kalmar ɗaukar fansa akan Aaliya, ba barazana ta ke min ba, zata aikata ɗin kamar yanda ta faɗa. ta kuma gwada na gani, dan sai da ta nuna min, domin ba don zuwan Umm wajen ba a lokacin da ta kwantar da ni ta ɗora wuƙa a wuyana tsab sai ta yanka maƙogorona na zama tarihi". furuncinsa na ƙarshe yasa na saki guntuwar dariya da ban san lokacin da nayi ta ba, da mamaki nace da shi,"yankawa dai!, ita Mamin sai ta yanka ka?, wace kalar mata ce ita ne?". tashi yay daga tsugunen da yake ya zauna kujerar kusa da ni yace,"idan aka tashi rubuta sunan masu faɗawa da cikawa to sunan Mami ne zai zo a farko. haka kuma tana sahun masu zafin zuciya, irin zuciyar da bata son wargi. uwa ce ita me daɗin sha'ani, amma kuma sam bata tolerating wani iskanci daga kowaye ba ma yaro ba".
nayi shiru ina nazarin kalamansa, kamin na jefa masa tambayar, "to dama su biyu ne da gaske?". sai ya juyo ya kalleni,"ba ki sa ni ba dama?". kaina kawai na ɗaga masa ba tare da bakina ya furta komai ba.
"twins ne su kamar yanda muke, ba su da wani banbanci a kamannin halittarsu, sai dai kuma a halayya da ɗabi'u. Mami ita ce ƙarama, wadda ta haifemu kuma ita ce Babba me suna Aaliya". "Aaliya kuma?". ya jijjiga min kai tabbacin amsata. sai na shiga girgiza kai ina faɗin,"ya ake neman a rikita min lissafi ne. wadda na tashi a wurinta fa tace sunanta Akila, ita kuma Mami tace min sunanta Aaliya. kai kuma yanzu kana ce min Mami ce Akila, ya haka kenan?". sai yace,"nima a ɗazu da na fuskanci tana kiran waccan da Akila na shiga cikin duhu, kuma Mami ba me son yawan tambaya bace shi yasa kika kalla nayi shiru, amma har zuwa yanzu kaina a ɗaure yake da sunan da ta kira waccan". sai kawai na zuƙi wani numfashi kamin na furta,"to ni dai kome za'ai ba zan fasa ɗaukar fansar shegantani da akai ba". na faɗi hakan har zuwa lokacin zuciyata bata rissina ba. sautin murmushin takaicinsa na jiyo ta gefen kunnena tare da cewar"a kanwa za ki ɗau fansar?". ina rumtse idona nace da shi,"akan Akila da Major, Al-Hassan idan kai ka yafe wallahi tallahi ni ba zan taɓa yafewa ba, sai na ɗauki fansar rayuwata akansu, sai na saka su kuka fiye da wanda suka sa ni, sai na saka sun wulaƙanta a duniyar nan, wannan alƙawarina ne".
sai yay saurin katse maganar tawa ta hanyar rufe min baki da tafin hannunsa,"shhh, Hussaina waɗannan kalaman fa har ina?, ina kike so ki kai ɗumbin zunubi?. to bari na faɗa miki abin da haƙuri bai bada ba rashinsa ba ya taɓa bayarwa, kuma ai idan hankali ya gushe hankali ake sawa ya nemo shi, nima nayi irin waɗannan kalaman a san da aka faɗamin ni ɗan zina ne, amma da na sami tarin nasihohi da wa'azi daga bakin Kakana Shaik Samin, kuma na zauna nayi nazari da tunani sai naga ɗaga hankalina ma nace sai na ɗauki fansa babu abin da zai haifar min fa ce ƙara dagula rayuwata...Hussaina wallahi Allah yana sonmu da Rahma, idan ba ki san da wannan ba to ki sa ni a yanzu, Allah yay mana ni'imar da bai kamata mu butulce masa ba. kina ina!, kina ina Hussaina ake haifar irinmu a watsar da su, wasu kuma asa su a kwalin indomi a rufe, wasu kuma asasu a masai ayi floshing ɗinsu, wasu ma su na jarirai shagaf a kashesu, kije gidan marayu ki kalla irinmu sunfi a ƙirga, waɗanda ba su san iyayensu ballantana danginsu, wasu kuma su na nan su na gantali a duniya cikin ƙasƙantacciyar rayuwa, bakin duniya na binsu...amma mu da ubangiji ya tashi, sai ya rufa mana asiri, bai sa mun wulaƙanta ba, bai sa mun tozarta ba, bai sa mun ɗanɗani wannan ɗaci da baƙin cikin a zuciyoyinmu ba tun muna ƙanana, sai ya barmu a cikin gatanmu, ya barmu a cikin ni'imarsa, to kuma dan me zamu butulce masa Hussaina?...Hussaina babu macen da zata so ace ta haihu bata hanyar aure ba, haka ma banda ƙaddara babu abin da zai sa mahaifiyarmu ta samar damu ta wannan ƙazamiyar hanyar, na sami tabbacin hakanne ta irin shaidar da mahaifiyarmu ta samu daga wajen mutane, idan har kuwa haka ne akan mene ba zamu yi mata uzuri mu yafe mata ba?, mu tayata goge wannan ruwan hawayen baƙin cikin da ta jima tana yinsa tun bayan zuwanmu duniya...a barshi ma da gangan tayi, amma shin ko kin san wannan lamarin tsakaninta ne da ubangijinta, kuma da zarar ta roƙe shi zai yafe ma ta, to idan har shi zai yafe ma ta dan me mu ba zamu yafe mata ba?, kuma da kike ikirarin sai kin saka sun wulaƙanta, to ki nutsu da kyau, ki sakawa zuciyarka salama na lokaci kaɗan, sai ki dawo da hankalinki gareni". a wannan lokacin sai yay shiru, ni kuma sai na ɗan kalle shi, fatarsa tayi jaa, manyan idonsa irin nawa sun yo waje, alamun dai shi ma tasa zuciyar a cunkushe take da tarin baƙin ciki, dauriya kawai yake yi. na sauke numfashi na bar kallonsa, a hankali na rufe idona, na zuƙi doguwar iska kamar yanda yace, sannan na fesar, sai da nayi hakan har sau uku kamin na shiga biya kalmar, "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, hasbunallahu wani'imal wakil". ashe a fili na faɗa, ba'a zuci ba kamar yanda nayi tsammani, sai naji Alhassan na ce min,"yauwa, kiyi ta maimaita hakan a fili, akan laɓ