NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 13 of 223

areni da idanu tare da jefo min tambayar, "ke me kike tunani haka za ki je ki kashe kanki a banza". Tambayar yayita ne a sanda yake janyoni daga tsakiyar hanya zuwa gabansa, sam banda yanzu da hankalina ya dawo jikina ban san ma nayi wannan tafiyar me tsayi ba, na san dai na fito daga ɗakin Baba da tambayar da Adawiyya keyi min, amma daga nan ban san inda hankalina ya cilla ba. Na dabarbarce na rasa ma me zance, sai naji ya sarƙe yatsunsa da nawa ya daɗa matso dani gabansa sosai, ya ranƙwafo da kansa kaina tare dasa yatsa ɗaya ya ɗago da fuskata na kalle shi, numfashina Da nasa suka gauraye wuri ɗaya, cikin wata iriyar murya da ban taɓa jinsa da ita ba yace,"Menene Mairo?". Murya a hankali ya tambayeni, na lumshe ido na buɗe sannan na bashi amsa da cewar kaina ke ciwo. "shi ne kuma ba za ki faɗa ba za ki wuce makarantar a haka?". "ai yanzu ne ya fara ciwon". Maganar Ya Amadu ta dakatar da Ya Kabiru da abunda yake son cewa. "ciwon kai ba?". Ya faɗa yana taɓa shatin jijiyar goshina da ta fito raɗau, Na ɗaga masa kai kawai saboda yanda nake jina jiki duka ba ƙwari, bakina har wani ɗaci yake yi, cikina kuma na ɗaurewa. Kasancewar su Suhail sun fito zasu tafi, sai Ya Kabiru yake ce musu dan Allah bari Ya Amadu ya bisu su saukemu ko a hanya ne zai kaini asibiti, Suhail yace da shi,"ka jika da wani zance Kabiru, ko motar aini mai bayarwa ne akaita, su fito mu tafi". Ya Kabiru yay masa godiya ni kuma ya buɗe min bayan motar na shiga, ganin Jawad aciki nace Allah ya kasheni in dai da shi acikin motar nan ni kam ba zani ba ƙwamma na mutu, Ya Kabiru ya doka min tsawa da rashin hankalin da yaga ina neman yi, ciwon ma har naji ya tafi. Shi dai Suhail kallona kawai yake da darun da nake bugawa, ban nutsu na shiga hankalina ba sai da Ya Amadu yazo. Da Adawiyya muka tafi aka sauketa a makaranta, Ya Amadu kuma ya bada uzurin rashin zuwana, sannan muka ɗau hanyar asibiti, ina jin Ya Amadu na cewa da Suhail na gwamnati za muje yace a'a bari mu wuce private, idan akace na gwamnati ne ciwon nawa har sai yayi worst basu duba ni ba, amma can inda za muje akwai file na ƴan gidansu sai a duba ni da shi. Kai tsaye wani haɗaɗɗen asibitin kuɗi muka je, sai dai ko kusa ban iya karanta sunan dake jiki ba dan rubutun kamar na aljanu, duk da cewar na iya karatu sosai amma nafi ƙwarewa a iya karanta Hausa, babu ɓata lokaci aka dubani aka kuma tula min magunguna, allura kuwa da akazo yi min nayi kuka na gode Allah, nurse ɗin kuma tasha Allah ya isa tafi cikin ludayi, na tsani allura ko ba'a kaina ba. A dubu Goma kaɗanne babu shi ne kuɗin da aka cajemu, kuma duka ba Ya Amadu ne ya biya ba Suhail ne ya biya, haka da muka fito daga asibitin ya saya min kayan marmari yace tunda tafiya zai yi ga kayan dubiyarsa. Ina jinsu su na maganar su zasu wuce ne gidan Sarkin bichi, Jawad na cewa Allah yasa idan sunje Fulani bata nan, Suhail kuma na cewa shi dama ba wurinta za shi ba, wurin Ammi zai je, dan akwai kyakykyawan albishir ɗin da zai kai mata. A yanzu ne kuma na fahimci Suhail da Jawad ƴan'uwana ne ba wai abokai ba. "Mairo ban yarda da amsar soyayyar kowanne namiji a waje ba, in har kika yi hakan Mairo ba zan yafe miki ba kuma zanyi miki Allah ya isa, duk wanda ya nuna yana sonki da aure kiyi masa kwantace da gidanku, ni kuma a ranar da yazo zan aura masa ke a lokacin ba tare da ɓata lokaci ba". Tun shigarmu motar haya bayan saukemu da su Suhail su kai muka hau, maganganun Baba dake ta aikin tariya acikin kaina kenan, kalaman da yayi minsu a kausashe kuma acikin faɗa. Muna dawowa gida na zube a ɗakin Gwaggo riƙe da ciki ina murƙususu a ƙasa, tun ina nishi har na daina na koma kuka wiwi ina kiran sunan duka ƴan gidan akan suzo su taimakeni, mutuwa ne zanyi. Mutum na farko da nasan yazo kaina Kulu ce, cikin tsananin tashin hankali da firgici ta tarairayoni jikinta, daga nan ban kuma sanin inda kaina yake ba sai farkawa nayi na ganni shimfiɗe a gadon Gwaggo. Gabana yayi mummunar faɗuwa ganin yanda Gwaggo da Inna Amarya da Kulu ke tsaye a kaina, kowanne fuska ɗauke da tsantsar damuwa, ni Gwaggo ma sai naga kamar tana jifana da mugun kallo da idanuwanta da sukayi jawur. Nayi saurin rumtse ido sakamakon wani abu me girma da ya fito daga gabana. [7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *MissAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* *4)* Daga can kujerar baya ɓarin dama na hangi Auwalu sai zare idanuwa yake yi, nayi ƙwafa domin tabbas da agabana yake zan iya shaƙe shi. matsawa nayi ɓarin da yake na tsaya, ina jin wannan saurayin ya fito daga mota idanusa kuma na bina da wani wulaƙattacen kallo, yaja mayafin da ke jikina ya riƙe, ni kuma na fizge domin bata tashi nake ba. Auwalu ya fito ya zagayo daga in da yake zuwa gabana, sai wani takun isa yake irin ta samarin ƙauye, shi alallai yana tare da alhazawan birni, na tsartar da yawun bakina a gefen ƙafarsa inasa hannu na toshe hancina nace, "kai kuwa Auwalu yaushe rabonka da wanka, kaji yanda
🏠