basu yi kama da magana ta hankali ba. kuma a jikina naji shigar kallonta, da na tabbatar da kallon nata gareni ta gefen ido sai naji jikina ya hau tsuma na tarin tsoron abin da zai biyo baya.
"yanayin da nagani a tare da ke ya shaida min cewar Akila bata kar ya alƙawarin da tasa muka ɗaukarwa juna ba. hakan yasa bata taɓa baki labarin cewa Uwarki Aaliya bata maimaita magana sau biyu ba, kuma idan har ta jefa tambaya da gaske tayi tambayar amsa kawai ta ke buƙata".
shirunta yay daidai da shigar leɓena na ƙasa cikin bakina na ɗan tsotsa sannan na bata amsa da,"bana aikin komai kuma bana sana'ar komai. lokacin da gaskiyar ta shiga kunnena zuciyata ta yanke shawarar barin kusa da duk wanda ya sanni na koma inda babu wanda ya sanni, domin zuciyata ba zata iya naɗar baƙin cikin rayuwar shegantani da jama'ar garin bichi za su dinƙa min ba, dan ko na tambayi ita matar dalilin da ya sa tayi zina ta haifeni bata da wata ƙwaƙwarar hujjar da zata bani wacce zata wanke laifinta a gareni. shi yasa da zan taho na ɗauko wallet ɗin Ya Kabiru na taho da ita, da ATM ɗinsa na biya kuɗin komai tun daga kan Passport har kan ticket...". yanda na lura kamar tana da azarɓaɓi ko me zance?, domin ban idasa zancena ba ta jefo wata tambayar acikin maganata.
"da ma ke ɓarauniya ce?". tambayar da tasa babu shiri na ɗago kaina na dubeta kenan, sai dai tsoron wannan manyan idanuwan nata masu kama da na zakanya ba su bar ni naci gaba da kallonta ba, nayi saurin sauke kai ƙasa ina girgiza ma ta kai da cewar,"a'a ni ba ɓarauniya bace. wallahi ban taɓa sata ba, Gwaggona da Babana ba su ɗorani akan wannan bigiren ba, sun bani kyakykyawar tarbiyar da zan nisanci duk abinda yake ba mallakina ba...".
yanzunma dai ban ƙarasa ba ta kuma katseni,"kin taho ne bada sanin kowa ba, haka zuciyata ta faɗa min a san da kike furta kalaman rashin ɗa'arki gareni a ɗazu...shi yasa yanzu a maganarki na tsinci cewar bada sanin Kabiru kika ɗauki wallet ɗinsa ba, me hakan ke nufi kenan?". na haɗiye wani yawu na daban, na bata amsa da,"sata". na faɗa muryata na rawa.
sai ta jijjiga kanta kamin tace,"da kyau! saboda haka da mun sauka a nigeria kanki tsaye ki wuce police station ki miƙa musu kanki, ki sanar musu kin saci wallet kin kuma yi amfani da kuɗin mamallakinta da suka fi ƙarfin riƙewarki. na san za su nemi Kabir, idan Kabir yace ya yafe miki shikenan, idan yace kuma bai yafe ba ni zan shige masa gaba wajen ganin yayi shari'a da ke kin biyasa kuɗaɗensa da kika satar masa kika biya buƙatar kanki, Maryam ko za ki dawwama a kurkuku sai na tsayawa Kabiru".
tayi shiru da maganartata, tare da ɗauke tab ɗin da ke saman cinyarta ta zira cikin aljihun jakar kujerar motar, sannan ta zira hannu a jakarta ta ɗauko wayarta da ke ringing ta kara a kunne, da larabci ta shiga magana saɓanin turancin da muke a ɗazu. kuma har lokacin idona bai bar kallonta ba da dukkanin iyaka adadin tsoron da ke cikin duniyata, tsoronta da tsoron abin da zata iya aikatawa da na tsinci tabbacinsa acikin furucinta da kuma saman fuskarta.
a yanzu zan iya cewa da gaske wannan ba Akila da na baro bace, da gaske zai iya zama wannan dabance, me daban ɗin da komai na duniyarta yake daban. sam babu sanyi a cikin al'amuranta, tun daga kan furucinta za ka shaida ita ɗin me zafi ce, da gaske take, kaifi ɗaya ce, ga wani kwarjini na daban da Allah ya bata, irin kwarjin da zaka ji kana shakkar yin magana a gaban mutum balle kuma haɗa ido da shi, ni dai nasan waccan da na baro ina iya kallon ƙwayar idonta, amma wannan sai dai ma na kalli fuskarta a sace, balle ta kai ga na iya saka idona cikin nata na faɗa ma ta abin da naga dama.
abu ɗaya na sani idan har da gaske ya zama ba ita ce Akilan da na sani ba, to kuwa in har zan miƙa ƙarar kaina, to ita ma zan miƙa tata, shari'ar sai ta zama guda biyu, na miƙa ƙararta akan haifata da tayi ba da aure ba, danni ba zan ɗauki wata kalma ta ƙaddara a cikin wannan lamarin ba.
tunanina ya katse lokacin da muka iso filin jirgi, maganar drivern ita ta katseni, dan ko dana dawo duniyar da nake rayuwa a ciki naga sai ni kaɗai a motar, ita ta fice tuni, na zuro ƙafata waje ina duban drivern da ya buɗen ƙofar da girgimamawa.
"ga ta can tare da Al-Hassan". drivern yace da ni a san da ya lura da kalle-kallen da nake na nemanta ne. na taka ƙafata ina tafiya kamar me ciwon cinya, sai ƙudundune hannayena nake ajikina har na ƙaraso inda suke tsaye. kuma da alama magana suke me tattare da nishaɗi duba da yanda haƙorin makka ɗinta ya bayyana a waje dalilin dariyar da tayi. nayi tsaye kamar wata munafuka a kusa da wanda ban san kowane shi ba, naji dai sunansa daga bakin direba. tare dai suke da shi, kaina a ƙasa ina wasa da zip ɗin rigar sanyin da ke jikina, ba zan iya kwatanta abin da nake ji atare dani ba, amma dai ina jin wani abu me kama da tsoro, taraddadi da kuma fargaba, ta ƙasan ido na hango ta ɗaga ƙafarta da zummar tafiya bayan tayi magana da Al-Hassan ɗin, amma ban san me tace masa ba, ka