ba haka bane. lokacin da su major za su tafi har da ni aka rakasu airpot, domin maƙalewa Abi nayi nace sai na bisu, son samuna ma Major ya tafi dani, tsarabar da Major ya bar min ita ce kayan kakin soja da yasa aka kawo masa, bayan tafiyarsa wannan kaya sai da suka zame min tamkar uniform saboda kawai idan na saka ina jin kaman ina manne a jikinsa ne. bayan tsawon wani lokaci sai na shiga ran Major fiye da yanda tunani ke hasaso min...hmm wato shi namiji ne da yake da baiwar sarrafa harshe ta ɓangaren soyayya, mutum ne shi me kyan hali da dattako, Major ya ƙara siye zuciyata da irin salon soyayyarsa, kulawarsa da kuma kyautatawarsa. muka fara gudanar da soyayyarmu me tsafta acikin sirri ba tare da sanin kowa ba hatta Aaliya dan itama sai daga baya na sanar ma ta, bayan da soyayyarmu tayi nisa tsakanina da Major, ita ta goya min baya ga cewar mun san abu ne mai wuya al'amarin aure da mu ke burin cimma ya kasance. muna da ilimin addini cikakke tun muna shekara takwas muka sauke alƙur'ani, kuma mun sauke manya manyan littafan addinin tun muna shakara goma. nasan da cewar akwai haramcin aure tsakanina da Major amma hakan bai dakatar da ni daga soyayyarsa ba, ƙoƙarin da nake a kullum shi ne naga na dasa masa son addinin da yake shi ne na gaskiya har Allah yasa yace zai karɓi musulunci. na gama tsara sauran rayuwata ne da Major, hakan yasa nake lissafin cewar rayuwata babu shi tamkar mutuwa ce. ana haka kwatsam sarkin garin bichi ya kai ziyara cikin masarautarmu ta harar wato a ethiopia, da zai dawo Abbu ya ba shi kyautar auren ƴarsa Hauwa. ƙanwar Kakarmu me suna Bella ita ta riƙe Hauwa tun tana ƙarama, san da Bella zata taho ƙasar nan wurin Addi Hauwa ta taho tare damu, mun sami kusan shekara guda a ƙasar nan kafin na sanarwa da Bella halin da muke ciki ni da Major, tun bayan titsiyeni da tayi akan ita bata yarda da yanda alaƙarmu ke tafiya da wannan kafirin ba. ni kaina nasan na tako abin da yake da wuyar kasancewa, dan Bella ce tai sam bata yarda ba, idan har ma ta ƙara jin wannan shirmen maganar a bakina sai ta saɓa min. ni kuma a lokacin yarinya ce me taurin kai da ke da wuyar tanƙwaruwa, ina da taurin kai ina da kafiya ina kuma da tsananin zafin rai, banbancinmu da Aaliya kenan a halayya. naga babu dalilin da zai sa Bella ta yanke alaƙar da ke tsakanina da Major dan kawai tana kakata, ai bata kai wannan matsayin ba tun da aurena ba'a hannunta yake ba, mutum biyu nasan za su iya zartar da maganar aure akaina na kasa ƙetarewa su ne iyayen da suka kawoni duniya sai Jadda(Kakarmu da ta rainemu), bayansu ina ga babu me isa da iko akan aurena, haka zalika ba'a isa a hanani abin da nake so ba, bayan tun da nazo duniya ban taɓa son abu na rasa shi ba, ko menene shi Jadda sai tayi yanda akai muka same shi, hakama Abi, mutuwa ce kawai zamu ce muna so ya hanamu mallakarta ita ma kuma dan yana gudun karta rabamu da shi ne. Yarinya ce ni da ban fiya jin shawara ba, hasalima me min magana naji Aaliya ce kawai, ba wai ina da ƙiriniya ko fitina ba, a'a abin da zuciyata tace shi kawai nake yi, ba kuma na abin da zai sa na kauce hanya ba ko in zo ina danasani. shi yasa ko a san da Fadila ke ban shawara na nuna ban jita ba balle har na tunanin ɗauka, ni dai tun da har Aaliya ta mara min baya magana ta ƙare. ganin Bella da gasken gaske ta ke sai ta raba alaƙata da Major, yasa na sanar masa da halin da ake ciki, shi ma ya nuna min cewar ba zai iya haƙura dani ba, nima kuma na nuna masa ba zan iya haƙura da shi ba. dan haka na yanke shawarar ya saya min ticket naje na sanar da Abi shi zai san abin yi, ai Bella ba ita ta isa dani ba, ko Aaliya bata sani ba muka wuce Qatar ni da Major, sai bayan mun sauka ne Bella ta kira Ammi tana tambayata tace ma ta ehh nazo ni da Uncle ɗina babu jimawa. lokacin da na sanar da iyayena ba ƙaramin mamaki da kuma jinjinawa rashin hankali da kuma rashin kunya irin tawa su kai ba. Abbi ya sanar da Major wannan hanyar da aka ɗauko ba me ɓullewa bace, ya haƙura da ni tunda shi mutum ne babba da ya san ya kamata, ni kuma ina da ƙuruciyar da ban gama haɗa hankalin kaina ba, ni kuwa a yanda nake jina zan iya rantsewa nafi kowa ma cikar hankali da sanin abin da ya kamata. duk ta yanda naso abin ya faskara, kowa yaƙi goyan baya, ga Major da nake ganin yabi maganar Abi yana neman ya rabu dani, dalilin da yasa na shiga tashin hankali matuƙa a lokacin, ganin da gaske za'a rabani da abin so na, har na kamu da ciwon zuciya, ciwon zuciyar da ya kaini ga kwanciyar asibiti. lokacin kowa yay fushi dani, a asibiti ma Jadda da Umm ne tare dani kawai, sai Jadd(mahaifin Abi) da ya zo shi ma yay min kacakaca ba dan zuwa dubiya ba. Umm ita ta kira Major yazo ya lallashe ni ya taushi zuciyata ko Allah zai sa a sami sauƙin abin da likitoci ke faɗa, shi kansa da ya zo sai da hankalinsa ya tashi, hakan yasa shi yin alƙawarin da bai shirya ba, na cewar zai musulunta saboda ya aureni, kuma naji daɗin hakan matuƙa dan ko kwana biyu ban ƙara a asibitin ba na warware aka sallamemu. a tunan