NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 154 of 223

iyastawa a matsayin mallakinsa idan har su ka kuɓuce min lallai wannan Matar zata shigo cikin lissafina tabbas kuwa". Kuma sai muryrta ta katse tare da katsewar numfashinta, da tsayar da idanunta akan mutanen da ke tsaye a bakin ƙofa, mutanen da bata san da zuwansu ba, sai dai dukkan wata alama ta nuna sun ɗauki mintuna sama da goma a wajen, hakan ya bata tabbacin sun shafci jin wasu daga cikin maganganun da tayi ɓarin faɗawa Khadija. bata san lokacin da taja wata doguwar ajiyar zuciya ba kuma ta kasa sauketa, a yayin da lokaci guda maƙogoronta ya bushe, haɗiyar yawu ya gagareta. me zuwan waɗan nan mutanen ke nufi? Me ke shirin faruwa da ita ne? Wa ya shirya girgiza teburun da ta ke lissafi akansa ne dan komai ya tarwatse?. ƙwayar idonta ta sauka a kan Khadija da ita ta ruɗe saboda ganin abinda bata tsammace shi ba a kurkusa haka. "You are under arrest". kalmomi huɗun da suka fito daga bakin police ɗin da ya ƙarasa shigowa cikin parlon kenan, wasu ƴan sanda biyu kuma suka mara masa baya, lokacin da Amarya ta buɗe baki dan yin magana, lokacin kuma ta girgiza da mamakin ganin Malam na shigowa shima. "idan har ba mafarki na ke ba, kuma abin da kunnuwana su ka ɗauki tsawon lokaci a wurin nan su na ji haka suke, to yallaɓai na baku damar ku kamata ku tafi da ita...Aisha daga yau kuma yanzu ina so yatsanki guda ɗaya da kike amfani da shi wajen zanen tsarinki, to a wannan lokacin ina so ya zana miki rabuwata da ke, rabuwa ta har a bada". Malam na faɗar hakan ya dubi Amadu da cewar,"kwaso min waɗancan takardun". daga haka kuma akasa ma ta ankwa aka fita da ita, da rufaffen bakin da ya kasa furta komai. *Bichi* "Inna kin san dai turancin nan ba sosai na ke jinsa ba, dan Allah ki rabu da ni idan su ka gaji da tsayuwa za su tafi ne". Zulai da ke wanke roba ta ƙwalowa Adawiyya robar akanta,"shashar banza ana sonki da arziƙi kina miƙa kanki da talauci, dan ubanki kin san adadin kuɗaɗen da za ki samo mana idan kin fita ɗin?". Adawiyya ta miƙe ta yafa mayafi tana turo baki ta fita, a ƙofar gidan daga gefen dakalin gidan tayi arba da wata dakakkiyar mota fake a wurin, sai Almustaphaa da ke tsaye jingine a jikin motar ya harɗe hannunsa a ƙirjinsa, ɗaya hannun kuma yana kare da waya a kunne kuma yanda ya tattara hankalinsa akan wayar gaba ɗaya zaka san waya ce me muhimmanci yake yi. sai kawai taji wani abu ya zarce ta maƙogoronta da bata san ko menene shi ba, tabbas da ta san da akwai surar halittar da ta fi ta Suhail, wannan tsarin halittar da ke gabanta, Allah ya sani da basu wahalar da kansu akan Suhail ba, abin tambayar shi ne, me yasa ne ita Mairo ke sa'ar samun irin waɗan nan tsadaddun mazanne?, sam ta kasa ganewa ita kam. shin da me Mairon ta fita?, har yanzu fa da ta sauya bata fita dirarran jiki ba, wannan sangalallun siraran ƙafafun nata kamar sillan kara su ne dai suke yawo a cikin zane, to kuwa namiji me rai da lafiya ina shi ina kwasarwa kansa mace me sikila, dan ita a ganinta wannan sirantar ta Mairo ba zata rasa nasaba da sikila ba...amma bari shi ma zata kora shi ne, zata shaida masa yarinyar da za'a laƙaba masa ba komai bace fa ce illigemate child, ai idan ta ɗanɗana masa wannan kalmar ta illigitimacy dole ya haƙura da ita, wai tun yaushe ne ma taiwa kanta alƙawarin Mairo ba zata auri mijin kerewa sa'a ba ne?, to kuma na mene zata damu kanta akan abin da take da yaƙinin tabbatuwarsa, a wannnan lokacin da ya bayyana cewar ita ƴar zina ce wa zai ɗauka?, sai tayi guntun murmushi cikin ranta tana ƙara cewa ai ta koma gefe kawai tai dariya son ranta. "Is Father at home?". tambayarsa da ta shiga cikin kunnenta ita ta katse shirmamman tunanin da ta ke yi, dan haka ta ɗago ta saci kallonsa kafin ta ba shi amsa da cewar,"ba ya nan sun tafi asibiti". kafin Almustapha ɗin ya ƙara cewa wani abu, Dad da ke cikin mota ya fito ya jefo mata tasa tambayar,"what about Ahmad, is he around?". sai ta girgiza kanta alamar a'a. shiru ya ratsa tsakaninsu na ƴan mintuna kamin Almustapha ya jefa ma ta tambayar,"wane ba shi da lafiya?". "Maman Mairo ce". sai ya waro ido waje da mamaki,"Maman Mairo kuma?, ita bata mutu ba dama?". anzo wurin da ta ke so, dan haka ta gyara tsayuwarta ta shiga koro masa bayanan da ke buga mata sarewar daɗi a ranta, kuma bata kai ga furta cewar,"amma ba'a san wane Babanta ba". Dad yay saurin cewa da Almustapha ya kira Ahmad yaji su na ina, hankalin Dad a matuƙar tashe ya shiga mota suka bar wajen bayan Amadu ya shaida musu asibitin da suke, a gefe guda kuma sai kiran wayarsa ake akan bikin mutuwarsu Granny da tuni aka kai gawar ta su can chapel ɗin ana jiransa shi da Emanuel. *Apex Consultant Hospital, Kano.* a cikin harabar asibitin, Aaliya na zaune kan plastic farar kujera, yayin da Amadu da Alhassan ke tsaye daga gefen damanta, a gabanta kuma ƴan sanda ne guda biyu sai guda ɗaya da uniform ɗinsa ya banbanta da na sauran yana zaune shi ma a plastic kujera yana fuskantarta, yayin da ta ke sauraren duk bayanin da ke fita daga bakinsa. "
🏠