NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 155 of 223

mun kama shi yaron da yay causing accident ɗin, bayan an kai shi mara lafiyar asibiti so a time ɗin ya shiga yana laluben aljihunsa time ɗinne wata nurse ta gansa sai tai gaggawar sanar damu. so kamar yanda ita Akila ta bamu waɗancan bayanan akan ita wadda kuke suspecting, mun sami dukkan ƙarin bayani a wayar shi Kabir ɗin, ofcourse kaman yanda Akila ta faɗa akwai record ɗin maganar ita waccan matar mun same shi a wayar Kabir, mun sami bayanin inda ta ke daga bakin shi yaron nata, dan farko munje can gidan shi Malam ɗin bata nan, kuma lokacin da muka je gida sai muka je a daidai gaɓar da ta ke bada labarin abin da ta shuka, duk da cewar ba duka muka tsinta ba amma mun tsinci muhimman abinda zarginmu yake akanta, yanzu haka tana can a cell su na karɓar hukunci ita da yaron nata". Aaliya tayi ajiyar zuciyar da ke shaida tsananin damuwarta kafin tace,"wannan mata anyi sheɗaniya, DPO idan kaji labarin ainihin fuskar da kowa yasanta da ita zaka sha mamaki, za ka rantse kace ƙazafi ne aka ma ta akan wannan abin da ta aikata...yanzu kenan mene ƙarshen hukuncinta?". "ehh to ranki daɗe for now dai zamu yita horasu ne zuwa lokaci zai nuna mana halin da Kabir zai kasance a ciki, yanzu dai nauyin kashe duk wasu kuɗi da za ai akansa ya rataya ne a wuyanta...". Aaliya ta tari numfashinsa da cewar,"ka bar wannan batun matsiyaciya ce ba zata iya ba, ko ka taɓa ganin faƙiri ya tallafi wani?, tukunna ma ba kalla duk akan kuɗi ta aikata hakan ba, so just go stregth to the point ɗin da nake son ji". ya jinjina kai,"right! to abunda dai hukunci zai tanadar akanta shi ne, idan Kabir yaji sauƙi case ɗin mutuwa akanta ya zama guda ɗaya kenan, amma idan Allah baisa ya rayu ba case ɗin mutuwa akanta ya zama biyu kenan, so a wannan lokacin zamu danganata ga kotu domin ta yanke ma ta hukunci akan abubuwan da ta aikata". Aaliyan ta ƙara cewa,"DPO matar nan ta shiga rayuwata da yawa, bima'ana ta shiga rayuwar ƴata tun tana ƙanƙanuwarta, dan haka kamar yanda ta ɗau lokaci tana saka firgici a rayuwar ƴata, haka nake so daga yau ta shiga fara ƙidayar mutuwarta da kanta ta hanyar irin gana ma ta wahalar da za ku dinƙayi, DPO da gaske nake maka daga yau Amarya karta kuma rufe idanuwanta da sunan yin bacci, kuyita galabaitar da ita acikin bugawar kowanne sakan na agogo...idan kayi min haka zan biyaka da kaso mafi tsoka". DPO ya jinjina kai alamar za'ai yanda ta buƙata ɗin. sai yanzu Amadu yay magana a sanda DPO ɗin ya miƙe yana yiwa Aaliya sallama. "DPO nace me yasa ita ma ba za'a ɗanɗana ma ta irin allurar da tayiwa Gwaggo ba kamin zuwan lokacin da ake jira ɗin". "kar ka damu, duk wani nauin wahalar da me laifi a cikin aikinmu yake". daga haka yay musu sallama ya wuce, yayin da Aaliya ta miƙe su na nufar hanyar wani dogon corrido da zai sada su zuwa ga room ɗin da aka kwantar da Kabir, zuciyar Amadu na raya masa cewar ko ya sanar ma ta da zuwan su Major da suke kan hanyarsu, kwatsam kuma sai ga kiran Almustapha ya shigo wayarsa, saboda haka ya ɗan dakata da tafiyarsa ya ɗauki wayar, Almustapha ke shaida masa gasu a compound ɗin asibitin, kuma wucewar daƙiƙa ɗaya sai gasu sun iso inda yake. "Alhassan". Alhassan ɗin ya juyo daga tafiyar da yake lokacin da yaji kiran Amadu, "ka tsaida Mami". Alhassan ya juya ya kira sunanta, juyowarta tayi dai-dai da ɗago da idon Major ya kai kanta da Amadu ke masa nuni da ita, ita ma kuma daga tazarar da ke tsakaninsu ta ganshi, ga mamakin Major sai idonsa ya ƙyallo masa saɓanin tunanin da zuciyarsa tayi a sanda ya kai ƙwaya idonsa cikin nata lokacin da ya iso inda ta ke. a yanzu da ya ƙaraso gabanta tana amsa wayar da Ammi ta kirata ne, dama tun ɗazun ta kirasu ta shaida musu halin komai da ake ciki a yanzu da na baya ma da ya wuce, ta sauke wayar daga kunnenta tayiwa Major kallon sama da ƙasa tamkar bata ma taɓa ganinsa ba, ko kuma wacce ta sanshi amma ta manta inda ta san shi ɗin tana dai ƙoƙarin recalling, kafin a hankali muryarta ta fito da faɗin,"why now?". kan yace wani abu ta juya ga Alhassan tace,"ga Ubanku...". sai dai abin da ta gani ne baisa ta ƙarasa sauran maganarta ba, kamar yanda Alhassan da Almustapha ke kallon junan su da mamakin kamanninsu haka ita ma ta ke kallon Almustaphan da mamakin kamar da ke tsakaninsu. "Major ban lissafa ganinka a yanzu ba, me zuwanka ke nufi?, kuma da wacce tsiyar kazo naji ko kaina zai iya ɗauka?". bai iya cewa komai ba, shi dai yay shiru kawai yana kallonta da wani irin kallo da shi kaɗai yasan me zuciyarsa ke ji a ga me da hakan. gaisuwar da Alhassan yay masa ita ta datse igiyar tunanin da yake, ya juyo gare shi cike da wata iriyar kunya ya amsa masa. sai Aaliyan ta dubi Alhassan ɗin da cewa,"binsa zaka yi ne?". sai yay saurin girgiza kansa,"no Mami, na gaishe shi ne saboda sunan mahaifi da ya amsa a gareni". ranta a haɗe tace,"to kaji, sai ka jira zuwa time ɗin da zan kammala activities ɗin da suka kawoni ƙasar taku, idan na koma ka iya zuwa da ƙafar rashin kunyar naka ka karɓesu". t
🏠