NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 148 of 223

jikoki a gefe, balle suci gaba da min kallon ɓacin ran da na haifar musu. amma sai Akila tace,"idan har haka ne to kiyi min alfarma ki taimaka ki bar min su, ina nufin ki mallaka min su mallakawa ta har abada, ta yanda ko da yaran nan sun taso ba zasu san cewar ke kika haifesu ba, ke kika ɗauki cikinsu, kuma ke kika haifesu, amma ji nake tamkar ni nayi naƙudarsu, wallahi Akila ina sonsu, soyayyar da ubangiji kaɗai yasan yawan adadinta, ni ina sonsu kuma zan zauna da su a koma ya suke, tun da kece kika haifesu". nace da ita,"ta ya hakan zata kasance bayan kowa yasan ni ce nayi ciki ba ke ba?". tana rungume da ke a ƙirjinta kina kukan shan nono tace,"zan maye gurbinki Aaliya, zan zama ni ce Aaliya ba Akila ba daga wannan ranar, ki min alƙawarin ba za ki taɓa fallasa wannan sirrin ga kowa ba ko da ace Allah ya qadarta zan dawo cikin alhalina". "ban gane me kike nufi da idan Allah ya qadarta komawarki ba". "Aaliya ba zan iya komawa ƙasar da akai watsi da ke ba a lokacin da qaddara ta afka miki, lokacin da ya kamata ace an ja ki a jiki, ba zan iya komawa inda aka ƙyamaceki ba Aaliya, Abi da Ammi har yanzu su na fushi da ke ban kuma san ranar dainawarsu ba, dan haka ba zan taɓa komawa gabansu ba sai a ranar da na san sun yafe miki sun bar fushi da ke, haka kuma zan nesanta duk wani abu da zai haifar miki da damuwa ko kuma ɓacin rai, bi ma'ana zan nesantaki da yaran nan kamar yanda kike so, domin abin da kike so shi nake so Aaliya, Aaliya in har rabuwarki da yaran nan zai sakaki farin ciki to ni na miki alƙawarin nisantaki da su har zuwa lokacin da za ki nemesu da kanki, domin ke uwa ce, kuma ko ba daɗe ko ba jima sai kin buƙace su wataran" banji wani ɗar acikin zuciyata ba, hasalima farin ciki nayi da hukunci da Akila ta yanke, wanda yake mafita ce a gareni, tunanina ɗaya shi ne ta yanzu iyayenmu zasu gasgata cewar ni ce Akila kamar yanda ta shirya hakan. hakan yasa nace mata,"amma ai kin san akwai shaidar da su Abi ke gane mu da ita ko". "shaida ba matsala bace Aaliya, nasan za ki san abinyi akanta. ni dai kawai ki min alƙawarin daga yau kin tashi daga matsayin Aaliya a idon kowa kin koma Akila harta ga yaran nan...duk da nasan akwai ranar da zata zo kiji kina biɗarsu ". na amsa mata dana amince, na kaɗa kaina nayi tafiyata ba tare da tausayinta ba ko ɗar a raina, ba kuma tare da tunanin wanne hali zata shiga ba, tunda buƙatata ta rabuwa da ku ta gama biya. fitata babu jimawa sai ga Major ya fito da kai Alhassan, wanda ban san ya suka ƙarke da shi ba har ta bari ya fito da kai, kamar yanda bai saurareni ba, haka nima ban bi ta kansa ba...daga nan ban wuce ko'ina ba sai germany, inda nasa aka min aikin a wuyana, aikin gaira babu dalili sai don kawai na samu shaidar amsa sunan Akila, muna yara tayi ciwon maƙogoro da har ta kai ga sai da aka ma ta aiki, tabon wannan ɗinkin bai goge ba wanda kuma ta shaidar ɗinkinne su Ammi ke iya ganemu. ban koma gida ba sai da na shekara guda bayan aikin ya warke tabonsa ya fito raɗau dai-dai da na Akila. na rayu a ƙasar Germany ba tare da kowa ba, kuma kullum ina ganin yanda ake cigiyarmu a kafafen sadarwa, ranar dana koma gida naje musu ne a zuwan waɗanda akai garkuwa da su, mun kuɓuta sai dai a hanyar tahowarmu da muke gudu muka rabe ni da Aaliya, ban san inda ta ke ba da ita da yaranta. bayan shekara biyu kuma sai ga wani ya kawo mana Alhassan lokacin yana shekara uku, yana faɗin wai an tsinci yaronne tun yana jariri to azurfar da aka gani a hannunsa me tambarin wannan masarautar ita ta bada shaidar cewa shi ɗin na nanne. wannan shi ne silar zuwanka garemu Alhassan, sai dai har kwanan gobe ina tantama akan mutumin da ya ce tsintarka akayi, nafi tunanin mahaifinku shi ya kaika, wataƙila dan ya rasa yanda zai yi da kai. to kunji abin da ya faru, tabbas na aikata muku babban laifi Ƴaƴana, ina kuma roƙonku dan Allah ku yafe min". tun da Mami ta fara maganar na ɗora kaina akanta nake kallonta har san da tayi shiru, tana saka handky ta goge hawayenta, har tsawon wannan lokacin hannayenta na cikin na Ummi a damƙe kamar wacca ake shirin a ƙwaceta. gefe ɗaya na zuciyata na jinjinawa Ummina Akila, da ta iya wannan sadaukarwar dan kawai rayuwar ƴar'uwarta ta inganta, ta ƙwammaci ita ta shiga wannan ƙuncin rayuwar, da gatanta da komai amma tsawon shekaru goma sha takwas tana raye a cikin ƙauye, lallai samun zuciya kamar tata abu ne da zan iya kiransa mara yiwuwa. kallonta nake da irin kallon mamakin da za'ace matashiya kamarta ta ajiye ƴaƴa kamarmu, dan idan ba wanda ya sani ba yana kallonmu tare da ita zai kirayemu da ƙannenta ne. tabbas ban da uwa ce, ban da ina son albarka a cikin rayuwata, kuma ina so duniyata da lahirata suyi kyau, da na kirata da irin kalaman ɗacin da ke ƙasan zuciyata, infact ma ni ban san a wanne irin sahu zan sakata ba, amma haƙiƙa ita me son kanta ce, tasan da irin halin da ta tafi ta bar Ummi amma tayi biris da rayuwarta, tana can hankalinta kwance, bata da wata matsala, ta manta da cewar ta bar ƴar'uwarta
🏠