sancewar da larabci ta faɗa, ita kuma ta tafi tana nufar wurin da jirgi yake. wucewar daƙiƙa biyu na ɗago da ganina ga mutumin da tun zuwana wajen tsayinsa ya bani tsoro, mutumin da Aaliya ta tafi ta barni da shi, Al-Hassan! kuma tsoron da ke cikin zuciyata ya ninku da idona ya sauka akan fuskarsa, nayi wata muguwar razana naja da baya, ina kallonsa da maɗaukakin mamaki da al'ajabi gami da ruɗani. me ya kawo Emanuel nan?, kuma mene haɗinsa da ita?, tambayar da naiwa kaina kenan, sai dai kuma abin da ya gilma ta cikin idona shi ya bani tabbacin ba Emanuel bane me kama da shi ne, wanda zan iya kiransa photocopy of Emanuel. na haɗiye wani abu a maƙoshina da ban san ko mene ba, shikenan ya ƙara tabbata Major Tosin shi ne mahaifinmu, kuma ko ba'a faɗa min ba wannan shi ne wanda aka haifemu tare, duk da bama kama da shi amma kuma ga kama ta jini nan ina kallo ɓaro ɓaro a tare da shi. na buɗi baki zanyi masa magana sai naga ya zabga min wata uwar harara da tasa na ɓata rai kamar yanda shi ma nasa yake, na kuma bishi da tawa harar nima.
cikin ɗagin murya yay min maganar da ban san me ya faɗa ba, dan haka ina zumɓuro baki nace da shi bana jin yaren da yake ya faɗa da turanci. sai kawai yaja tsaki yay gaba abinsa ya barni a wurin, nabi bayansa da ido cike da haushi, _wannan miskilinne Yaya na?, tabɗi lallai ma, kenan ta ya zamu haɗa kai da shi wajen ɗaukar fansar haihuwarmu a shegu?_
kamar Aaliya tasan meke faruwa sai ta dakata da tafiyarta ta juyo, ban san me tace da shi ba, kuma shi ma ban san abin da ya mayar ma ta ba, amma dai a maganar da ta ƙara yi masa da turanci cewa tayi,"eh mana bata jin larabci, ka ma ta yaran da ta iya...kuma nima har muje mu dawo da english ɗin zamu ke magana kaji me nace ai". shi ma cikin harshen turancin yace,"to amma Mami wace ita?". daga in da nake na hangi irin kallon da tayi masa kamin ta bashi amsa da cewar,"uban ƴan kishi, to ƙanwarka ce, Hussainarka da aka haifeku tare". "Hussainata dai Mami?, da gaske kike?". tace masa,"ban san lokacin da na fara maka ƙarya ba balle na dinƙa shigar da rantsuwata cikin maganarmu kamin ka yarda da ni". da alama su na ɗasawa da shi, dan maganar tayi masa ne fuskarta tana washewa da annuri kamar ƙawaye, sai ya sake tambayarta da cewa,"to Mami ba ki faɗa min abin da zai kai mu nigeria ba". sai naji tace masa,"Mai Martaba Abi kayi haƙuri muyi tafiyar nan, idan muka je can duk zan amsa maka tarin tambayoyinka ranka ya daɗe, yanzu duk a matse nake da naje inda zan isa". sai ya juyo yana min harar ƙasan ido, kuma kaman wanda aka tursasawa yin maganar yace da ni,"zo ki wuce". ina ƙunƙuni da mummurguɗa baki na fara tafiya zuwa inda yake, har yanzu kuma Aaliya na tsaye tana kallonmu da jiran tahowarmu. tace da shi,"ka bata jakar ta riƙe, kai ka huta". maimakon ya bani kamar yanda ta ce sai kawai ya jefo min ajikina, sai naji nayi saurin tarota jikina gudun karta faɗi ƙasa, dan nasan akwai muhimman abubuwa a ciki, ga wannan masifaffar matar. kamar daga sama naji yace,"gaba nake da ke, so ki biyoni a baya ki daina shiga gabana". na ɗago na harare shi da kyau kamin nace,"ba haka Ya Kabiru yake min ba". "ko a suna akwai banbanci, Al-Hassan na ke ba Kabir ba". yace dani kenan yayi gaba, ni kuma nabi bayansa.
duk sun rigani shiga jirgin, kuma sai dana iso gaban jirgin naga a jikinsa an rubuta EMIRATE AIRLINE da manyan baƙi, a ƙasansa kuma an rubuta Shaik Samin Bin Hamad Al Thalis da ƙanan baƙi. nasa ƙafa na shiga ciki, daga can gaba na hangosu kowa kujerarsa daban, na wuce nima ina neman wurin zama sai naji Aaliya tace,"ki zauna kusa da Al-Hassan".
na zauna a kujerar kusa da shi, sai naji duk na takura, ga shi bini bini sai yay tawani ja min tsaki, yana hararata ta gefen ido, kamar ma me shirin rufeni da duka.
ban san lokacin da bakina ya furta,"Mami ni bana son zaman nan".
sai bayan na faɗi hakan kuma na kafeta da ido, gani nayi ita ma tana kallona, wanda na san sunan da na kirata da shi yasata shiga schock.
a hankali tace,"halin ku ɗaya. tashi ki dawo kujerar gabansa". sai yay karaf yace,"Mami ta dai koma ta bayana, ni ne fa babba". kafin tace da shi wani abu nace,"ai sai ka bari ka tabbatar da ni ƙanwar taka ce kafin ka yanke hukuncin kai ne Babba". sautin murmushinta kawai muka jiyo, tayi shiru bata ce damu komai ba, shi kuma sai yay guntun tsoki ya miƙe daga kujerar tasa ya koma kusa da ita.
na taɓe baki kamin na nemi wata kujerar na zauna, duk da hakan a kujerar gabansu na zauna, ina sane dan naga shi ɗan rainin hankali ne, bai san duk tsiyar da yake ji da ita ba na fi shi. ina jinsa yana cewa da ita,"Mami da kika tsintota ba ki faɗa ma ta ni jinin sarauta bane, izzata ba zata bari na ɗauki rashin kunyarta ba.". amsar da ta ba shi itace,"to sai ka fara koyawa zuciyarka sonta tun wuri domin ita ɗin dolenka ce". maganar Aaliya ta shiga kunnena a san da na kwantar da kaina jikin kujerar na rufe ido.
"a irin furucinki na rashin hankali a ɗazu, na tabbatar da cewa ba ƙaramin ɗibar albar