ina ƙarshen matsalar tazo, ashe sabon fegi ne za'a buɗe, dan da muka komawa da Abi maganar sai ya ce duk da haka ba zai aura min shi ba, sai in har zai musulunta ne domin Allah ba dan auran ƴarsa ba. shi kuma Major ya ce shi mutum ne da ba ya ƙarya balle yaudara, ya faɗa musu gaskiyar abin da ke zuciyarsa kuma wanda zai iya, amma duk da haka Abi da Abbu da Jadd suka ce a'a. ni kuma naga ina dalili tun da dai yace zai musulunta kuma sai a hana shi?, kawai sai na yanke mana shawarar mu tafi wajen wani sarkin musulumin ya amsa musulunci a hannunsa sai kawai a ɗaura mana aure. nasan duk tsiya in har ya musulunta ɗin dole kowa ya haƙura. dan haka a ranar muka yiwa saudiya shigar dare, muka sauka a hotel da zummar da safe zamu isa wajen sarkin musulmai na ƙasar Major ya karɓi musulunci a hannunsa. ashe tsautsayi ne ya kirani wannan tafiyar, cikin dare ina cikin bacci sai ji nayi Major na amfani da ni. sam ba'a hayyacinsa yay min fyaɗe ba, dan ya farka ne shan ruwan dare sai yasha barasa yay overdose har ya fita daga hankalinsa gaba ɗaya. nayi kuka, nayi kuka kamar raina zai fita, yanda nake kuka shi ma haka yake kuka a wannan lokacin, ban da tsine masa babu abin da nake yi shi kuma yana bani haƙuri. nayi niyyar na kai Major kotu amma sai Aaliya ta hanani, amma duk da hakan ban haƙura ba na ƙudurta cewar sai nasa yayi nadamar da bai taɓa yi ba a rayuwarsa. babu wanda ya san da abin da ya faru dan mun rufe abinmu ni da ƴar'uwata, na koma gida naci gaba da rayuwata zuwa lokacin na cire Major a raina saboda babu abin da na tsana a duniya yanzu sama da shi. rayuwata taci gaba da tafiya kamar ta ainihi kowa na murna, kuma har Abi ya haɗa min gagarumar walima dan jin daɗina. har zuwa san da Bella ta dawo gida, kuma da zata dawo nigeria muka kuma biyota, bayan dawowarmu na fahimci cewar ina da ciki, cikin da ban san da shi ba sai da naji bayi na gulmar wai yanayina kamar na masu ciki. aiko ina zuwa asibiti likita ya tabbatar min, na yanke shawarar zuwa nayi abortion Aaliya ta hanani, amma naƙi ji na kama hanya babu wanda ya sani na tafi asibiti, da naje likita ya tabbatar min in har akace za'ai abortion nasa zan sami matsala kasancewata ƙaramar yarinya mahaifata zata mutu gaba ɗaya, nace eh na amince, sai da akazo yi sai akaga ba zai yiwu ba saboda ƙunguna na maza ne, hasalima ko haihuwa zan yi sai dai ayi min aiki. na dawo gida cikin takaici da tunanin neman mafita, nasan duk ranar da aka gane ina da ciki na gama kaɗewa, na ƙudurta barin gida na shiga duniya amma Aaliya ta dakatar dani, tace a'a mu zauna har zuwa lokacin da zai fito muga yanda ubangiji zai yi hukuncinsa. alƙalami yayi kaɗan ya faɗi irin tashin hankalin da nake ciki a wannan lokacin, kuma duk da abin da akaina yake amma tashin hankalin da ƴar'uwata ke ciki ya ninka nawa. na sha magungunan abortion sunfi kala a ƙirga dan har order na dingayi amma duka a banza, ga shi ina ta neman wayar Major na rasa, tsanarsa ta ƙara ninkuwa a saman ta da. wani dare mun fito daga turakar me martaba mun an gama hira, zamu wuce ɗaki Bella ta kira sunana, tace da Aaliya ita ta wuce ta kwanta. gabana sai da ya faɗi, dan ajikina na san maganar da zata fito daga bakin Bella, domin zuwa wannan lokacin cikina ya fara fitowa, maganar ma da Aaliya tayi min a ɗazu kenan muka kasa samun solution.
"cikin wane ajikinki?". tambayar da Bella ta jefo min kenan san da na zauna kusa da ita akan kujera. naji wani ras, na kuma ji maganar da girma, to amma ɓoye-ɓoyen me zan tsaya yi?, ko nayi bai da wani amfani dan shi ciki ba'a ɓoye shi, idan ma na ɓoye akwai ranar da gaskiya zata fito, saboda haka ba kwane-kwane kai na babu tsoro balle fargaba nace ma ta,"cikin Major". amsar da na bata kenan, kuma cikin daƙiƙar da na bata amsar, cikin wannan daƙiƙar tasa aka watsomu daga cikin masarautar bichi. haka ta ke, macece me alkhairi, macece da kaf dangi banga me mutuncinta ba, amma kuma daban ta ke da kowa a wajen yanke hukunci. na ciji yatsa har sai da na karya shi saboda tsananin zafin da zuciyata ke yi, ko kaɗan ba muyi tsammani ta yanda lamarin zai kasance ba kenan. ko kaɗan ban yi hawaye ba, amma kukan da Aaliya keyi a wannan lokacin zaka ce ne ma ko mutuwa ta rabamu da iyayenmu ne. ba wai ban damu ba, zuciyata ce ta ke tafarfasa saboda baƙin cikin irin korar karen da akai mana, kamar mu ba jinin Bella bane, kuma kamar bata taɓa saninmu ba. irin tozarci da cin kashin da aka mana ba zai misaltu ba, hasalima Addi Hauwa cewa tai dama ai ta lura tun da nazo ƙasar nan na ke bin maza, Bella kuwa ce tayi babu mu babu ita ko a lahira kar mu nuna mun santa balle a wata ƙasa da ta ke ƙasar haihuwarmu. da Aaliya na musu magiya ji nayi kamar nasa ƙafa na take ta dan haushi, ehh nayi abun kunya, amma matsayinmu yafi ƙarfin mu tsuguna muna roƙo a gaban wata halittar, ƙwarai ina da wannan izzar kam. dan baƙin ciki ma da nacewa Aaliya ta tashi mu tafi sai ce min tayi wai na duba agogo sha ɗaya na dare ina muka dosa a wannan lokacin bayan bamu da kowa da