ya wuce su, tabi bayansu taɓa ƙara roƙon Addi Hauwa akan su barmu zuwa safiya. ni kuwa nace sai dai ita ta koma ciki ta kwana, amma ni ko za'ai gunduwa-gunduwa da nama na babu abin da zai maida ƙafata cikin wannan wajen, masarautar da gaba ɗaya bata fi girman lambun gidanmu ba. gaba da ba ya jinin sarauta ne mu, dan haka why Aaliya zata duƙa tana zubar mana da martabarmu da ƙasaitarmu, na ɗagota dan haushi na bata mari ko Allah zai sa ta sai tu idanma barin hayyacinta tayi, naja hannunta muka bar ƙofar masarautar da ko a mafarki bana fatan na ƙara ganinta. sarƙarta muka siyar mu kayi kuɗin jirgi muka koma, sai dai ko da muka je ethiopia can ma ba sauƙi, domin tuni Bella ta kira waya ta sanar musu, suka ƙi karɓata suka ce sai dai na koma wurin wanda yay min cikin muci gaba da rayuwa tare, Abbu yasa aka karɓe passport namu na shiga Qatar, Aaliya tace ba zata iya zama babu ni ba sai dai ita ma a koreta daga gidan. dan haka bada saninta ba na gudu na bar ƙasar na koma london da zama har lokacin da cikina ya shiga wata tara, kwatsam watarana naje asibiti sai muka haɗu da Major shi ma yaje, an masa aiki an cire masa bullet dalilin wani harbi da ƴan bindiga su kai masa. har ga Allah soyayyar Major ta riga tayi ginuwar da ba zan iya kimantata a cikin zuciyata ba, ina ganinsa sai na manta da duk halin baƙin cikin da soyayyarsa ta jefani a ciki, da baƙin tabon da ya bar min. shi ma cikin tsananin tausayina ya rungummeni yana ƙara bani haƙurin abin da ya faru, abinka da Mace raunin duk sai ya ban tausayi ganin Babban mutum kamarsa yana kuka da kuma tarin nadama ɓaro-ɓaro shimfiɗe akan fuskarsa. tare muka dawo nigeria da shi inda ya sa ni a wani gidansa na kano, duk bayan kwana biyu yana zuwa wajena kasancewar shi yana zaune ne a abuja. ranar da na tashi da naƙuda ba ya garin, Aaliya ta ɗaukeni muka tafi asibiti shi kuma yace yana kan hanyarsa ta zuwa, sai da na kwan ɗaya ina labour ƙarshe sai CS aka min aka ciro min twins, maimakon naji ina sonsu sai naji kaf duniya babu waɗanda nake ƙi sama da su, tun da Major ya damƙa min su a hannuna naji kamar na murɗe musu kai, ko nono da akai akai na basu nace wallahi ba zan bayar ba sai dai a yanke min nonon na zauna a haka, ko kuma su mutu, babu yanda ba'ai da ni ba naƙi, ga kuma ruwan nonon na zuba amma na ƙwammaci na sakeshi yana jiƙa jikina, ƙarshe sai Aaliya ce ta ɗau kofi ta tara ta zuba a fida ta basu suka sha sannan suka daina tsanyara kukan da suke yi. shi kansa Major da farko yana ta murna da ƴaƴan musamman macen kasancewar cikin ƴaƴansa kaf babu mace, amma daga baya sai murnar tasa ta ɗauke, yace shi ba zai iya karɓarsu ba yana gudun girmansa ya zube a idon duniya, nima nace masa bana ƙaunarsu tun da ban samesu ta hanyar da ta dace ba, saboda haka ya zubasu a leda kawai yaje ya yasar da su, ko kuma ya zuba su a kwali yaje ya ajiye me so idan ya gani ya ɗauka...".
tarin da ya sarƙe Kulu shi ya dakatar da ita daga bada labarin, abu kuma kamar wasa sai aman jini, nan da nan hankali ya tashi Malam yace ai sauri a kira me chemist, ita kuma tana cikin wannan hali babu sunan wanda ta ke kira sai na Mairo har bakinta ya ɗauke.
***tun da Ya Kabiru ya rufeni bai ko waiwayeni ba, tun ina hawayen har suka ƙyafe, kawai sai na karayar da kaina a jikin bangon ɗakin, na rufe idanuwana ina tunanin irin ƙaluban da zan fuskanta a sabuwar rayuwar da zan shiga, ciki kuwa har da aurena, auren da na tabbata sai an rufa asiri sannan za'a yishi, idan ma na sami me auren nawa kenan, ɗaya ɓari na zuciyata yace,_"to ke Mairo ban da abinki tunanin za kiyi ma yi aure ai bai taso ba, dan babu ɗan halak ɗin da zai auri shegiya, ba ki ga misali ga uwar taki bane, da tayi cikin shegen ai babu wanda ya aureta gata nan har yanzu a zaune...ci gaba da zaman gidan nan ma bai taso ba, yanda ƴan gari suka gama jin kowace ke shikenan kowa zai fara tsangwaramarki ana goranta miki, ai ki tashi kawai ki tafi ki nemawa kanki mafita, shege ai sai shiga duniya. kije kema ki ɗauko musu abin kunyar kizo ki dire musu a gabansu kowanne cikinsu ki bashi ɗai-ɗai."._ sai kuma ɗaya ɓarin zuciyarta tawa ya gargaɗeni da,_"kul, karki soma, ita ma mahaifiyar taki da hakan ta kasance da ita ƙaddara ce"._ sai kawai na rumtse idona gam da ƙarfi na furta,"a'a ƙarya ne ba ƙaddara bace, kawai dai ta zaɓi ta fito dani ta wannan hanyar ne, son zuciya ne irin nata, kuma wallahi sai na sata kuka ba zan janye daga ƙudurina ba". sai nayi shiru naci gaba da saƙe-saƙen neman mafita a gareni, mafitar fita daga cikin wannan ɗakin, ban da ace Ya Kabiru ya ɗaureni da ko daƙiƙa ɗaya ba zan ƙara ba a cikinsa, dan yanda nake jin wani mugun ƙarfi ajikina tsab zan jijjige ƙyauren ɗakin na ɓanɓare shi nai ficewata, kuma ba tare da kowa yay min burki ba, domin yanzu a shirye nake wajen karawa da kowa.
Akila ta riga ta goga min baƙin tabon da babu ta yacce za'ai na goge shi, sam ba zan iya ci gaba da zaman cikin gidan nan ba balle cikin garin, to idan ma na tafi in