a zan nufa?, ai kawai na biyewa shawarar zuciyata na shiga duniya shi ne kaɗai mafita, domin da shi na dace. duk da cewar a duniya ba zan taɓa mantawa da Baba ba, sai dai shi ma ba zan ƙara waiwayarsa ba tun da ya ɓoye min asalina, mene yasa tun farko ba su sanar min wace ni ba sai da aka zo wannan gaɓar, shi ma kuma da banji ba shikenan haka za su ci gaba ɓoye min?, har sai sun aurar da ni sunja min baƙin jini a wurin dangin miji?, tabbas a yau idan na bar garin nan ba zan kuma waiwaiyen wannan gidan ba illa kawai na san duk inda zan shiga Baba da Gwaggo su na nan maƙale a zuciyata, kuma ba zan fasa binsu da adu'a ba.
wani guntun murmushi me ciwo da takaici ya subce min a saman leɓe, wato Akila ma bata da tunani, da har ta ke tunanin ta ƙaƙabawa Ya Kabiru ni ya aura, saboda dai ita zuciyarta azzaluma ce har yanzu bata rissina daga saɓon Allah ba. ban da haka ina Kabiru ina ni Hussaina shegiya, dole Baba yaƙi amincewa dan shi yasan ɗansa bai cancanci auren mace mai gurɓataccen asali irina ba. kuma ni kaina ko da zan mutu babu aure ba zan taɓa aurensa ba, dan yafi ƙarfina, ni shegiya shi kuwa cikakken mutum me cikakken usili, ai abun ma babu gami.
ina cikin wannan tunanin naji an buɗe ƙofa, ban ko waigi wajen ba. Adawiyya na gani tsugune a gabana tana kiran sunana, ni dai da ido kawai nake bin ta dan ko motsi ban ba. tasa hannu ta shiga warware ni da igiyar tana ɗan shashsheƙar kukanta, kukan da ko ban tona zuciyarta ba nasan na munafurci ne, ƙasan ranta fal frinciki, yanzu kuwa ko babu asiri sai su karɓe Al-Mustapha da hannunsu, ko ba shi ba ma ni na bar musu kowa ne.
"sannu kinji ƴar'uwata". ta faɗa tana rungumeni. sai kawai naji saukar wasu sabbin hawayen na sakko min, na buɗi baki murya na rawa nace,"ashe kema kin jima kina min kallon ƴar zina shi ne ba ki taɓa faɗa min ba". ita ma muryar tata rawa ta ke tace,"wallahi ban sani ba. ni ban taɓa sanin da wannan zancen ba". na haɗiye guntun yawu da cewar,"ta ya akai kika buɗeni?". tace, "dagani sai Inna ne a gidan, Baba da su Yaya da Yagana sun wuce kai Ummanki asibiti tana ta aman jini har ta kai ga ta suma, kuma an yayyafa ruwan amma bata farfaɗo ba, shi ne Idris me chemist yace su wuce asibiti...Ya Kabiru bai sani ba na zare maƙullin a aljihun wandonsa". sai na sake yin murmushin da sautinsa ne kawai ya fita, na furta,"Allah yasa ma mutuwa tayi, ta hutawa kanta daga hukuncina. na gode miki".
nasa hannu na hure ma ta ido daga tsareni da shi da tai, na ɗaga ma ta gira da cewar,"yane, ki tashi ki fita kar tsautsayi ya dawo da Ya Kabiru ya tadda ke anan, kin san halinsa sarai". sai tayi azamar miƙewa da cewar,"to kema ki fito dan Allah, Inna ma tace karki zauna ki gudo ɗakinta, ko me ki kai ai ba laifinki bane". "jeki kawai, ki ja min ƙofar yanzu zan fito".
bayan fitarta na tsawon daƙiƙa uku kamin zuciyata ta gama ayyana abin da ya dace da ni a yanzu, saboda haka na miƙe na ƙarasa ga ƙatuwar akwatin Ya Kabiru me shegen kyau, na buɗeta na shiga binciketa, har nayi nasarar samun wasu kuɗaɗe masu yawan gaske da ban san iyakar adadinsu ba a cikin wani envelop, na gyara zaman trolly ɗin yanda ba zai fuskanci an taɓa masa wani abu aciki ba.
sannan na ɗauki p-cap ɗinsa na saka na fice daga gidan ba tare da ko su Adawiyya sun sani ba. gidan Yagana na wuce kai tsaye, da zuwana na ɗauki ɗaya daga cikin ɓaƙaƙen abayata da Ya Kabiru yay min tsarabarsu na saka, na lulluɓe jikina ruf ta yacce babu me shaidani balle ya nunani yace ga shegiyar can, na ɗauki akwatun kayana nayo waje, har na saka ƙafata akan dakalin ƙofar ɗakin sai idona ya zuƙo min wallet ɗin Ya Kabiru da ya ban ajiya ɗazu haɗe da wayata a ajiye kan shimfiɗar da na tashi, na koma na ɗauko ina goge hawayena ta cikin niƙabi, Allah ya sani zanyi kewar wannan ɗakin da mamallakiyarsa.
zuciyata bata yanke shawarar inda zan dosa ba sai da na shigo garin kano, na samu wuri na zauna gefen wani me sai da idomie, ban san wacce unguwa bace, ni dai kawai nace a saukeni a wurin. warin taba sai tasowa yake daga wurin me indomien da alama ƴan shaye-shaye ne mafi yawanci zaune a gun, kuma sai na jiyo ɗaya daga cikinsu na faɗin,"Baaba kaga wata mace da lulluɓin baƙin kaya ajikinta, anya ba ɓarauniyar yara bace". hantar cikina ta kaɗa, kamin na ɗago na kalli inda suke sai ganinsu nayi tsaye a gabana su na tuhumata. na yaye niƙab ɗin ina zazzare ido nace,"wallah ni ba me satar yara bace, matafiya ce dare ne yay min a hanya kuma ban san kowa ba anan". sai baƙin cikinsu wanda duk gashin kansa yafi muni yace,"kuma shi ne saboda ki jawa me so asara za ki zo ki zauna a irin wuraren nan". yana tangaɗi ya kama hannun trolly ɗina yana cewa,"muje na ba ki masauki zuwa wayewar gari". duk na bisu da ido, dan da ganinsu ba mutanen arziƙi bane, sai nayi saurin gyaɗa kaina da cewar,"a'a zanje hotel na kwana acan..". ban ƙarasa ba na tsakiyarsu yay wata iriyar dariya yana faɗin,"au ashema ƴar hannu ce, kawai to kizo muje muma can ɗin da za ki zauna