muhalli ne me kyau. inda sabo ai an saba zamu more dare ne kawai".
a wannan karan ba ƴaƴan cikina kaɗai ba, ni kaina sai da na kaɗa, na shiga rarraba idanuwana ina tunanin ta yanda zan rabu da su lafiya, ga titi sai ɗaikun motoci da ke wucewa.
babu shiri na shiga sakawa napep ɗin da ta zo wucewa hannu, Allah ya taimakeni kuwa ta tsaya, ban tsaya faɗa masa inda zai kaini ba na faɗa ciki ina ce musu na gode, nace da me napep ɗin ya shigo min da trolly ɗin, ban sami natsuwa ba sai da naga mun bar wurin gaba ɗaya sannan na shiga sauke ajiyar zuciya ɗaya bayan ɗaya.
munyu tafiya me nisa sannan me nepep ɗin ke tambayata,"Hajiya ina zamuje ne, dare fa yayi ƙarfe goma yanzu". ina zance ya kaini ne?, ni gaba ɗaya ma ban san wurin da zan dosa ba, kamar nace masa ya kaini matattarar karuwai sai kuma zuciyata ta kwaɓeni da hakan, ban san sanda bakina ya furta masa airpot.
"amma kin san kuɗinki zai ƙaru ko?". nace masa,"babu komai muje". a filin jirgin Malam Aminu Kano na sauka, sai da na sauka kuma na shiga tunanin wurin zuwa, da na zo nan da sunan hawan jirgi wacce ƙasar zan nufa to?, tayama za'ai nayi bucking a wannan lokacin?, ba lallai kuɗin da na ɗebo su isheni ba. dama na ɗauka ne dan siyan abincin da zan riƙa ci, da ƙananun buƙatuna.
security ya ƙaraso in da nake yana min magana akan na matsa daga wurin, naja trolly na na shige cikin reception, na ɗauko envelop ɗin kuɗin na shiga ƙirgawa, tun ina lissafin dai-dai har ya ƙwace min saboda yawan kuɗin, sai kawai na zuba musu ido ina kallo. can na miƙe na ƙarasa wurin cashier ya ƙirga adadin kuɗin naira miliyan ɗaya, na tambayeshi wacca ƙasa za su iya kaini?, yace min za su kaina ƙasashe da dama in har bani da wani kaya da yawa, har zan ce masa ai min ticket na saudiya sai kuma maganar Akila ta haska acikin kaina, Qatar!, dan haka kai tsaye nace masa Qatar. yace min akwai jirgin da zai tashi ƙarfe sha biyu da rabi, amma na sani in dai ticket na ke buƙata ayanzun nan kuɗin da zan biya sai ya haura ɗari biyar, babu yanda ban da shi ba akan ya haƙura ya samin duka 550 ɗin yace sai nayi addition ɗin 100k. na buɗe wallet ɗin Ya Kabiru na zaro atm ɗinsa na bashi, nace ya zara aciki.
ƙarfe sha biyu da rabi jirginmu ya tashi, kuma ƙarfe shida na safe jirginmu ya sauka a ƙasar Qatar. saukarmu a airpot na ciro wayata nayi serching hotel nearby. "Hilton Doha, Diplomatic District". nace da texi drivern na shiga na zauna na daidaita zamana.
online booking nayi dan haka ina isa kai tsaye stairs na hau zuwa room ɗin da na kama, ina shiga nayi wanka na shirya sannan na kwanta ina tunani kala kala, tunanin da ke neman tarwatsa zuciyata, hakan yasa na tashi na fito dan naga gari ko na sami sassauci a zuciyata.
tafiya na ke ina kalle-kallen yanda ƙasar ta ke gwanin sha'awa, ba irin nigeria ba, kowanne bulding nasu me kyau da tsari, gasu kansu mutanen garin masu burgewa. ina tafe ina karanta wani symbol ban sani ba kawai naji nayi karo da mutum wayoyin hannayenmu duka suka faɗi, muka sunkuya muka ɗauko mu nayiwa junanmu sannu, sai dai a san da hannuna yay gogayya da farin hannun da ke ɗauke da jan lallai sai naji zuciyata tayi bugawar da ko a san da naji cewar ni shegiya ce batayi ba, haka kuma naji ina shakkar haɗa ido da koma wace idan ta ɗago.
ko dana baro gida bana faɗuwar gaban da nake yi a halin yanzu.
"Sannu, kiyi haƙuri ba da sanina na bigeki ba". abin da na faɗa kenan cikin harshen turanci, sai dai ita abin da tace min da larabci ta faɗa. da ma nayi goggling akan yaren ƙasar english da arabic kawai suke ji saboda haka ne ma yanzun na bata haƙuri da english.
ɗagowar da zanyi da kaina kawai sai naga Kulu a gabana, kallonta nake da maɗaukakin mamakin da ke haskawa a ƙwayar idona, tare da wani kallo na daban da ni kaɗai nasan ma'anarsa. ita ma kallona ta ke da mamakin, mamakin da zan iya kiransa na rainin hankali, dan ko ban rantse ba yacce idanuwanta ke nunawa shaida min yake ba su gane ni ba.
sai na buɗi baki nace,"hmm mayaudariya kawai". na faɗa tare da bangajeta zan wuce, ba ganinta a ƙasar ne mamakina ba, yanayin canjawarta shi ne abin mamakina, kai bakace matar da na baro cikin wani hali ba, ta gudo ta barsu cikin tashin hankali.
sai naji ta dafo kafaɗata, na dakata da tafiyar ta zagayo gabana. cikin fusata nace,"wai nufinki hakan da kike shi zai sa na sauka akan ƙudurina ne. ko kaɗan bana tausayinki, kije kiyi rayuwarki nima nayi tawa, kije ki ɗora daga inda kika tsaya, nima zan shigo sahunku".
da mamakina na rainin hankalinta sai ji nayi tace,"bana jin abin da kike faɗa cikin yaren da kike magana, yare biyu nake ji arabic and english, kina iya min magana da su". nayi mata wani kallo na kin raina min hankali, naja tsaki zan wuce maganarta ta dakatar da ni. "please who are you?". na zuƙi numfashin fusata na sauke sannan nai juyo gareta nace,"ni ce shegiyar ƴarki da kika haifa a yawon tazubar ɗinki, ƴar da sai da ku kai tarayya da ƙazamin abokin karuwancinki wato Major Tosin