NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 149 of 223

a halin ƙaƙa na ka iya, wanda Allah kaɗai ne yasan halin da ta ke ciki, kuma duk tsawon wannan shekarun bata taɓa waiwayenta ba daidai da rana ɗaya don ta duba halin da ta ke ciki...lallai duniyarta dabance da ta kowa. nasa hannu na share ƙwallar da ta taru a idona, na bita da ido ina kallonta, sai na tsinci kaina a wani irin yanayin da ba zan iya fassara shi ba, yanayin da nake jin wani abu na ratsani tun daga tsakiyar kaina har tafin ƙafata, kafin wata iriyar ƙauna ta uwa ta keta zuciyata da ilahirin jikina, irin ƙaunar da ubangiji ne kaɗai yasan yawan adadinta, lallai uwa uwace, kuma a koma ya uwa ta ke ɗan da ta haifa yana ƙaunarta, haka ita ma a kowanne irin yanayi ɗanta ya kasance ita ma tana ƙaunarsa, ƙwarai kuwa haka ne, domin ga shi akaina, domin ƙaunar da nakewa Gwaggona da Ummi ta banbanta da tata, ban taɓa jin irin wannan ƙaunar me wani sirrin tasiri na daban ba sai akanta, ƙaunar da nasan tata ce, tata ita kaɗai. sai naji a gaba ɗaya duniyata babu wani abu da ya rage min wanda ko da daga shi ne ace na faɗi na mutu burina ya gama cika, shi ne na faɗa jikinta, na rungumeta, na sanya kaina a kan ƙirjinta, naji ɗumin jikinta, wannan ɗumin jikin na uwa, wanda ban samu ba, wanda na rasa shi a iyakar tsayin shekaruna. wani irin shiru ya ratsa cikin ɗakin asibitin, irin shirun da zuciya ke saƙa abubuwa acikinta, Alhassan dai na zaune kawai akan kujera, wanda ya kafe Mami da ido yana kallonta da mamakin da nake ganinsa ƙarara a saman fuskarsa. ni kuwa hannuna toshe yake da bakina saboda kukan da ke neman kuɓuce min tun ɗazu, sai dai naƙi ba shi dama, domin a yanzu gani nake kamar lokacin zubar da wani abu wai shi hawaye ya ƙare min, tunda har gani ga mahaifiyar da ta haifeni, cike da tarin so da ƙaunata da nake gani ƙarara acikin idanuwanta, dama cikin zuciyarta wanda fuskarta ke nuna hakan. tun ɗazu kanta na sunkuye tana aikin share hawaye, na lura da alamu bata so mu gani dan tana gogewa ne ta yanda ba zamu gani ba, kuma sai yanzu ne ta ɗago ta dubeni, ta saki hannun Ummi sannan ta buɗe min duka hannayenta alamun na in taho gareta, ba shiri kuwa jikina na sassarfa na ƙarasa gareta nayi mata wata iriyar runguma, rungumar da sai dana saka ƙashin bayanta amsawa, ita ma kuma ƙanƙameni tayi kamar mai shirin sakani a zuciyarta saboda ƙauna. "kiyi haƙuri Maryam, ki yafe min kinji...". sai nayi saurin ɗago da kaina ban bari ta ƙarasa ba nasa hannu na rufe ma ta baki ina faɗin,"ni babu abin da kika min Mami, Uwa bata laifi ga ɗanta, idan ma tanayi ni dai na yafe miki har abada, nima ki yafe min...abin da kawai nake so naji daga gareki shi ne ki furta min so, wannan soyayyar da kike ikirarin bani da ita a wajenki...". sai tayi saurin rufe min baki nima,"Maryam inji wane yace miki bana sonki?, aina kika taɓa jin uwa na ƙin ɗanta?, ko wancan lokacinma ai wauwta ce akaina, amma wallahi tallahi ina matuƙar sonki, daga ke har ɗan'uwanki...ko kin san da cewar na dawo ƙasar nan neman Akila amma na rasata, sai da na kusan shafe shekara a ƙasar nan amma ban sameta ba ko da labarinta, nasha zuwa ƙasar nan ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba duk akan yawon nemanku, sai daga baya naga ashe ɗacin raine yasa naƙi amsarku, amma kewarku Maryam har kusan illata lafiyata tayi...". ni dai kallonta kawai nake gaba ɗaya na kasa kwantanta irin emotions ɗin da nake ji a tare da ni, abu ɗaya kawai na sani, da akwai damar da zan tsaga ƙirjina, na kuma buɗe zuciyata, to tabbas zan ɓoye Mamina acikinta, ko dan saboda wannan nadamar da kuma danasani da suke saman fuskarta su gushe. "Dama nasan za ki zo". Muryar Ummi da ta farka ayanzu ta furta hakan a hankali. wani farin ciki ya lulluɓe Mami sai ta sakeni ta koma gefen gadon ta rungume ƴar'uwarta. "Akila dan Allah ki yafe min...ni ban ma san me zance miki ba, bakina yayi kaɗan ya furta duk wasu kalamai a akanki". Ummi na goge ma ta hawaye tace,"ba ki min komai ba Aaliya, idan ma kin min na yafe miki tuni...ina Alhassan?". Mami ta saketa tana mata nuni da shi, wanda ya taso a yanzu shi ma fuskarsa cike da murmushi, ya tsaya a gabanta yana mai rissinar da kansa tare da cewa,"barkanki dai Gimbiya, Barkanki dai Ƴar Sarki Jikar Sarki, Barkanki dai jarumar Mace, Barkanki dai Macen da babu irinta a wannan duniyar, Barkanki dai Uwa ta gari, Alhassan na gaisheki, yana miƙo gaisuwa da jinjina a gareki, ubangiji yaja zamaninki, Ubangiji ya ƙara miki lafiya, ya wanzar da farinciki a rayuwarki, yay miki katanga da dukkan wani abin cutarwa da zai riskoki...daga ƙarshe ina ƙara jinjina Ummina, Ummin Alhassan, ɗanki Alhassan na neman albarkarki". ya ƙarasa faɗa yana zube gwiyoyinsa a ƙasa, tare da duƙar da kansa a gabanta da dunƙule hannu ya ɗaga babban yatsansa ɗaya. tana murmushin da ya bayyanar da duka haƙoranta ta miƙo hannu ta dafa kansa, tana saka masa albarkar kaman yanda ya nema, sannan ya miƙe yana mai kai mata sumba a goshinta, itama ta sumbace shi tana me rungume shi da faɗa masa iya adadin tarin soyayya
🏠