ma abin da saƙon ke ɗauke da shi, "Akila bint Tamim". gajeren saƙo ne, kuma gajeren saƙon da ya girgiza duniyarsa gaba ɗaya, a fili ya maimaita sunan ba tare da ya sa ni ba. kenan mafarkinsa zai tabbata?, idan bai manta ba sau uku kenan yana mafarkin sun ƙara gauraya da su a wata duniyar, ai shi a tunaninsa tun da ya binne wannan hotunan nasu kamar ya rabu da ƙayar tunaninsu ne, amma ya akai haka?, lambar nigera!, kenan tun san da suka rabu da Akila tana ƙasar nan bata koma gida ba kamar yanda ta faɗa musu?. sai ya lumshe ido ya shaƙi wata iska me zafi, ƙarar saƙon da ya kuma shigo masa shi yasa shi buɗe ido zuciyarsa na me wani irin harbi. yay swapping ɗin wayar ya shiga whatsapp account nasa, ya duba lambar farko da saƙon da ya shigo masa, ya kuma buɗe hoton da tun kamin ƙarasa buɗewarsa zuciyarsa ta raya masa hoton ƴarsa ce. kamar yanda ya zata, hoton na gama buɗewa sai ga hoton Akila da Mairo, hoton Mairo shi yafi girgiza shi har ya kusa faɗuwa a ƙasa, sannan saƙon da ya biyo ƙasan hoton a yanzu yasa shi saurin dafe bango.
_"tsawon shekara goma sha takwas kayi biris da mu. naso ace na ɓoye amma hakan sai ya faskara, a yanzu ƴarka ta buƙaci sanin wane ubanta, kuma na faɗa mata, ta kuma ce sai tayi shari'a da kai, dan haka Major ka shiryawa abin da zai biyo baya. Ƴata zata ɗaukar min fansa, zata lalata duniyarka kamar yanda ka lalata mana tamu"._ sai yasa yatsansa ɗaya tun daga kan goshinsa har kan hancinsa, shikenan abin da yake gudu zai faru, komai ya zo ƙarshe, girmansa! mutuncinsa! ƙimarsa!, shikenan za su zube ƙasa wanwar kamar yanda yake ta jimamin faruwar hakan tuntuni. shi yasa tun a wancan lokacin, yay yay da Akila ta haƙura su kai yaran marayu, ta yanda ko da sun girma ba za su nemi iyayensu ba tun da sun san rashin gata ne ya kaisu wurin, kuma ko da watarana sun buƙaci iyayensu, amsa ɗaya za'a ba su ita ce ba'a sansu ba, shikenan asirin kowa ya rufu, ko kuma kaman yanda Aaliya tace ma ta a yasar da su to amma da yake ita tafi Aaliya kafiya, sai taƙi, tace sam ita ba zata iya ɗaukarwa kanta wannan babban zunubin ba, wannan rashin imani har ina, a haifi jarirai sannan a zubasu a leda aje a watsar. ya ƙara kallon lambar wayar da kyau, sai yabi bayanta da kira, sai dai daga can kamfanin layin MTN maimaita masa suke da cewar babu network, saboda haka yace da Al-Mustapha ya ba shi wayarsa, ya miƙo masa. sai dai ga tsananin mamakinsa ko da ya rubuta numbar a wayar, sai yaga sunan Sectary ya bayyana, wato Ahmad Adam Bichi. aikin Amadu ne, dan tun bayan da suka kawo Kulu asibiti, ya tuna labarin da ta basu, ya ɗau aniyar sai ya girgiza Major, sai ya saka masa tsoro a wannan zuciyar tasa ta rashin imani. dalilin da ya sa ya ɗauki hoton Kulu kenan da Mairo ya turo masa, tare da wannan saƙon.
*A Ɗaya Ɓangaren.*
saukar jirginmu a airpot ɗin Malam Aminu Kano mu ka fito hannuna na cikin na Al-Hassan yana riƙe da ni, tun bayan wasu daƙiƙu da tasowar jirginmu daga can Qatar na ke zubar da hawaye, hawayen da har yanzu suka ƙi tsayawa. Mami na gaba muna biye da ita a baya har mu ka ƙaraso bakin farar motar da aka zo ɗaukanmu, sai dai a san da aka buɗewa Mami murfin motar zata shiga a sannan na zube gwiwoyina a gabanta, cikin amon muryata da ta gama raunana, cikin sautin muryar da ke fitowa da rawa, cikin sautin muryar da zuciya ta ke a karaye, cikin sautin muryar kuka, na tattaro busassun yawun bakina da suka ƙafe na shiga roƙonta.
"Mami dan Allah kiyi haƙuri, dan Allah kiyi haƙuri kar naje wajen police, wallahi ban san a inda zan nemo kuɗi na biya Ya Kabiru ba, kuma idan naje wajensu tsare ni za su yi su kaini prison". kaina na ƙasa nayi maganar, inda ƙwayar idona ke a kan doguwar farar ƙafarta me ɗauke da zara-zaran yatsu. a jikina naji kallon da ta ke bina da shi, tsawon daƙiƙa 1,2,3,4, bata ce komai ba, ko ba'ace ba nasan nazari ta ke, haka zuciyata ta faɗa min, cikin wannan ƙunar da ke zuciyata, ta cikinsa naji gilmawar furucin Al-Hassan da ya ce da ita,"Please Mami, ki min alfarmar idan mun je wajen Kabir ɗin ni zan biya shi kuɗaɗensa". shirunsa ya haɗu da maganar da nayi,"balle ma ba zai taɓa cewa na biya shi ba". sai kuma Mamin tace,"sanin cewar ba zai ce ki biya shi ba shi yasa kika sata kenan?". nayi saurin girgiza kaina da sauri,"a'a wallahi Mami, ba haka ba ne, sharrin zuciyata ne". sai ta ƙara cewa,"to ni ba ɓarauniya bace, dan haka ba zan yarda na haifi ɓarawo ba". sai na ƙara fashewa da kuka ina faɗin,"Mami wallahi tallahi ban taɓa sata ba, ban taɓa ɗaukar abin wani nayi amfani da shi ba, yanzuma tsautsayi ne, dan Allah kiyi haƙuri kar naje gaban ƴan sanda".
zuƙar nunfashi ɗaya tayi sannan tace,"ku shiga mota mu wuce". dai-daituwar zamanmu a motar Al-Hassan yasa handky ɗinsa yana goge min hawayena, muryarsa a hankali ta fito ta cikin shirun motar.
"ba za ki daina kukan ba kuwa". amon muryar ya fito da sautin nuna damuwa da kulawa. nima muryar tawa ta fita a hankali wajen ce masa,"zan daina, amma sai Ummi t