NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 153 of 223

yasa da sirrin ɓoye ya fito fili na ɗora alƙalamin zargina akansa, zuciyata bani ta ke shi yaywa Uwarta cikin nan dan ruwa ba ya tsami banza". Khadija da ke dubanta da tsantsar mamaki tace,"kina nufin Yaya Mairo ma kinsa hannu a cikin rayuwarta?". "ƙwarai kuwa, aini da ita na fara kishi kamin matan gidan...nayi amfani da kissata ne wajen karɓarta a matsayin ƴa ta yanda zan kauda ita cikin sauƙi kuma ba tare da wani abu ya taɓa farina ba, ni na dinga ɗirka ma ta wasu ƙwayoyi da nasa aka min safararsu waɗanda za su illata ƙodarta, kuma sunyi ɗin, amma sai Malam ya sadaukar da ƙodarsa ɗaya gareta, haka kuma ni na ɗauki kwangilar ɗauketa da akai...hmmm cikin hikima na ke gudanar da aikina ta yanda hankali ba zai taɓa gasgata zargi akaina ba, a yanzu idan na dafa ƙur'ani nace ni na zuba ma ta maganin ɓera a tsiren da taci babu wanda zai gasgata ni, illama kallon mahaukaciya da za'a min". sai kuma ta bushe da dariya sannan ta ƙara cewa,"ban taɓa aikin asiri ba sai a san da nasa aka tura ma ta maciji, kuma nayi danasanin wannan lokacin saboda ban sami biyan buƙatar haukacewarta ba kamar yanda na tsara, Mtsssww Yasira ce ta bani wannan banzar shawara, dama tun farko na faɗa ma ta ni ban yarda da wani aikin asiri ba, shi yasa na barta akan komai, dalilin haukar Yasira da kike ganin shi ne wannan silar...Khadija ada Mairo da Uwarta ne kawai a cikin lissafina amma daga baya sai Yasira ta nusar da ni zuwa hanyar da ni ban taɓa ganowa kaina ita ba saboda kishin waɗancan abubuwan da suka rufe min ido, Gado! tsawon shekarun da na ɗauka babu haihuwa a gidan Malam banza a wofi zan tashi in ya mutu, ban mallaki komai daga gare shi ba balle na sami gadon wani abu me tsoka, na ɗauki tsawon shekaru ina rayuwa tare da shi amma ban shuka bishiyar da rassanta za su min amfani ba a san da baya raye?...dalilin shigar lissafi na uku kenan cikin tsarina, da Mairo da Suwaiba ne kawai, amma sai tunanina ya lissafa min cewar ya kamata sauran ƴaƴansa ma su shigo cikin lissafin, ta inda na ɗauki aniyar kaudasu 1 by 1, kinga duk sanda akace ba shi da ɗa ko guda kasona zai zama dai-dai da na Zulai, kamar hakanne yasa zan fara ta kan Amadu sai kuma aka sami akasi a jiyan...amma shi Kabir da kike gani sam ban sanya shi a cikin lissafin waɗanda zan rabasu da duniyar nan ba, saboda ina sonsa". sai da ta dubi Khadija da ta zuba ma ta ido sannan ta murmusa kamin tace,"So dai da kika sa ni, ina masa so sosai irin soyayyar da ko ubansa bai sami gurbi a zuciyata ba kamar yanda shi ya samu yay bake-bake a cikinta, tabbas ina so mu kasance tare da Kabir irin kusancin mata da miji, amma da na lura cewar ba zan sami biyan buƙatata a tare da shi ba, sai zuciyar ta karkata akalarta akan dukiyarsa, kuɗinsa kawai na ke buƙata a yanzu shi yasa zan kauda shi amma ba don son raina ba saboda wannan soyayyar tasa na raina har abada, sai dai nasan shi ba zai min amfanin da kuɗi za su min ba a rayuwa". tayi shiru ta miƙa hannu a gefenta ta ɗauko wasu takardu tana murmusawa,"kinga waɗan nan takardun da kika kalla ina kaffa kaffa da su kamar ran mahaifiyata, ba komai bane fa ce takardun gonakin Malam...ni ce na shirya faruwa komai da tsaruwar yanda abin zai kasance ace Gwamnati ce ta ƙwace masa su...wannan ita ce babbar Kadarar Malam kuma da ace nayi haƙuri da Gonakin nan kaɗai da na mallaka ta ƙarfi ƴaƴansa ma ba su isa su gaji kwatan abin da na samu ba...Ya kika kalla kwanyar tawa?". Khadijan ta jinjina kanta, bayan ta sauke numfashi tace,"kin wuce tunani da kuma dukkan hasashe...amma kuma Yaya acikin maganganunki kin faɗi da ace da yawa, kinga kenan cikin tsarin naki ma ba a ko da yaushe nasara ke tare da ke ba". sai Amarya ta kama karan hancinta ta murza, buɗar bakinta za tayi magana wayar da ke kusa da ita tayi ƙara, dan haka tayi saurin ɗagawa ganin sunan Musbahu akai tare da karawa a kunne. "Ya akai?". daga can ɓangaren yace da ita,"an sami mishkila". tai saurin rumtse idanuwanta,"kar ka ce min har zuwa wannan lokacin Kabir bai mutu ba kuma baka sami abubuwan da muke buƙata daga jikinsa ba?". "ehh Hajajju duka babu ɗaya da ya faru, ai na taƙaice miki ma gaba ɗaya jikin Kabiru babu wallet a tare da shi, duk na caje shi wallahi babu kuma har wurin da accident ɗin ya faru babu irin duban da banyi ba amma babu...". "Dakata Musbahu, zan samo mafita akan wannan wuyarta na zurfafa tunanina...mene abu na gaba?". "Amadu ya kuɓucewa shirinmu". "fahimtar da ni". "Ranki ya daɗe Amadu tare da motar jami'an tsaro suka zo, shi kansa Kabirun an sauya masa asibiti zuwa wani babban asibiti...Hajajju tare suke da wata Mata me babban matsayi dan ba ki kalla yanda jami'an tsaro ke nan da ita ba, ance ƴar sarkin Qatar ce tazo nan ƙasar ziyara...Hajjaju babbar matsalar ita ce...". ɗif ta katse wayar kafin ya kai ga faɗa ma ta abun da ba ta shiryawa jinsa ba, a hankali ta furta kalmar,"zanga bayanta, tabbas zan ga bayanta idan har ban sami biyan buƙatata ba, yacca na gama lissafin adadin kuɗaɗen da naji Kabiru na ƙ
🏠