ɓanki da kuma cikin zuciyarki".
wucewar daƙiƙa 1,2,3,4,5 sai naji wani sanyi na daban yana ratsa zuciyata, kuma sai naji Al-Hassan yaci gaba da cewa,"to ki faɗa min shin za ki so ace mahaifiyarki ta wulaƙanta a duniya?, shin za ki so yau ace mahaifiyarki ta tozarta?, to idan ma kinyi hakan ke mene makomarki? kuma mene ribarki?...haba Hussaina, yanayinki bai yi kama dana yarinyar da bata da ilimi ba, ko kuma bata sami tarbiya ba, idan ace tunaninki ya gushe, to ina iliminki fa?, ki tattaro hankalinki wuri ɗaya ya dawo miki da iliminki, wannan ilimin naki ya tuna miki cikin rukunan musulunci akwai yarda da ƙaddara me kyau ko mara kyau tare kuma da fawwwalawa Allah komai. sannan ilimin naki ya tuna miki faɗar Allah SWT da yake cewa, "kuyi haƙuri, haƙiƙa ubangiji yana tare da masu haƙuri, kuma yace ku zama masu afuwa ga wanda ya saɓa muku, haƙiƙa ubangiji me afuwa ne". Fansa! Fansa dai! Hussaina idan har za ki tuna wannan faɗin na ubangiji to ki faɗa min mene amfanin ɗaukar fansa?, kuma ma abu mafi muni da tashin tashin hankali ɗaukar fansar akan uwa, wadda sai ta ɗaga miki digadiganta ne tukunna za ki samu wucewa zuwa aljannah. Macen da ita ce ma'aiki ya faɗeta har sau uku kamin ya ambaci uba, Uwa Hussaina, Uwa ba'a bar wasa ba, ki shiga hankalinki, ki kuma shiga nutsuwarki, domin ɓacin ranta shi zai kai ki wuta, hawayenta kuma ya turaki jahannah. shin ni kin san tsawon shekara nawa na ɗauko ina roƙon Allah ya haɗani da ita, na jingina a kafaɗunta, na goge mata dukkan wani datti na damuwa da ke cikin ranta, na maye ma ta gurbinsa da farin ciki, ba don komai ba sai dan kwaɗayin wannan ɗumbin ladan na kyautatawa iyaye. to wallahi Hussaina indai ba so kike ki ɓata lahirarki ba? tun wuri ki tuba, yo zunubin ki kai shi har ina?, kiyi ƙoƙari ki gyara lahirarki tun wuri, kuma tun lokaci bai ƙure miki ba, mutuwa na nan zuwa, ko ta ɗauke ki ko ta ɗauke Mahaifiyarki...Hussaina dukanmu masu laifi ne in one way or the other, kuma a kullum burinmu da fatanmu shi ne a yafe mana, kiyi tunani, ki ƙara tuna wannan girma da darajar na iyaye kamin ki zartar da hukunci".
tun da ya soma maganar naji numfashina yana yin sama sama da har ta kai ga na gagara wajen in fesar da shi, ƙwaƙwalwata kuma naji tana bugawa da wani irin duka dum dum, kaina ya cushe gaba ɗaya.
"kice astagfirullah, kiyi istigfari ko kya sami sauƙi a zuciyarki, dan wallahi wannan mummunan ƙudurin kaɗai da kika ɗauka ba zai barki jin daɗi ba". Alhassan yace da ni a sanda ya lura da yanayin da nake ciki, kuma cikin wata iriyar murya da ba zan iya kwatanta yanayinta ba na shiga faɗin,"Astagfirullah, Allah na tuba, Allah na tuba". faɗa nake ina ƙara maimaita, a lokacin babu a inda nake so na ganni illa agaban Ummi nah, babu abin da idanuwana ke son gani sama da Ummi nah, ita kawai, ita kaɗai don inje in nemi yafiyarta.
a hankali na shiga buɗe idanuna ina mai jin zuciyata a matse, na sauke idona akan titin da muke cikin go slow, sai naji Alhassan na saka min earport a kunnena, suratul yusuf ce ke tashi cikin ƙira'ar Shuraim, a hankali sai naji ina samun nutsuwa.
"ranki ya daɗe gamu mun shigo garin bichi". security ɗin da aka haɗa Aaliya da shi ya faɗa, yana daga gaban motar a zaune. sai tace da ni,"ke gamu a garinku, sai ina?". na buɗe idanuwana na sauke su a cikin garin bichi, garin da na fita da niyyar barinsa har a bada, na haɗiye abin da ke dunƙule a maƙogorona sannan nayiwa driver ɗin nuni da hanyar da zai ɗauka. tsayuwar motarmu a ƙofar gida na riga kowa buɗe murfin motar, Mami na fitowa abin da bakinta ya furta shi ne,"anan Akila ta ke rayuwa?". na ɗaga ma ta kai kawai, sannan na wuce zuwa cikin gidan. a tsakar gida na sami Inna Zulai da Adawiyya da Sadiya da Zubaida, kuma dukkansu sai suka miƙe a razane saboda ganina kamar wacca aka jefo.
"Mairo". Inna Zulai ta faɗa, Adawiyya ma da ke dafe da ƙirji tace,"me kika dawo yi? hankalin kowa ya tashi anata cewa kin gudu kema kin shiga duniya". na sharesu na wuce zuwa ciki, dan bata su nake ba, hasalima a yanzu bana son wani abu wai shi ɓacin rai, sai dai ƙofar ɗakin Gwaggona a rufe da kwaɗo, saboda haka na dawo nace da su,"ina Ummina?". da mamakinsu su ke tambayata,"wace kuma haka?". "Babata ta ainihi". Inna Zulai tace,"ohh ai tun jiya da suka wuce asibiti basu dawo ba, ɗazun nan ma Kabiru yazo ya ɗiba kayanta wai an basu kwanciya".
"innalillahi kwanciya kuma, a wane asibiti?". "asibitin bichi, za ki je ne?". kamin na basu amsa sai ga Mami ta doko sallama, kuma kafin wani cikinsu ya amsa Inna Zulai da ke daga bakin ƙofa tace,"ikon Allah ba dai ma su ne suka dawo ba, kinji maganarta ƴar halak". sai nace,"ba ita bace". "amma kuwa maganar zam ita...wa'alaikum salam, shigo". Innar ta faɗa tana dawo daga inda nake tsaye tana leƙan zaure, a tsorace kuma taja da baya tana dafe ƙirji kamar wadda taga mugun abu,"na shiga ni Zulai, Kulu kece haka?".
na ƙara bata amsa da,"ba ita bace Innah, ƴar'uwarta ce". sai ta kalleni tana ƙifta idanu