har fa da Mairo na gani ita ma hannunta kamar da makaman yaƙi, tahowa su ke dadab fuskokinsu duk a fusace..ni Rakiya ko me mu kai musu Allah masani".
Amadu yay guntun tsoki da shi kaɗai yaji kayansa sannan ya wuceta zuwa ciki, tabi bayansa da ido tana faɗin,"au ina faɗa maka ruhinta yazo a fusace kana ƙara zuwa inda ta ke...kai wannan ɗa kai da Mairo ban san waya fi wani rashin jin maganar na gaba ba...Amadu gawa ce fa kake tsaye a gabanta, ni dai ina faɗa maka kazo ka karɓo mana takarda wucewa gida". yay mata shiru yana buɗe ledar magungun nan ya fito da su. Malam yace da ita,"Yagana ƙila kin saka wani abu a ranki ne shi yasa, amma Akila da ranta dan yanzun nan fa bacci ya ɗauketa ko minti uku ba'ai ba...". ta katse shi da faɗin,"Adamu kana ina?". ta faɗa tana zura fuskar hijabinta. Malam yace,"gani Yagana". "to ban hanya na wuce, dan ni kaɗai nasan abin da na gani". rufe bakinta kenan a san da ta ke ƙarasowa bakin ƙofa sai gamu mun ƙaraso wurin, kan ƙiftawar ido Yagana ta ture Malam ta koma ciki tana shimfiɗa hailala tana neman mafaka. Ba Malam kaɗai ba, harta Amadu sai da allon ƙirjinsa ya girgiza da ganin Aaliya, abin mamaki da al'ajabin da zasu iya kira ba su taɓa gani ba shi ne mutane masu kama da juna sak irin haka. da ace Akila bata basu labarinta ba, da su kansu a yanzu da suka ga ƴar biyunta zasu iya tsorata su kirata da fatalwa. to amma sanin cewar sun san komai dan haka sai basu ji wani ɗar ba, ba su yi mamakin ganin nata ba kasancewarta tare da Mairo, dama tun a daren jiyan Adawiyya ta kira waya ta ke shaida musu wai Mairo tace ta shiga yawon duniya, Kabiru ya koma gidan ko Allah zaisa ya gamu da ita a hanya sai dai haka ya ƙaraci bincikensa har a tasha bai sameta ba, kuma da suka koma gida yaje gidan Yagana ɗauko wallet ɗinsa ya tarar babu ita babu kayan Mairo ya tabbatar da cewar zai yi wuya idan ba Qatar ta nufa ba, kuma a safiyar yau ɗin ya wuce airpot dan tabbatar da zuwan nata.
Malam ne ya amsa sallamar Aaliya tare da yi musu maraba da zuwa, sai dai sam ita ba fuskantar me yake cewa takeyi ba tun bayan sallamar da ya amsa musu. kanta kawai ta ɗaga musu tana sauke idanuwanta akan Akila da ke kwance tana bacci, yayin da gefe guda na zuciyarta ke mata wani susa da ita ɗaya ta san irin abin da susar ke haifar mata.
"Mairo kin kyauta". abin da Malam yace kenan da ni yana duban fuskata, sai na ɗago da kaina daga barin kallon yatsun hannuna da nake na dube shi na sakan ɗaya sannan ta faɗa jikinsa. "dan Allah Baba kayi haƙuri ka yafe min, nayi kuskure kuma na tuba, ina neman afuwarku". sai kawai ya ɗora hannunsa akaina ya shafa tare da faɗin,"babu komai Maryam, ƙuruciya ce taja kika aikata hakan, amma sai dai ina so na tunasar da ke wani abu, ubanjiji ba ya ramuwar gayya kuma ba ya son masu yinta, don haka ko dan gaba ki dinƙa tunawa da wannan...Allah ya sanyaya miki zuciyarki ya kuma baki haƙuri da juriya...kuma Allah yay miki albarka da ayanzu kika zama silar dawowar mahaifiyarki duniyarta ta asali". maganar da Yagana keyi ta karkata hankalinsu gareta.
"yo aini gaba ɗaya na mance da wannan balarabiyar ta shaida mana ita biyu ce, kai jama'a Allah da iko yake, yo ku me iya ganinku ai sai me dakakkiyar zuciya...ka duba dan Allah wata sarauta ta ubangiji...Mairo to ita wannan ɗin aina kika tsintota?, kar dai kice min ɗaukar fansar ta ki ne ya kai ki can Ƙasarun". "kai Yagana mene wani kuma ƙasaru, Qatar ake cewa". Amadu ya faɗa yana miƙawa Alhassan kujerar zama. a cikin larabci Baba da Amadu suka gaisa da Aaliya kasancewar su na jin kaɗan-kaɗan, Yagana ce dai ta ke ta zabga mita akan tana ta kula Aaliyan tayi mata banza tana yi mata kallon hadarin kaji daga ita har shi zololon ɗan nata. sai da Mairo tace mata,"Yagana dukansu fa basa jin hausa, Larabci da turanci suke ji idan kuma kin iya to bismillah". ta riƙe haɓa da faɗin,"ashe abin babba ni Rakiya ƴar gidan larabci da turamci, da dai alu ambaki ne sai na biya...kuma kema tun farko ai sai ki min bayani ba sai ta kai ga na fara jin haushinsu ba, ko da yake kema Mairo yanzu ai kinfi ƙarfina ni Rakiya Mannir". murmushi kawai nayi, na shiga yiwa Aaliya bayanin cewar Yagana na gaisheta, kai kawai ta ɗaga kamin na ƙara cewa wani abu ta tari numfashina wajen faɗin,"ki tambayesu mene silar ciwon nata?". maganar tata ta fito very cool, kuma har sannan idonta na kan fuskar Ummi da tayi looking very innocent, duk ta rame tayi duhu, idonta kuma bai bar saukar da ƙwallar tausayi ba a hankali.
"to mu dai tana cikin bamu labarin rayuwarta ne sai kuma ta shiga wannan halin". Malam kewa Mairo bayanin, ita ma sai ta juyar da shi ga Aaliyan.
"me tace musu a labarin nata?". Mairo ta kuma faɗawa Malam ɗin, kafin yace wani abu Yagana tayi caraf tace,"ke labarin wannan ja'irar uwar taki da kayan haushi yake, ki faɗa mata ta haƙura daji dan Allah tun da dai tasan komai, ni labarin ɓatan rai yake...ƴar ƙaniya kana kallonta fuska a bar tausayi ashe nan iya shege ne fal a cikinta, banda ma dai yarinya