NOVEL SHARES -
sannan ku ka samar dani. Akila ina fatan yanzu kin shaida wace ni".
idan na lura kamar tayi suman tsaye ne, saboda haka sai na buɗe jarkan swan water ɗin da ke hannuna na fesa ma ta shi duka a fuska ko ta samu ta farfaɗo daga duniyar tunanin da ta faɗa. sai dai me! kamar yanda na tsammaci dawowarta, haka na sami saukar marin da sai da ya kaini har ƙasa, marin da shigarsa ya haddasa ganin tartsatsin wuta acikin idanuna, marin da sai da yasa jina da ganina suka ɗauke gaba ɗaya, azaba tasa nayi zaman dirshan a ƙasa ina jiran dawowar hayyacina, sai dai ji nayi kamar a lokacinne ta ke wankeni da marin, da sauri na dafe kuncina ina sake mayar da numfashi da sauri sauri. a ƙalla na ɗauki tsawon daƙiƙa biyar kamin na dawo duniyar da na bari, kuma ina ɗago kaina naga har lokacin tana tsaye a gabana, da yanayin fuskar da na kasa fassara abin da ke shimfiɗe akanta, tunanina ya tsaya cak san da naji ta ambaci sunana.
"Maryam". ta faɗa da kakkausar muryar da ke shaida min da gargaɗi ne zai biyo bayan sauran furucin. sai dai nima zuciyata ta kai maƙura, dan ta jima da bushewa, ko kaɗan bana ma ta kallon wannan sunan na uwa da ake ambata, na miƙe a fusace zan kai hannuna fuskarta ta riƙeni ta watsar da hannun tare da sake sauke min wani sabon marin da ya fi wancan don lokaci ɗaya na nutsu. idonta kamar na mage akaina tace,"ki tsaya ki saurareni kamin na illata fuskarki da yatsun hannayena".
idan da ace ban san Akila ba, to tabbas zan rantse wannan ba ita bace, sai dai tambayar da tayi min ita ta wanzar da maɗakakin mamaki da al'ajabi a tare da ni. "ina Akila?". tambayar da ta min kenan, kuma sai da na ƙara maimaitata a cikin raina kamin nace da ita, "rainin hankalin naki har ya kai nan?, ko a duniyar karuwancin na ki ma...". a wannan karan marin da ta sakar min maganata ce ta ɗauke gaba ɗaya, kuma zan iya rantsewa idan na buɗe bakina babu harshe balle haƙori.
cikin tsananin ɓacin ran da zan iya rantsewa a duniyata ban taɓa ganin wani acikinsa ba ta fara ce min, "dan uwar da tai silar ubanki zuwa duniya, Akilan da kike kira da waɗannan kalaman rashin ɗa'ar taki ba ita ce ta haifeki ba, ni da kika ganni a gabanki ni ce uwarki da kika fito daga cikina, ni ubanki yaywa ciki ba Akila ba, ni Aaliya ni ce na haifeki. ita kawai sadaukarwa tayi, kuma akanta babu mahaluƙin da ba zan iya ɗaukan kowanne mummunan mataki akan aibantata ba, saboda haka ki iya bakinki kamin ki harzuƙa zuciyata. ina kallonki zuciyata ta bani ke ƴata ce, kuma sai kika zo da maganganun da suka tabbatar min da hakan". ta ƙara matsowa gabana ni kuma ina ja da baya, har ƙarshena ya kai jikin motarta, ina jin yanda zafin numfashinta ke sauka ajikina, gaba ɗaya nema takeyi ta juye min kamar zakanya, jikina kyarma kawai yake yi, ta miƙo hannu kamar wadda zan bawa wani abu, cikin wata razanniyar murya wadda ba irin ta mutane ba tace min,"ina Akila?, tsawon wannan shekarun ita na ke nema bake ba". shirun da nayi yasa ta bugan tsawan da yafi wancan, har ban san lokacin da na kai hannu ina neman ƙanƙameta ba,"ba za ki faɗa min ba sai na saka ƙafa na ɓalleki". ta faɗa tana zare min idanu. a tsorace nace da ita,"ai tana nigeria". kaman na fesa mata wuta haka ta shaƙo wuyana tana faɗin,"uban me ya rabaki da ita da har kika zo nan?". cikin saurin ba da amsa nace,"ai sai yanzu ta faɗa min asalina shi ne na gudo nan zan shiga yawon duniya". sai naga ta juya tana duban drivern da suke tare da shi tace,"ka kira Al-Hassan yay min buking tafiya nigeria yanzu ba tare da ɓata lokaci ba". sannan ta dawo kaina tace,"karki fasa shiga duniyar, idan kika fasa kuma ba ki haifu shegiya ba Maryam". ta ƙyasta yatsunta,"abu ɗaya da zan gargaɗeki idan bakinki ya kuma furta Akila sai na sa an datse harshenki, sunanta Ummi, sunanta Ummi ". a tsawace tai min maganar, tsawar da sai da tasa zuziyata ta harba, kuma babu shiri nabi bayanta muka shiga mota kamar yanda ta umarceni da idanuwanta.
*Pls Comment&Share.*
[7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
_Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._
*34)*
"Uwa da Uba su na da girma da daraja, Alƙur'ani ya fito fili ƙarara ya nuna mana mu kula da su. wajibi ne ƴaƴa su ɗauki nauyin yin magana ta mutuntawa da darajartawa ga iyayensu. Allah SWT yana cewa,"wala taƙul lahuma uffin". ana so ɗa ya zama me kyakykyawan saurare ga iyayensa. bima'ana idan su na magana kar ka katsesu ko da kuwa faɗa ne suke maka. ka zama me ladabi, haka kuma ya zamana kana tare da su ko da yaushe kar mutum yace zai guje su, haka zalika ka da kayi abin da za ka jawa iyayenka magana. Abu Darda yana cewa naji Manzon Allah yana cewa, "mahaifi shi ne ƙo