NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 15 of 223

u mu da babu abin da muke siyarwa". "ai gobe za'a koma makaranta dan haka idan an bamu kuɗin kashewa sai ku haɗa ku bani". Tare muka haɗa baki ni da Adawiyya muka ce masa, "to shikenan mun ji". Yana munafukar dariya ya ce, "Allah in dai baku bani ba ko ba gobe ba sai na faɗa". Gaba ɗayanmu bamu farga daga rashin hankalin da muka yi ba sai da muka shiga gida, domin kuwa dai langar Gwaggo mun barota acan wurinsu Auwalu, Adawiyya na yafitoni akan mu koma muje mu ɗauko, sai kawai na dake nace mata muje ai ba zata san bamu kai ba. "to idan kuma ta aika a karɓo langar fa Babaa tace bamu kai mata ba, muce me?". Ganin yanda Adawiyya duk ta tsure yasa ni komawa zaure ina aikin ƙyalƙyala dariya har da riƙe ciki, taɓata rai tana cewa,"ke dai wani bin akwai ki da abun haushi wallahi. Da wannan shirmen da kike ma da tuni munje mun dawo, Allah ina jiye mana hukuncin Gwaggo dan kin san da Sunusi zata haɗamu". Na kuma ƙyalƙyalewa da dariya har ina zama akan wani buhun yashi dake ajiye a zaure, tayi tsaki zata bar wajen na riƙo hannunta. "ke dilla can ki tsaya kiji". Ta kuma ƙwace hannunta tana cewa,"ai ke kayan haushinki yawa gare shi, sai lokacin da ake abun hankali ki dinga yiwa mutane dariya bayan kin san kuma bana so". "yi haƙuri Amini, kece yanda ki kai wuƙi-wuƙi kamar kazar da aka tsoma a ruwan zafi kika ban dariya. Allah Adawiyya ki rage tsoro ki zama jaruma, yanzu akan ɓatan langa za ki bi ki tada hankalinki, kuma fa langar nan yanda muka kaita wallahi har a shafe rayuwar Babaa Lami Gwaggo ba zata aika a karɓo ba sai dai idan ita Baaba Lamin ce ta aiko mata da ita. Kinga kuma ba'a kai mata ba balle har tayo aikenta". "to ai ba haka tace mu bar mata ba, cewa tayi ta juye ta bamu". Na tsayar da dariyata ina cewa,"ke dai Allah baki da wayo, sai muce mun kai mata tayi godiya iyaka godiya har tace ba zata iya bada langar haka nan ba adawo da ita saita saka wani abun aciki da za'a kawowa Basma saboda haka ne ma muka daɗe, kuma shiru-shiru yaron da ta aika bai dawo ba sai muka ce mata mu dai mun tafi kar Baba ya dawo". Adawiyya ta rungomoni tana cewa, "kai ƙanwalli shi yasa nake sonki saboda akwai kawo mafita". Yanda muka haɗa kuwa haka akai, dan Gwaggo ta tsaru da tsarin dana yi mata. Bayan sallar magriba muna zazzaune a tsakar gida yaro ya shigo yace ana sallama da Kabir, Gwaggo tace yaje yace baya nan amma idan ya dawo suwa za'ace masa, tunda yaron ya juya bai dawo ba, sai can kusan daƙiƙu biyar da aiken sai ga Saleh ya shigo da gudu, ya nufa hanyar bayi yana bada saƙon wai abokan Ya Kabiru ne suka zo daga birni su na ƙofar gida sunce a miƙa musu ruwan alwala, yana faɗar hakan ya faɗa bayin dama shi kusan kullum haka yake baya shigowa a nutse, ko dai ya dawo da kashi ko kuma fitsari. Gwaggo ta miƙe ta zuba ruwa a butoci guda uku sannan ta dawo ta shiga ɗaki ta ɗauko sabuwar tabarmarta, anata jiran Saleh ya fito ya kai musu shiru bai fito ba, gashi duk mazan gidan basa nan sai shi ɗaya da ya shigo yanzu. Inna Amarya tace, "Ni dai Saleh na rasa wane irin ciki ke gareka, idan ka shiga bayan gida sai kace mace mai naƙuda... Kinga Mairo sanyo mayafinki ki kai musu an barsu sunata jira ba daɗi, ga lokacin sallah ma har ya wuce...ke kuma Adawiyya ɗauki tabarmar ki shimfiɗa musu daga zaure, sai kuce musu Kabiru bai dawowa ba amma dai yana kan hanya dan lokacin dawowarsa yayi, ko kuma su kirashi a waya saboda wataran yana tsayawa ɗaukan karatun dare a masallacin Liman". Gwaggo tace,"to ba'a sanma ko su nawa bane a kai musu buta biyu, ko da ike idan kinje sai ki tambayesu idan da buƙatar ƙari sai a kai musu". Na ɗebi butoci nayi waje Adawiyya na biye dani, a ƙofar dakalin gidanmu na tarar da mutum zaune ya bani baya, na nutsu sosai sannan na ƙarasa ta gabansa, na tsuguna ina ajiye butocin tare da gaishe shi. Suhail wanda yake jin kamar ya san muryar yay saurin ɗagowa yana duban fuskarta, babu shakka ita ɗin da yayi tsammanin gani ce dan bai manta da muryarta da har yanzu kalaman tsiwarta ke zaune cikin kunnensa. Laɓɓan bakinta masu cike da tsiwa ya ƙurawa ido kamar yanda ya ƙura mata ido a ɗazu ba tare da saninta ba, lokacin da take tsaye gaban abokinsa tana ramawa ƴar'uwarta abunda yayi mata, shi kuma a sannan yana zaune daga cikin motar duk yana jinsu, ta kuma burgeshi matuƙa, har yaji ta cancaci da ai mata kyauta, domin hakan ya nuna masa tasan mutuncin mahaifinta dama na ƴan'uwanta, ba kuma zata bari wani yaci mutuncinsu ko kuma ya wulaƙantasu ba dan kawai su na talakawa kuma mutanen ƙauye. To amma wace ita da ya ganta a gidansu Kabir? Bata yi kama da kabir ba ko kaɗan balle ya bata matsayin ƙanwarsa, dan kamannin Kabir na cikakken Bahaushe ne, ita kuma kamanninta sunfi kama dana shuwa arab, ta iya yiwuwa kuma uba suka haɗa, ita tayi kama da mahaifiyarta ne, ya ɗauke ido daga ɗan tsukeken bakinta da yake kallo ya mayar ga fuskarta, yana kallon yalwataccen gashin da ya shimfiɗe a saman goshinta kamar na jarirai, duk da ɗankwalin dake ɗaure ruf akanta hakan
🏠