ace ta yafe min abin da nayi ma ta tukunna". sai yace,"bana tunanin Ummi zata ƙi yafe miki akan wannan laifin da nasan ɗan ƙarami ne a wurinta, abin da kullum Mami ke faɗa min shi ne; Umminka tana da haƙuri, tana da kirki, kuma ƴar aljannah ce insha'Allahu".
na fesar da wata iska daga bakina, tare da sauke gajeran numfashi, dukkan tunanina ya tafi kan rayuwata ta baya kamin na san komai a yanzu, lokacin da na girma na fara wayo, zuwa lokacin da na mallaki hankalin kaina, bakin Ummina a rufe yake da yin magana, idanuwan nan kullum akaina su ke cike da so, ƙauna da tausayi. ta takure kanta a waje ɗaya, a cikin ƙunci da damuwa, ta hana kanta walwala balle ta sawa kanta jin daɗin rayuwa, a gida ɗaya mu ke rayuwa, tana so ta kasance tare da ni, amma gudun halin da zan shiga idan naji wace ni, ta haƙura ta nisanta kanta da ni, ba don komai ba sai don saboda naji daɗin rayuwa, ta fara tsufa tun da sauran ƙuruciyarta kuma wai duk saboda ni. amma na rasa da me zan saka mata sai da waɗannan kalamai na rashin tarbiya, na rashin ɗa'a, na rashin ya kamata. ko da yake ba laifina ba ne, i was very shock a lokacin da naji cewar ni ƴar zina ce, shi yasa na kasa controlling zuciyata, amma wallahi ba da son raina ba, nayi nayi na lanƙwasa zuciyata amma sam na kasa saboda tafi ƙarfina a lokacin, tabbas na aikata babban kuskure, na aikata abin da nake yin nadamar aikatawa a yanzu, amma ko kaɗan, ko kaɗan na san Ummi bata cancanci abin da nayi mata ba, uwata ce, ko a ya ta sameni ya akamata ace na martaba ta, duk lalacewarta sai na bita zan shiga aljanna, sai na bita zan samu rahmar ubangiji.
to wai ma aina na dinga samo waɗannan ƙazaman kalamai da na dinƙa jifanta da su ne?, ko da yake kamar yanda na faɗa ba laifina ba ne, zuciyata ce, sharrin shaiɗanne, babban tashin hankalina a yanzu bai wuce idan na tuno wannan barazanar da ke shimfiɗe a ƙwayar idon Mami sai naji kamar na haɗiyi zuciya, a yanda na ke bana taɓa tunanin Ummi zata iya yafe min abin da nayi mata, ga Al-Hassan ya tabbatar min da Mami bata barazana, tana faɗar abin da tasan cewar zata aikata shi ne, kuma sai ya tabbata, bata da haƙuri ko kaɗan, mafaɗaciya ce, tana da kafiya, cijiya, taurin kai akan abun da ta ƙudurta. shi yasa a kullum kuma a ko da yaushe alƙawari ya ke biyo bayan furucinta...to ni kuwa Maryam idan haka ne na shiga uku, dan tabbas nafi kowa rashin dacewa a duniyar nan. sai kalaman Al-Hassan su ka shiga haskawa a cikin kaina, a wannan lokacin da muna cikin jirgi, lokacin da Mami ta tashi ta koma seat na daban don gudanar da aikin office ɗinta a cikin system, Al-Hassan ya shiga toilet ya fito, da ya zo wucewa ta gabana ne ya tarar da ni ina zubar hawaye, idanuna a rufe su ke a lokacin saboda haka har ya tsuguna a gabana ban sa ni ba sai da naji yana faɗin.
"a rayuwata hawayen mace yana ɗaga min hankali, ki tambayi Mami nah kiji, yanzu-yanzu hawayen mace zai hargitsani, ya kiɗima ni, ya gigita ni, saboda haka ki taimakeni ki goge su.
shin ma me akai miki a duniyar nan da har kike zubar da hawaye masu gudu irin haka?". ban amsa masa ba illa iyaka buɗe nauyayyun idanuwana da nayi na saukesu a kansa ina binsa da kallo kawai, ina kallonsa da hoton fuskar Al-Mustapha, naga lokacin da wani abu ya wuce ta maƙogwaronsa kafin ya ƙara buɗe baki yace min.
"Mami bata taɓa yi min wata magana da wasa ba, duk abin da ta faɗe shi to haka yake da gaske. shi yasa ko a yanzu da ta faɗa min kece ƙanwata banyi tantama ba na amince da hakan, duk da zuciyata tana cike da mamakin ta yanda akai ta sameki bayan tsawon shekaru goma sha takwas da aka ɗauka, alhalin kuma tun kina jaririya rabonta da ke da mahaifiyarmu, sai dai da nake kallonki yanzu zuciyata ta kore duk wani tunani da kokonto, na ƙara amsar maganarta, duba da kamanninki, kamanninki zam irin nasu ne, siririyar fuska kawai kika fisu".
sai nace da shi,"yanzu kai kenan baka damu da ta hanyar da aka bi aka haifemu ba?, ka ganka fa hankalinka a kwance, ko baka san komai ba ne?". murmushi me ciwo naga yayi da ya tsaya iyakar leɓensa, kafin ya bani amsar,"na san da cewar ba ta hanyar aure aka haifeni ba, na san da wannan tun ban ma san me hakan ke nufi ba har zuwa san da na girma na san ma'anar kalmar zina, na san ta wannan hanyar aka bi aka haifeni, kuma bayan haihuwar tawa mahaifiyata ta gudu ta barni saboda kunyar duniya. kin san a lokacin da Bella ta tareni da wannan maganar me nayi?". da mamaki na zaro ido waje ina tambayarsa,"ai na kasan Bella kuma?".
"Bella Kaka ce a wurinmu. kuma ita ta shaida min waye ni, a wannan ranar da ta faɗa min kwana nayi ina aikata abin da ban taɓa yunƙurin yinsa ba a rayuwata, kwana nayi ina shan abin da Allah ya haramta saboda baƙin ciki, idan da ace giya na yin tsiro da yanzu tayi rassa ajikina. to amma daga baya da Abi yay min nasiha akan karɓar ƙaddara sai naji zuciyata ta washe. duk da cewar sai da Mami tayi min barazanar yankani idan na kuma yunƙurin shan giya ko kuma na kuma furta zan shiga duniya balle na furta