NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 139 of 223

je Ya Rufe Mahaifin Nasa, Duk da Mahaifin Nasa Ba Musulmi Bane. sai dai karkayi duk abin da Muslunci yace kar ayiwa wanda ya danganci jana'izar waɗanda ba musulmai ba kamar yi musu Addu'ar neman Rahama, da duk wani bukukuwan da ake yi, da raye-rayen da akeyi da sauransu. Allah Ubangiji Ya Baka Juriya da Haƙuri Ya Kuma Tabbatar da kai a Musulunci"._ maganar ta ƙara haskawa acikin kansa a karo na babu adadi tun bayan da ya tabbatar da mahaifiyarsa ta bar duniya. amsar da Malam Liman ya ba shi kenan a da ya kirasa a waya yay masa tambayar,_"Malam shin a addininmu ya halatta na halacci jana'izar mahaifiyata matsayina na musulmi ita kuma kiristan?"._ sai kawai ya kuma rumtse ido gam, tabbas shi yafi kowa rashin dacewa, zai iya kiran kansa da hakan. ganin cewar ba zai iya yiwa mahaifiyarsa wata adu'a ba, babu wani abu da zai iya yi ma ta domin ta dace da wannan Rahmar ta ubangiji, lokaci ya rigada ya ƙure ma ta, to amma kuma a ɗazu Liman yace da shi,"Kul ɗinka Al-Mustapha, kar ka ƙara cewa kai kafi kowa rashin dacewa, Allah yana sonka, domin da ba ya sonka da bai haska zuciyarka da hasken musulunci ba". sai ya haɗiye wani abu da bai san mene ba a maƙoshinsa. kuma yana cikin wannan yanayinne Obi ya turo ƙofar ɗakin ya shigo, ya ƙaraso bakin gadon ya tsaya, ganin yacca hawaye ke sunturin sauka ta gefen fuskar Yayan nasa sai shi ma yaji zuciyarsa ta ƙara tsinkewa, yasa handky ya goge nasa hawayen kafin ya buɗa baki yay masa magana. "Bros Dad yace ka kira Michel ka sanar masa yaje Dunamis International Gospel Centre, a can za'ai bikin mutuwar. amma ya hanzarta wajen yin decoration na wurin". maganar ƙanen nasa tasa yaji zuciyarsa ta ƙara matsewa, bai motsa bai kuma amsa masa ba, bai kuma nuna yaji shi ba. tsawon daƙiƙa biyu Obi ya juya ya fita ya bar ɗakin, babu jimawa da fitar tasa sai ga Dad ya shigo. daga tsakiyar ɗakin ya tsaya yana saƙale da hannayensa ta baya, wanda hakan yake ɗabi'arsa, fuskantar ɗan nasa yake da tausayi, kamin ya kira sunansa,"Emanuel". a can duniyar da ya faɗa yaji sautin muryar mahaifin nasa, da sunan da ya fara mancewa da nasa ne. ya buɗe idanuwansa a hankali kamin ya miƙe zaune ya amsa kiran Mahaifin nasa. "ka bar kukan haka, ka tashi ka shirya zamu wuce chapel, Pastor yana jira karmu ɓata masa lokaci, zai bar ƙasar ne yanzu". kansa a ƙasa yaji maƙogoransa ya bushe, da ƙyar ya iya tattaro wata jarumta da yake ganin kamar bai da ita yace,"Dad ni ba zan sami damar zuwa chapel ba don bikin mutuwar Mom da Granny...". bai kai ga ƙarasa zancen nasa ba Dad ɗin yace,"what! are you mad?". ya miƙe tsaye ya fuskanci Dad ɗin sannan yace,"Dad i am not a christian now since last three days past, i am now a muslim...". tamkar saukar tsawa a cikin duhun dare, tamkar ƙarar bindiga a cikin tarzoma, haka maganar ta sauka a kunnen Major, ya waro dukkan idanuwansa waje yana duban ɗan nasa da ɗumbin mamaki. bai ga wani abu related to kayan maye a ɗakinsa ba balle yace Emanuel ya sha ya samu gushewar hankali, haka kuma bai yi masa kama da mahaukaci ba balle yace ciwon ya kama shi ne babu jimawa, to amma me ya shiga ƙwaƙwalwar yaron?, kan ya jefa wata tambaya ga Emanuel ɗin sai ya tsinci kansa da haska masa cewar tabbas zai iya musulunta, kuma ya musulunta ne ata dalilin yarinyar nan da aka ƙi ba shi aurenta, ya yarda ba zai ƙaryata ɗan nasa ba, tun da ga shi nan babu wannan sarƙar cross ɗin da ba ya taɓa rabuwa da ita. gaskiya ne! yanzu ya yarda da cewar so yana sawa mutum ya zare ya zama taɓaɓɓe, gashi ya gani akan ɗansa, sai dai shi ba zai lamunci wannan haukan ba, dole zai yi masa maganin abin, dama shi ba me tolerating wani iskanci daga yaro ba ne, bare kuma yaron yazo masa da maganar da kansa ma ba zai ɗauka ba, yana jin zai iya ɗaukan ciwon haukan Emanuel kowanne iri ne, amma banda wanda ya shafi wulaƙanta addininsu, how comes ma zai fuskance shi kai tsaye yace masa ya musulunta, ina ya samu wannan ƙwarin gwiwar?, ko kuma shi ne dai ya rasa wannan girman kwarjinin da yake da shi ba tare da ya sa ni ba?, ƙwarai zai yiwa tufkar hanci, yanzu kuwa bada jimawa ba. to amma sai dai me? kamin ya kai ga ɗaukar matakin ɓulan kan Emanuel da bindigar da ya zaro a gefen wandonsa, sai yaji Emanuel ɗin na magana, maganar da tasa yayi suman tsaye saboda tsantsar mamaki, babu tsoro balle shakkarsa a idon ɗan nasa, illama shi da yake ganin yau ɗan nasa ne yake masa kwarjinin, da kuma shakkar aikata masa abin da yake niyyar yi. "Dad kuje kuyi gaggawar abin da ya kamata ga gawar tasu, sannan kuma ku dawo ku karɓi addinin da nake a cikinsa yanzu tun kamin ƙurewar lokaci, domin ita mutuwa bata da notice, ni kuma ba zanso ace duk na rasaku a wannan addini na ƙarya da kuke ciki ba". Dad ya ɗaga hannu zai kai masa mari sai ƙarar wayarsa ya dakatar da shi, ya zura hannu a aljihu ya ɗaukota kuma dai-dai lokacin da kiran wayar ya katse, sai dai saƙon da ya biyo bayan wayar shi ya ɗan dakatar da shi yana kallon lambar wayar da aka turo saƙon da mamaki, da ku
🏠