai-dai.
"wacce iriyar shaƙuwa ce ke tsakaninsu?". "ina Alhassan?". tambayoyi biyun suka fito a tare daga bakuna mabanbanta, suka kalla juna inda Aaliya ta ɗagawa ƴar'uwarta kai,"ki fara bani amsar tawa, wacce iriyar shaƙuwa ce ke a tsakaninsu?". ta faɗa tana ƙara maida idonta kan Mairo da har yanzu bata ɗago daga kifa kanta da tayi ba daga gefen hannun Kabir. "shaƙuwar me ƙarfi ce, kamar shaƙuwar hanta da jini...shi na zaɓa ma ta, kuma shi nayiwa alƙawarinta in har muna raye, ina roƙon Allah da izininsa su kasance a inuwa guda". har yanzu idon Aaliyan na kansu biyun tace,"kenan da mun koma sai bikin aurensu?". Akila ta dubeta da mamaki,"auren Maryam kuma very soon haka?." "ƙwarai, domin a irin critical condition ɗin da yake ciki ya kamata su kasance a tare...ina ce kin ce min Mamansa ta rasu?". "ehh ba ya da Mama a raye, amma ni kuma ai ba haka na tsara auren Maryam ba, so nake sai ta kammala karatunta tukunna". "Kabir ɗin jahili ne?". Aaliyan ta wurga ma ta tambayar san da tayi shiru. Akila na girgiza kai tace,"kaf gidansu ma ai babu me iliminsa". "so me ilimi kamarsa kina tunanin zai hana mace yin karatu?, ko da bata so tayi ba dole zai tursasata, dan haka a irin shauƙin son da nagani a idanun Maryam kasancewarsu a tare shi zai wanzarwa da zuciyarta natsuwa...wanne time suka ce z