kake gumamar wari kuwa, ka gyara kaji, wataƙila ka samu ƴan matan ƙauyen da kake bi su daina gudun aurenka". Sai kuma na bushe da dariya sannan nace, "ko da yake matsalar ba daga wurinka bane, ashe daga wurin tsoho na gida ne da baya iya bada sile a saya ruwa a gidansa, tsohon da baya gajiya da kunyatar da iyalansa". Maganata ta soki Auwalu saboda haka cikin fusata ya kawo hannunsa fuskata na dakatar da shi da sauri. "kul ɗinka, dan wallahi ka sake ka taɓani yau ba zaka kwana lafiya ba a garin bichi, dan sai nayi maka sharrin da zaman cikin garin bichi zai gagareka har a bada...Kuma dama zuwa nayi na maka fashin baƙi akan matsiyacin tsoho me farin gemu, wanda ba kowa bane sai ƙazamin Ladanin masallacin gidan ƙofa, baƙi wuluk da shi haƙoransa duk sun yi kanta da goro, yana tafiya a noƙe kamar mutumin kirki nan kuwa baƙin munafiki ne, mutumin da duk inda yaji ana raba zakka shi ne a sahun farko, wanda kullum ka gansa gaban masu kuɗi a duƙe tsabar maula, asararran tsohon da baya iyaci da iyalinsa sai dai matarsa taci da su, mutumin da ake zuwa har gida a titsiye ya biya bashin da yayi ƙarya da sunan ɗansa ya karɓa, uban da baya iya aurar da ƴaƴansa sai sanda yaji gwamnati na batun aurar da zaurawa sannan yaje ya kai sunansu, tsohon da ƴaƴansa basa ganinsa da gashin ido, mutumin da idan jama'ar gari suka bishi sallah a sanda tantantama akan sallarsu. Auwalu wannan shi ne matsiyacin tsoho me farin gemu na cikin garin bichi, idan kuma kana tantama sai na baje maka magana a fefai ta yanda zaka gane kai ɗin ƙaramin mara kunya ne, ka kuma gane ba kowa bane soko irinka da za'a taɓa mutuncin ubansa ya ƙyale".
Auwalu dai tuni yay suman tsaye, na gama da shi dan haka bana buƙatar ci gaba da tsayuwa kusa da inda yake, sai kai na dana ɗaga na maida dubana ga saurayi ɗan birni nayi masa banzan kallo, kana na dubi Adawiyya kafin nan na yatsine fuska cike da takaici nace mata, "ke daman wannan tsamurmurin kika kasa maidawa martani, dube shi fa abu kamar maburgin kaɗa kuka, ke ba kyace ɗan birni ba, dan yafi kama da mutanen ƙauyen da basu ci sun ƙoshi ba, to har me zai tsorataki a tare da shi, farin ko kuma tsayin? To idan farinsa ne farare nawa Allah ya bayar acikin gidanku, idan kuma tsayinne dogaye nawa ne acikin gidanku wanda idan wannan tsolon ma ya tsaya a gabansu shi wada ne, amma dai kin gwaigwayi asara da yawa, ko da ike shi ya fiki asarar da ya kasa amfani da iliminsa, kinga kuwa da shi da jahilin duka ɗaya, kuma banda abinki ai sai ki faɗa masa tsohuwa ma ta gida asalinta ƙauye, wataƙila ma naku ƙauyen yafi nasu arziƙi dan ba lallai anasu zamanin turawa sun shiga ƙauyen ba, ƙila ma bata san da jar fata ba sai da arziƙin aure ya fito da ita daga ƙauye zuwa birni, ƙoɗaɗɗun kaya kuma ai sai kice yaje ya tambayi tsoho ko kuma tsohuwa acikin wacce iriyar sutura suka tashi, idan su basu saka ba na sama dasu ai sun saka, kinga kenan koɗaɗɗun kaya ba daga ke bane daga zuri'a uban kowa ne". Na kama hannunta ina cewa muje, kafin na kai ga ɗaga ƙafata naji an riƙo mayafina da ƙarfi har yana kusa zamewa daga jikina, na juyo a fusace. "wai kai wanne irin mara ɗa'a ne da zaka dinga kama suturar macen da ba muharramarka ba. nan fa ba can idan aka raineka bane, dan haka kasan a inda kake, ko kuma dan kaji mara kunyar yaronka na cewa muna yawo kwararo-kwararo shi ne kake neman wuce gona da iri, to ai gaka ga shi nan sai ka tambayeshi zamanin da yaji anyi waɗannan ƴan matan fanɗararru, kace ya baka labarin ita kanta shugabar tasu nawa aka zubar kafin ai mata maganin abun a ɗaureta da igogin aure har aka haife shi. Dan haka ni sakarni idan ba haka ba kuma nayi maka ihun kwarto".
Auwalu ya ka da baki naji yace da shi, "Yallaɓai sakarta dan zata aikata, kuma wallahi ka shiga hannun mazan ƙauyen nan sai dai a haifi waninka". Naja musu dogon tsaki na kama hannun Adawiyya muka barsu a wajan.
Dai-dai da zamu shiga gida muka jiyo maganar Mubarak a bayanmu yana kwaɗa mana kira. Muka juya ni da Adawiyya muna dubansa, ya ƙaraso gabanmu yana cewa, "lallai Mairo, shi ne kika yiwa manyan mutane rashin kunya ko, bayan kin san Baba ya ce mu dinga girmama na gaba damu a duk inda muka gansu ba lallai sai na cikin gidanmu ba, kuma ma ai an hanaki faɗa ko". "to ai su suka yada girman nasu ni kuma nabi ta kai". Na faɗa ina hararsa gabana kuma na faɗuwa, dan babu makawa wannan zancen ƴaje kunnen Baba na kaɗe dan ko neman ba'asi ba zai tsaya ji ba. Adawiyya tasa hannu ta dungure masa kai bayan ta harare shi tace, "munafuki kai aina ka ganmu ma". Yana jijjiga kai yace, "ni ne munafukin? Za kiga ƙarshen munafurci". Ya faɗa yana sa kai zai shiga gida muka yi saurin riƙo shi, muka hau lallashinsa muna ba shi haƙuri akan dan Allah kar ya faɗa, da ƙyar muka sha kansa yace ba zai faɗa ba amma sai mun ba shi naira hamsin, na marairaice masa fuska nayi kalar tausayi.
"haba Mubarak duk wanda fa ya rufawa wani asiri shi ma Allah zai rufa masa. Yanzu idan kace mu baka hamsin aina zamu sam