NOVEL SHARES -
ka ki kaiwa Akila ba kamin gudowarki. to umarnin da zan ba ki da zarar mun isa ki duƙa a gabanta, ki zube gwiwoyinki a ƙasa, ki tattaro yawun baki da dukkan wasu tarin kalamai na ban haƙuri da suke cikin kanki ki bata haƙuri, ki nemi yafiyarta, ki bata haƙuri ki nemi yafiyarta...umarni na ke ba ki Maryam, domin akan Akila bani da kyau ko kaɗan, wallahi summa tallahi in har ta nuna min rashin jin daɗin rashin kyautawar da kika ma ta, na rantse da Allah zan manta da zafin naƙudarki, na saɓa miki kamanni ta yacca ba za ki taɓa ganuwa ba a idon duniya...furucina ne wannan, kuma alƙawari ne sai na cika shi".
shirunta yay daidai da tambayar da Al-Hassan ya jefa ma ta,"Mami wacce iriyar magana naji kina yi, wace me irin sunanki haka, kuma me kike nufi da abinbda kike faɗa?". duk da bana kallonta amma na san tayi murmushin da ya tsaya ne iyakar leɓenta, kuma sai naji ta bashi amsa da cewar,"kamar yanda ta ke a cikin duhu, kaima a cikin duhun kake, haɗuwata da ƴar'uwata ne zai haska muku hakan, har ku sami amsar tambayar da ke saƙe acikin zuciyoyinku...bana son wata tambayar Al-Hassan".
*Abuja, Nigeria.*
a cikin ƙaton falon gidan babu abinda kake ji sai sautin kukan da ke tashi daga bakuna da dama. daga tsakiyar kujerun da ke kewaye da wurin gawa biyu ce lulluɓe da jan ƙyalle, kuma daga gefen kan gawar Madam Gloria Joseph ne duƙe yana girgizata da kiran sunanta akan ta tashi.
Major ma na zaune kusa da gawar Granny hannunsa a cikin nata yana kukan rashin mahaifiyarsa. mutuwar da su kai ta dalilin hatsarin motar da suke akan hanyarsu ta dawowa daga Ibadan sun je taron buɗe wani flatfom da ita Madam Gloria ta buɗe.
*Comment & Share.*
[7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
_Ummu Naseem😍, Hajiya Fasilat me sunan labarabawa😘, Labbaiki Ya Zahra🥰, nace ba duk ku matso ku maƙale a katarar juna😅, page ɗin yau domin jin daɗinku ne💃, irin nishaɗin da kuke bani yasa nace dole in miƙo tukwici gareku💋, ina jinjina da gaisuwar ban girma mutanen kirki, Allah ya jiqan mahaifa🤲...shafin yau dai na bar muku shi sai kun so wani zai karanta😉._
*35)*
Acikin bedroom ɗin, a bakin gadon, Al-Mustapha ne zaune ya dafe kansa da dukka hannuwansa biyu, a gefe ɗaya kuma hawaye na sakkowa saman fuskarsa da yake jin zafinsu tamkar tartsatsin wuta ajikinsa.
ya miƙe a zafafe yay tattaki zuwa bakin ƙofa, ya murɗa handle ya fita, daga saman benen yake hango ƙasan parlon da jama'a ke kukan mutuwar mahaifiyarsa da kakarsa, ya rumtse ido yay taku uku baya sai gashi ya komo cikin ɗakin, a saman gado ya zube tare da saurin dafe kansa da ke barazanar rabewa gida biyu, kafin ya naushin gadon tare da faɗin,"Nooo!!". amon muryar ya fita da wani irin ƙaraji, har sai da ɗakin yay amsakuwa.
ya ƙara damƙe kansa sose yana me jijjiga shi kaman wanda zai yi hauka, ya zai yi ne wai?, me yasa mutuwa zata yi masa haka?, sai kawai ya ƙara fashewa da kuka tare da kifa kansa akan ƙafafunsa. Allah ya sa ni, tun bayan musuluntarsa yakewa ahalinsa kwaɗayin wannan addinin mai ni'imar gaske, tun a ranar da ya musulunta ya fahimci akwai tarin ni'imomi da ke cikin wannan addinin na gaskiya. zai iya rantsewa tun zuwansa duniya yana jin kansa da wani irin nauyi, nauyin da zai kimanta da wanda aka ɗorawa wani babban dutse, kuma kamar yana jin yafi kowa matsala a duniya duk da cewar ba shi da ita ɗin, ya sami gata da dukkan komai na rayuwa da yafi ƙarfin yaji zuciyarsa na cunkushewa.
to amma tun da ya musulunta sai yaji komai ya sauya masa, wannan nauyin da yake jinsa da shi babu, haka wannan matsalar da yake jin kamar yana da ita ita ma babu, tun daga ranar da ya musulunta sakayau yake jinsa, kuma zuciyarsa babu wannan cunkushewar da yake jin yana da ita ada. idan ya tuna rayuwarsa ta baya sai yaji yana tausayawa kansa, matuƙar tausayi na wanda ya kauce hanyar dai-dai yabi ta gargada, gargadar da ba zata ɓullar da mutum ko'ina ba sai ga halaka. to amma idan ya tuna sabuwar rayuwar da ya shiga a yanzu, ya kuma tuna Rahmar ubangiji ga bayinsa, sai yaji kamar yafi kowa sa'a da dacewa a duniya da Allah ya haska masa hasken musulunci tun kamin ƙurewar lokaci a gare shi. shi yasa yake roƙon ubangiji da ya haskawa sauran ahalinsa wannan hasken suma, domin su samu su rabauta a duniyarsu da kuma lahirarsu. sai ga shi a ranar da ya ƙudurta zai fuskanci ahalin nasa da maganar da yake ganin zata iya zamowa ƙarshensa a wurinsu, sai ga shi mutuwa ta ɗauke masa mahaifiyarsa, ta ɗauketa ba tare da ta tuba ga mahaliccinta ba, ta mutu zata je ta tarar da wannan azabar da aka tanadarwa irinsu. sai kawai yasa hannu ya matse goshinsa, yana kuma ƙoƙarin tsaida hawayensa, babu wani abu da zai iya yi ma ta shi kam, tata ta ƙare.
_"Ya Halatta Ka Halacci Jana'izarta Tun da Mahaifiyarka Ce Tana da Wannan Hakkin Akanka. A lokacin da Mahaifin Aliyu bn Abi Ɗalib Ya Rasu, Manzon Allah (SAW) Aliyu Ya Umarta da Ya