iya cewa tayi kaɗan ta juya min baya a wannan lokacin, kan wannan gaɓar, akan wannan gaɓar da na ke tunanin na kammala dukkan shirina da na lissafa...tukunna ma! me kike nufi da lokaci ya tsaya min?". Khadija tace,"tun lokacin da kika shirya cewar za ki kauda Kabiru da Amadu na faɗa miki hakan kaman ganganci ne, shi yasa a yanzu da aka zo gaɓar da Kabiru ke kwance a asibiti na ke ganin kamar asirinki zai tonu...". ba ta kai ga ƙarasawar ba Amarya ta dakatar da ita,"ke za ki fallasa ni ko?". ta girgiza kanta,"a'a ko ɗaya ba haka bane...idan aka kai Kabiru asibiti a wannan yanayin da yake ciki dole sai hukuma ta shiga cikin lamarin, shi yasa nake tsoron me ka iya zuwa ya dawo".
cikin tsananin ɓacin rai Amarya ta dakatar da ita wajen kiran sunanta a tsawace,"kar ki ƙara min wannan zancen, kar ki ƙara idan ba haka ba kuma ranki idan yayi dubu sai ya ɓaci...ta ya za ai ki dinga kutso min da wata magana mara daɗi cikin sha'anina, ke kin san kuwa tsawon shekarun da na ɗiba ina gudanar da aikina domin cikar burina, babu boka babu Malam da irin dabaruna kawai da suke cikin kaina nake aiwatar da komai nawa da babu wanda ya isa ya gane ina da wata fuskar bayan wacce kowa yasan ni da ita, wannan kyakykyawar innocent fuskar, bari kiji na faɗa miki, ko da lokacin ya yanke, duniyar Amarya ba zata juyawa ba daga yanda ta ƙawatata da tsarata, duniyar nan da kike gani ita ce al...". caraf Khadija ta dakatar da ita daga abin da zata faɗa, wannan kalmar ce da kullum ta ke faɗa mata a matsayinta na wadda tayi imani da Allah da kuma manzonsa bai kamata ta ke faɗar irin wannan kalmar ba, wanda hakan zai sa ta iya fita daga imaninta, cewa da ta ke duniyar nan ita ce aljannarta, saboda ta gina ta da abubuwan da ko da an shafe tarihin kowacce halitta zata ji daɗinta ba zata wahala ba".(auzubillah), ƙwarai matuƙa Khadija na jin takaicin wannan kalmar shi yasa sau tari ta ke kutso da wani zancen a duk san da Amarya tayi yunƙurin furtata.
"Khadija ada ni mutum ce kamar kowa me anfani da zuciyar da ubangijina ya halicceni da ita, amma a yanzu sam ba haka nake ba, tuni na sauya wannan zuciyar zuwa irin wadda nake so ta zama, ta yanda zan cimma burina a gidan Malam, ba dan komai ba sai dan bana so na tashi a tutar babu in Malam yay sallama da wannan duniyar, bima'ana ba zan iya zuba ido naga wasu da ƴaƴansu kaɗai sun wawashe dukiyar da Malam ya tafi ya bari ba, ba zan iya ba!, shekarata ɗai-ɗai har goma sha biyu a gidan Malam amma kullum abin da yake faɗa min game da rashin haihuwata shi ne Amarya ki ƙara haƙura, ubangiji shi ne me yi, yana sa ne da ke, kuma duk wani jinkiri da kika gani a rayuwar mumini wallahi alkhairi ne, dan haka kar muyi azarɓaɓin da zaisa mu iya kauce hanya, saboda kiji daɗi yasa na ba ki Mairo, wannan Mairon da kike jin tamkar ke kika tsuguna kika haifeta". ta rufe ido kafin taci gaba da magana,"ni ba ciwo ba, lafiyata ƙalau amma ace tsawon shekarun nan da nake gidansa banyi shukar da rassanta za suyi irin yaɗon da ba zai sa na jigita ba in bana tare da shi, ehh haihuwa ta Allah ce amma abin yana damuna". tai shiru tana mai jan nunfashi, ta kai hannu ta damƙe glass cup ɗin da ke kan taburin gabanta, wanda tana ƙara sa masa wani ƙarfi zai iya tarwatsewa.
"Malam yay kuskure da ya bayyana soyayyar Suwaiba ɓaro ɓaro ga kowa, da kuma kasa ɓoye irin matsayin da ta ke da shi na daban akanmu a wurinsa, da fifitata da yay ya bata wani linzamin matsayi daban da namu acikin fadar zuciyarsa, da irin yanda ba ya yabon kowacce acikinsu sai ita, komai it ta iya, haƙuri ita ce, hali ita ce, nagarta ita ce, sanin ya kamata ita ce, iya kula da tarbiyar yaro ita ce, idan wani sirrin nasa ne ita ce, yabawarsa da bajintarsa duka nata ne...wannan dalilin shi yasa na kasa danne zafin kishin da na ɗebi shakara da shekaru ina yi akanta, na shiga na fita na kauda ita cikin ƙanƙanen lokaci, buƙatata ta biya, kuma burina ya cika, domin a yanzu dukkan wata daraja tata da matsayi zai dawo kaina".
sai kuma tai wani murmushin nasara da ya tsaya iyakar leɓenta taci gaba da cewa,"ƴarta kuwa Mairo, ko kuma nace ƴar zinar da ta riƙe Mairo na zanata a cikin lissafina ne tun bayan shekaruna biyar da zuwa gidan, dalilin da ya sa naso na kassara rayuwarta tun farko kenan amma sai Malam yay gangancin shigar min cikin al'amarina har aka samu aka ceci ranta". sai tayi wani tsaki da ke bayyana tsantsar takaici kamin tace,"ban san dalilin da ya sa Malam ya fifita yarinyar nan akan duka ƴaƴansa ba, Khadija Malam ya shayar da ni ruwan mamaki da na san gaskiyar cewar Mairo ba ƴarsa bace...Malam ya so yarinyar fiye da yanda alƙalami zai rubuta, ke zan iya ƙaryata duk wanda ya nemi ya kwatanta irin yacca Malam ke sonta, saboda ba abu ne da zai ƙiyastu ba dan ko mizani yay kaɗan ya auna irin soyayyar da yakewa yarinyar nan, shi yasa tun kamin na kamu da kishin Uwar riƙonta na kamu da nata, ni da Mairo na fara kishi a gidan aurena, ƴaƴan Malam sama da goma sha uku amma kyace ita kaɗai ya haifa, shi