fa ta tsakiya cikin ƙofofin Aljannah,(uwa ko uba), wanda yake so ya shiga Aljannah, to ƙofar tsakiya wadda da ka shiga tsakiyar aljannah zata kai ka ba gefe ba to mahaifi shi ne wannan ƙofar, mahaifiya ita ce wannan ƙofar". saboda haka in har mutum yana so ya shiga aljannah to idan yaga dama ya kula da wannan ƙofar idan kuma yaga dama ya jefar da maƙullin wannan ruwansa ne. hakana kada ka sake ka taɓa yin magana me tsauri ga iyayenka, su iyaye kullum so ake ka zama kana saka su cikin farinciki. kuma wallahi duk lalacewar iyaye sunfi ƙarfin ai ramuwar gayya akansu, haka kuma ba'a yin jayayya da su. saboda haka ina me horanku akan saɓawa iyayenku ko kuma ɓata musu domin Allah na fushi da wanda iyayensa su kai fushi da shi".
maganganun da ke yawo a cikin kaina kenan tun bayan shigowata cikin wannan motar, tunasarwar da Malamin makarantar allonmu yay mana kenan a ranar da Mahaifiyar wani yaro ta kawo ƙararsa makaranta. to amma ban san dalilin kutsowar wannan magana cikin kaina ba a halin yanzu, bayan an ɗauki tsawon shekaru da yinta. naja dogon numfashi sanyayyan ƙamshin da ya cika cikin motar yabi bayan iskar da na zuƙa. _"wallahi matsawar mutum yana so ya samu rahmar ubangiji, yaji daɗi duniya da lahira to yabi iyayensa, iyaye duk yanda suke iyayenka ne, balle Uwa da hadisi ya tabbatar da ma'aiki ya faɗeta sau uku"._ maganar Malamin ta ƙarshe ta kuma haskawa a cikin kaina, nayi saurin saka hannayena biyu na toshe kunnuwana, dan sam zuciyata na faɗa min kamar bata so wata nasiha makamanciyar wannan a halin yanzu, ko kaɗan bana so gwiwata ta raunana akan ƙudurinta na ɗaukan fansa akan Akila da Major, shi kansa tunanin rashin kyautuwar abin da nayi da wanda na ke shirin yi tun a sanbda na baro gida nayi watsi da shi, wataƙila zuwa san da na ɗauki fansa tukunna. saboda haka na san yanda nayi na ture hakan daga cikin kaina, sannan na dawo da ruɗani da na shiga a ɗazu, wannan Matar da ke zaune kusa dani, wannan matar da nasan Akila ce amma kuma tana ƙaryata hakan, _to dama ubangiji na halittar surar mutum a guda biyu ne?,_ tambayar da naiwa kaina kenan, kuma amsar da zuciyata ta bani ita ce a'a, babu ta yanda za'ai hakan ta kasance, ita ɗin ba kowa bace fa ce Kulun da kika sani, tana so tayi wasa da hankalinki ne.
sai naji zuciyata ta matse, saboda tunawa da nayi da marukan da ta sharara min a ɗazu, to a bisa wanne dalili?, ita fa ta zalunce ni. ta ke na saki wata gajeriyar ƙwafa acikin raina, ƙwafa me tarin ma'anoni a wajena. zan gani idan da gasken najeriyar zamu je, zanga iya gudun ruwanta a wajen rainin hankalin da ta ke neman yi min, idan har naga saɓanin abin da ta faɗa to tabbas zan nuna ma ta bata ga komai a ɗanyan kaina ba, hasalima abin da taga na mata ban ko buɗe shafin farko ba.
a cikin wannan duniyar saƙe-saƙen nawa, a cikinsa ne muryar Aaliyan da ke kusa da ni ta kutso ta cikin tunanina, amon muryarta ya fita da wani irin sauti a cikin shirun da ya ratsa cikin motar tun bayan shigowarmu, kuma sautin muryar da sai da ya girgiza allon ƙirjina.
"kin ce a jiya kika san komai, aina kika sami visa na shigowa ƙasar nan cikin lokaci kaɗan haka?".
simple tambaya ce tayi min, amma sai da zuciyata tayi wani irin duka a cikin ƙirjina, wani tsoro na daban ya dirar min, duk da irin daɗin sanyin ac'n da ke busawa a motar, amma maganar tata sai tasa ni shaƙar wata busashshiyar iska ta daban a maƙogarona, na haɗiye wani wahaltaccen yawu da zance ya wuce da ƙyar, ofcourse zuciyata na faɗa min Akila ɗaya ce, to amma na rasa dalilin da ya sa nake shakka da tsoron wannan da ke kusa dani a yanzu saɓanin wadda na baro a can, na tattaro yawun bakina na bata amsar tambayarta cikin sanyin murya.
"babu buƙatar da kuɗi basa biya maka a duniya in har kana da su".
"yi min dalla dalla". sai kawai na karkato da kaina ga barin kallon titi na dubeta, kamar ba ita tayi maganar ba, don kanta na kan wata ƙatuwar tab da ke saman cinyarta, kuma zan iya cewa hankalinta ba akaina yake ba, tana tattaro shi ne a san da zata min magana, da alamu tana ji da zallar izza da ƙasaita ne wanda suka bi jininta. kaman nayi shiru naƙi bata sauran amsar, amma tunawa da wannan zafin da ke jinin jikinta yasa ni babu shiri nace.
"na biya adadin wasu charges da suka nema bayan na nemi alfamar su barni na fita...". ban kai ƙarashen zancen ba ta jefo wata tambayar a cikin maganar tawa. "aikin me kike?, ko kuma sana'ar me kike?". tambayar tasa na ɗora ganina akanta da har yanzu fuskarta na kan tab, ata gefen fuskartata na hango tambayar da tayi min cike ta ke da tuhuma da kuma mamakin kuɗin dana bayar, duk da ban faɗa ma ta yawansu ba, amma tasan bill ne ba kaɗan ba. a wannan karon yawun da na haɗiya yafi na ɗazu zafi, to amma sai na noƙe naƙi bata amsar, nima na kauda kaina gefe nayi kamar ban jita ba, ina dalilin da zata tsareni da waɗannan tambayoyin, ai kar ma ta bari mu isa nigeria na tabbatar da ita ce ainihin Akilan da na sa ni, ina tantama akan maganganun da ta faɗa min, domin