NOVEL SHARES -
kidnapping ɗin Maryam, kuma aikin Amarya ne yin wannan allurar gubar wa ƙafar Gwaggo har ta zama silar mutuwarta, sannan akan gaɓar shirinta na yanzu shi ne taga bayan Ahmad da Kabir...kuma Malam idan nace maka gonakinka da aka ƙwace ba gwamnati bace Amarya ce ba lallai ka gasgatani ba duk da cewar waɗannan magangunan nawa ma ba lallai su zama abin yarda a gareku ba, tunda banda wata hujja, amma idan ba ku yarda dani ba nasan za ku iya Yarda da Kabir wanda ya san komai...fatana da adu'ata shi ne Kabir ya rayu ko dan saboda alƙadarin Amarya ya karye, ko dan ya tsaya min wajen kafa muku hujjar da za ku yarda da abin da na faɗa muku...Ahmad kai gaggawar zuwa inda yake da wuri, ai saurin miƙa shi asibitin da zai sami kulawa duk da ba likitocinne da iyawar ba, ubangiji shi zai yi iyawarsa".
abin da zan iya cewa shi ne ba duka naji maganganun nata ba, na san dai ƙafata ta riƙe kamar an kafani ne a wurin, haka kuma ban san lokacin da ƙafata da nake tunanin ba zan kuma iya ɗagata ba sai sanda naga Ya Kabiru a gabana da lafiyarsa, na motsa na kai bakin ƙofa na tsaya daga gefen Ya Amadu, nayi saurin miƙa hannu na riƙo shi saboda juwar da naji tana neman ɗibana, har ga Allah ban san me nake ji ba, ban kuma san meke shirin faruwa da ni ba, idona da basa gani da kyau Ya Kabiru kawai suke son gani sannan su washe, kamar ƴar maye ko kuma wadda ke cikin nauyin bacci na tafi luuu na faɗa jikin Ya Amadu wanda yay saurin daidaita min kaina a saman ƙirjinsa dai-dai lokacin da ya sauke wata doguwar ajiyar zuciya da zan iya cewa daga ita ban sa ke jin komai ba.
*A can ɗaya ɓangaren.*
Amarya ce zaune akan kujerar da ke cikin matsakaicin falon gidan, yayin da wata ma ta ke fuskantarta, yanayinta na nuni da na wanda ya tattara hankalinsa gaba ɗaya ga mutumin da ke masa bayani.
a wannan lokacin babu abin da zaka tsinta a saman fuskar Amarya face zallar ɓacin rai, babu walwala balle yanayinta ya nuna maka tana tare da wani abu wai shi farin ciki.
ta kai hannu ta zame ɗankwalin da ke kanta zuwa baya, sannan ta fuzgar da iska daga bakinta, ta dubi matar da ke gabanta da irin kallon da zai shaida maka girman matsayin da take da shi ga waɗanda suke ƙasanta. wucewar daƙiƙa biyu tana dubanta kamin ta ɗauke idonta daga kanta ta mayar da shi kan wayarta da ke gefenta tana ringing, ta ɗaga wayar ta kara a kunne da cewar,"bana son wani abu wai shi kuskure ya kuma shigowa cikin lamarina, ka faɗa min kawai anyi nasara Musbahu?". ban san me na cikin wayar ya faɗa mata ba sai naji tace da shi,"ka tabbata raunin da ya samu ba zai bar shi ya ƙara shurawa ba?". wucewar wasu sakanni kamin na cikin wayar ya gama bata amsar tambayarta sannan ita kuma tace da shi,"da kyau!, yanzu kayi abin da zaija tsaiko a wajen mutanen da suke ƙoƙarin kaishi asibiti, kuma tunda kace sun kira waya nasan Amadu suka kira, kuma Amadun zai ce zai taho wurinsa, ka kafa ka tsare Musbahu kar Amadu ya ƙarasa wajen nan, domin duka su biyun nake so a rasa a lokaci guda, ta yanda zanyi aikin kwashe duk wata dukiyar da Kabiru ya tara ba tare da hankalin kowa ya kawo kanta ba...sannan a ɗazu da na koma gida na tsinci maganar su Zulai su na batun kamar ita wadda ta zauna a gidan namu ɗiyar wata ƙusan ce, dan sun ga alamun hakan a jikin ƴar'uwarta da tazo, to da zarar ka kawar da Amadu shi ma, ina so ka shiga yi min binciken wacece Kulu, yanzu zan san yanda nayi Malam ya faɗa min a salinta ta yanda aikin zai zo maka da sauƙi....".
*Plss Share&Comment and also vote.*
[7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
_Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._
*(37)*
"an gama ranki ya daɗe, zanyi kamar yanda kika faɗa, ba za'a sami kuskure ba, wannan alƙawari ne nayi miki". Musbahu ɗin ya faɗa daga can inda yake.
"shikenan sai naji daga gareka, komai ake ciki kai saurin sanar da ni". ta sauke wayar daga kunnenta tana me yasar da ita a gefenta. sannan tayi wani murmushi mai ciwo, irin murmushin nan na takaicin rashin cimma wani abu da kai burin samu, sannan ta kwantar da kanta ajikin kujerar. "Amma Yaya kina tunanin za ki cimma nasararki a wannan karan?, sai nake ganin kamar lokaci ya ƙure miki ko kuma ma nace lokacin ya tsaya miki cak, domin anzo gejin da ba zai barki kici gaba da amfani da shi ba". Khadija wadda ta ke ƙanwa ce gareta tayi maganar. Amarya ta ɗau lemun soɓo dake cikin kofi ta kafa a baki, sai da ta kusa shanyewa sannan ta ajiye shi tana mai sauke numfashi.
sannna ta dubi Khadija tana murmushin mai bayyana irin yaƙinin samun nasarar da ta ke da shi akan dukkan wani abu da ta rubuta shi a lissafinta sannan tace,"nasara bata taɓa juya min baya ba, kuma zan