da babu hankali da tausayi ina ke ina haifar ƴaƴa kice a watsar da su, kai kaji wani ɗibarwa kai zunubi...yo ba ma dole aman jini ya maƙure miki maƙogoro ba, ja'irar yarinya kawai me kafiyar jaraba. shegen taurin kanki ai duk shi yajawo miki halin da kike ciki, kuma gwanda da rayuwar ta garaki, kinga kya gane taurin kai abin cutarwa ne".
tayi shiru ta ɗago ta dubeni ta ɗora da cewa,"kema da kika biyo halinta idan kinga dama sai ki sauka tun wuri daga kai...dan ba komai yaja miki zuwa duniya a shegiya ba sai taurin kai...duk da naga jikinki yayi laushi kamar lawashi ban sa ni ba ko ita ƙanwar Uwar taki ta labarta miki komai shi yasa kika rissina...amma ni ai ce nake idan kin tashi dawowa da makamai za ki zo". maganar take min amma ni tuni na bar ganin Yagana da abin da ta ke cewa, tun a san da ta furta kalmar,"ki haifi ƴaƴa kice a watsar!", ba ƙaramin harbawa zuciyata tayi ba, maganar Alhassan ta dawo cikin kaina, kenan suma da tuni yanzu su na a matsayin marayu?, idan ma sun rayu kenan, tun da Jaririn da za'a yasar ai ba lallai ya rayu ba, ita kenan Ummi da bayan laifin zinar ma da ta aikata da sai ta kuma azawa kanta wani laifin?, kamar ta faɗi wani abu sai kuma zuciyarta ta kwaɓeta dan abin da zata faɗa akan mahaifiyartata ba me kyau ba ne.
tasa hannu ta goge hawayen da ke sauka a cikin dasashshiyar muryarta tace,"wai lokacin da ta ke faɗa musu zata zubar damu a time ɗin da ta haifemu shi ne sai kawai ta fara aman jini". "ba ita ta haifeku ba, ni na haifeku". kafin maganar ta kaɗamu ni da Alhassan, ta girgiza Ya Amadu da ke tsaye gefe wanda yay saurin waro ido waje yana faɗin,"what!?".
"Mami kika ce mene?, ke fa kika haifemu? wannan wanne irin batu ne na ɗaure kai?". ta kalli Alhassan ɗin, sannan ta kalleni kana kuma ta kalli Ya Amadu da har lokacin yake mata kallon rashin gasgata maganarta. sai tayi murmushin da ya tsaya iyakar leɓenta kafin tace,"Alhassan kamar yanda ka taso kaji kowa na kirana da Akila ciki kuwa harbda iyayena, to bani bace asalin Akila, ni Aaliya na ke ita kuma wannan ta kwance ita ce Akila, haka kuma ni na haifeku wanda bayan ita da Major da kuma ni ɗin da na haifa Allah kaɗai ne zai shaidi hakan domin shi ne shahidi.
lokacin da na haifeku da ace da wani makami a kusa da zan iya kasheku tabbas a wannan lokacin zanyi amfani da shi wajen ganin na aikata abin da zuciyata ke ingizani akai, na sha baƙar wuya sosai kafin zuwanku duniya, tun daga san da na sami cikinku har zuwa san da aka min aiki aka ciro ku, tun baku zo duniya ba na ke ƙinku, zuwanku duniyar kuma yasa ƙiyayyar taku ta ninku a raina ba don komai ba sai don saboda ban sameku ta hanyar da ta dace ba. a wancan lokacin da na haifeku ni da mahaifinku duk ba ma ƙaunarku, ko da yake zan iya cewa gwara shi akaina, dan ni gaba ɗaya ne bana sonku, shi kuma saboda wani dalili nasa na zubewar mutuncinsa yasa yake jin ba zai iya karɓarku ba balle har ya rayu tare da ku. dalilin da ya sa ya yanke shawarar cewar mu kai ku gidan Marayu idan yaso ko daga baya ne sai mu ɗauko ku, ni kuma nace sam sai dai a zubaku a leda aje a ajiye wanda Allah ya tsaga da rabonsa ya ɗauka, ko kuma ayi floshing naku, muka ɗaukeku da yaƙinin zamu watsar da ku a bola amma sam wannan baiwar Allahn ta hana, tace matsawar muka aikata hakan wallahi sai tayi shari'a damu, shekararmu goma sha bakwai a duniya kuma tun muna yara bamu taɓa samun saɓani da ita ba sai a wannan ranar, wannan rana da kuka zo duniya, wannan rana da ake neman yanda za ai daku. faɗa mukai sosai da ita har Major ya kasa rabamu, nayi mamakin da duk haƙurin Akila sai da na tuƙeta a wannan ranar, dukkanmu muna da baiwar ƙofi amma ita duk zaluncin da mutum zai mata ba zata taɓa yi masa ba, amma a wannan ranar sai da ta min, sai dai sam ba zata iya cutar da ni ba hakan yasa ta maida abinta. na tsira daga baƙar kunamar da ta turo min ta harbeni sai nima na jefa mata nawa ƙofin macijin, macijin da zai iya illata kuzarinta da lafiyarta, to amma sai nayi katari da abin da ya kaini ƙololuwar mamaki akan jaririyar da na haifa a wannan lokacin, abin da kuma har ya tsorata ni. Allah me hikima, me ikon da babu irinsa, cikin ƙudurarsa Maryam ke kika ceci Akila daga wannan macijin da na san ko magani ba zai yi aiki akansa ba, da idanuwanki a waje tar kika kafe wannan maciji da ido da wani irin sauyin halitta ta ƙwayar idonki da tayi har macijin ya kasa tunkararta balle harya cutar da ita, ƙarshema sai ni naji ajikina san da macijin ya ɓace.
babu irin roƙon da Akila bata min ba akan nayi haƙuri mu tafi da ku gida amma sam naƙi, nace ba zan taɓa bari ku lalata min duniyata ba, domin ina da tarin buruka a rayuwata, burukan da su ke na siyasa da kuma riƙe manyan muƙaman da na nake fatan Allah ya ida min nufina akansu, sai dai matsawar ina tare da ku ƙasarmu ta shaida ta yacca na sameku ba lallai wannan burin nawa ya cika ba.
haka kuma ba zan taɓa bari ku lalata alaƙar da ke tsakanina da iyayena ba, gwara ace babu ku sa iya mancewa da su na da shegun