NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 150 of 223

r da ta ke masa, da faɗa masa cewar taso ace shi ma ta rayu tare da shi, amma kuma ta godewa Allah daya sa ya rayu tare da mahaifiyarsa, wanda hakan ishara ce gareta, yanzu ta gane baka taɓa tsarawa kanka komai sai wanda ubangiji ya tsara maka. sannan ta jaye shi daga jikinta tana faɗin,"ina ƴata? ina abar ƙaunata? ina masoyiyata? ina farin cikina?". ta faɗa tana mai dubana, wanda ni kuwa a lokacin na ɓata fuska, ina tura baki gaba kamar zan fashe saboda kishi. ta ƙasan ido naga yanda ta faɗaɗa fuskarta da annashuwa, kamar ta shiga zuciyata taga abin da ke ciki sai naji tace,"ko dan gaba wannan Ummin Maryam ce bata Alhassan ba, ina fatan kai da Babarka za ku shaida hakan...taho gareni Maryam ɗin Umminta". ta faɗa tana me buɗe min hannu, na tafi gareta kai tsaye na faɗa jikinta har sai da ƙirjinta ya amsa, na shiga raira kuka a hankali ina bata haƙurin abin da nayi ma ta. "Ammi da Abi fa?". tayi tambayar ga Mami. tace da ita,"nan da anjima kaɗan zamu isa garesu". sai ta ƙara cewa,"anya zan iya tafiya na bar su Malam?, Aaliya bana jin zan iya ci gaba da rayuwar wani wajen ba tare da waɗan nan bayin Allahn ba". Mamin tace,"nima na sa ni, kuma ko da nazo na sami irin karamcinsu gareki sai lissafin komawa da ke ɗaya ya sauya, ƙafarmu ƙafarsu insha'Allahu, in dai har sun amince". Yagana muka ji tana faɗin,"ni dai ana shiga da hakkina a wurin nan, kusan rabin awa anata magana amma ni Rakiya ban san me ake cewa ba, to Allah yasa dai ba munafurcina ake ba". sai kuma ta dubi Ummi tana faɗin,"ja'ira, ai ki saka ran idan na maida ke gaban iyayenki sai na saka wannan masifaffiyar Kakar taki ta jibgeki". nace,"amma dai Yagana lokacin da bana numfashi ko? dan me taɓa Ummina ko ruwan sama sai nayi niyya, ah toh". sai ta harareni tace,"ke fa ba kya gane mutum na jin haushinki ko?". na ƙyalƙyale da dariya ina cewa,"Hajiya Yagana muyi daɗi muyi tsiya". tace,"inda kike cutata na sakko daga fushin da nake ki haɗa sunana da kalmar Hajiya". sai na ƙarasa gareta na dafa kafaɗarta ina faɗin,"ai kinma gama zama Hajiya da yardar ubangiji, Yagana indai da rai da lafiya kin dinga zuwa hajji da umara kenan har ƙarshen numfashinki, sai dai idan babu familyn Shaik Samin a raye". ta shafa kumatuna tace,"Allah ya amince...yanzu faɗa min abin da wannan baturiyar ta ɗau lokaci tana faɗa muku". nace da ita,"ki tambayi Ya Amadu". ta buɗe ba ki zata masa magana shi kuma ya ɗaga wayarsa da tayi ƙara, kalmar da ya ambata bayan amsa sallamar da yay ita taja hankalinmu gareshi kowa ya tsare shi da ido, ƙirjin kowa na amsawa. "innaillahi wa'inna ilaihi raji'un, aina ne?". bamu san me akace masa ba ta cikin wayar sai ji mu kai yace,"dan Allah Malam ka taimaka ku miƙa shi asibiti mafi kusa, yanzu yanzun nan zamu ƙaraso da izinin Allah, dan Allah ku taimaka kuyi duk abinda ya dace gani nan ƙarasowa". lokacin da ya sauke wayar daga kunnensa kowa ya haushi da tambayar meke faruwa?, yana nufar hanyar fita yace,"Kabiru ne yay hatsari, kuma hatsarin me muni dan yanzu haka ma anata ƙoƙarin ciro shi daga cikin mota ne abin ya faskara". ban san sanda nayi mutuwar tsaye ba, take kuma naji wani dunƙulallan abu game da Ya Kabiru ya nemi waje ya tsaya a zuciyata, kamin furucin Ya Amadu ya shiga haska min hoton faruwar abin a idanuna, hoton Ya Kabiru a cikin jini, a cikin mummunan hatsarin da aka ambata, Ya Kabiruna dai!, sai kawai nayi saurin gimtse idona ina girgiza kaina dan kawar da wannan hoton da ke haska min. daga can kuma sai naji Mami na faɗin,"tabbas wannan hatsarin shirya shi akayi, ba hatsari ne na haka kawai da ya same shi ba, wani ne a gefe ya shirya masa shi saboda yana so yaga bayansa". Ya Amadu da nake gani dishi-dishi naga ya dakata da fita ya juyo yana kallon Ummi. kuma Baba sai yace da ita,"Akila me kike cewa ne?". Yagana tace,"ina ga fa ciwon kamar har da surutai ya sata ko?". tayi maganar tana me gyara ɗaurin zaninta tare da cewa Amadu,"kai shige mu tafi ka bar batun wannan, Kabirun yana ina aka ce maka?". Ummi ta buɗi baki taci gaba da cewa,"Malam akwai ɓoyayyen sirrin da ya jima yana faruwa a gidanka wanda babu wanda ya san da shi sai ni, ni ɗinma daga baya na sa ni, wannan SARAN ƁOYEN da aka jima anayi a cikin wannan gida tun daga lokacin da Maryam ta kamu da ciwon ƙoda har zuwa kan wannan gaɓar ta hatsarin da ya sami Kabir, hatsarin da ba shi aka shiryawa ba Amadu aka shiryawa shi sai kuma shirin ya faɗa akansa...sai dai zan iya cewa ba kuskuren aikin aka samu ba, canja tsarin akai". tayi shiru da wani guntun murmushi a saman leɓenta na baƙin ciki da takaici kafin ta furta,"Amarya! Malam Amarya ce ta shirya wannan hatsarin da manufarta da ban santa ba, amma tabbas aikin Amarya ne, aikin amarya ne ɗirkawa Maryam wannan ƙwayoyin da suka haifar ma ta da matsalar ƙoda, kuma aikin Amarya ne zubawa Maryam abin da ban san menene ba har tayi wannan ciwon cikin, kuma aikin Amarya ne yi mata turen wannan macijin da ya rutsa da ita a banɗaki, Malam da sa hannun Amarya akayi
🏠