NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 128 of 223

an ba, azo ai mana saukar aradu da ka muna cikin kwanciyar hankalinmu, ina mu ina jawa garin bichi faɗan arna". ta faɗa tana kama haɓa, Kabiru yay guntun tsoki yace,"kefa matsala ce da ke wallah". tace,"Kabiru gidan haya ma nan ya ganni ya ƙyale". yay kamar ya tashi ya bar wajen Amadu ya dakatar da shi. "Yagana ki gane mana wai, ita fa musulma ce shi kuma kirstan, anata miki magana da yarenki amma kin gagara ganewa". ta harari Kabiru tace,"ubana ɗaga muryarka ai ba ita zata sa na fahimta ba". sai kuma ta juyo ga Malam,"ka shiga tsakanina da Ɗanka". Malam yace da Kabiru,"kar na ƙara jin bakinka". Yagana ta dubi Kulu tana rissinar da kai a gabanta tace,"ashe da gangan kika turata can wajen ubanta, kika tashi hankalinmu anan mu bayin Allah. Allah sarki Suwaiba Allah ya saka ma ta. da kika san lokacin komawarta wurin ubanta yayi ai sai ki tattara ku tafi tare gaba ɗaya, mu san sallama ki kai mana, amma kina ganin yacca baiwar Allah nan Suwaiba ta kasance duk akan ƴarki, kika ja baki ki kai gummm saboda mugun hali irin na ku na arna, da ma ance kasa mutum a inuwa ya saka a rana". Kulu ta gigice tace,"wallahi Yagana bani na turata ba, ikon ubangiji ne kawai". Yagana ta taɓe baki,"daga baya kenan ingozi...ni wallahi da nasan kema kafirar ce ba zamu taimaka miki ba, tun da dama ai kun saba iskanci a junanku, to sai me dan kin haifi shegu kuma da gida za su koreki". Kulu ta shiga kaɗa kanta,"a'a ni ba kafira ba ce musulma ce, ƙaddara ce ta haɗamu da shi". Yagana ta ɗaga ma ta hannu, "kinga kar ki yiwa ƙaddara sharri, ina dalili, haka kawai da anyi abu sai ku ƙalawa Ƙaddara dan kunga bata da baki". Amadu yace,"ni dai gaba ɗayana kaina a ɗaure ya ke, dan komai ganinsa nake tamkar shirin film ko wani labarin littafi. dan Allah Baba wannan abin da ke faruwa da gaske ne?". Malam yace,"Amadu ya za'ai mu yi wasa da irin wannan al'amarin mai girma". "to amma Baba taya a kai Kabir ya san da hakan ni ban taɓa sani ba?". Malam yace,"za ka san komai daga bakin Kulu, nima ita na ke jira ta faɗa mana ainihin tarihin rayuwarta da kuma yacca aka yi Kabiru ya san komai". Kulu ta fashe da kuka sosai sannan ta soma da cewa,"mu biyu ne kaɗai a wurin mahaifinmu sarkin Qatar, tagwaye ne mu Aaliya da Akila. ni Akila ni ce ƙarama Aaliya ita ce babba. kamanninmu ɗaya tamkar an tsaga kara, hakan yasa ba'a iya banbacemu sai ta awarwaron zinaren da aka saka mana a hannu. a kaf duniya idan aka cire iyayenmu babu wani mahaluƙi da yake gane kamanninmu sai Major. mun girma a wurin kakarmu wadda ta haifi Mahaifiyarmu sarauniyar ƙasar ethiopia. a can muka girma dan bamu koma gaban iyayenmu dindin ba sai da muka shekara goma sha biyu. kasancewar muna da tsayi kuma Allah ya hore mana dirin jiki ga kyau yasa muke da farin jini a wurin duk wani ɗa namiji har ma da matan, gamu da saurin shiga rai. a wata ziyara da shugaban ƙasar nigeria ya kaiwa mahaifinmu na fara ganin Major Tosin, san da na fito zanje lambu shaƙatawa, ni macece mai tsananin son kyau, duk inda kyau yake ina wurin, kuma duk inda naga abu me kyau ina ƙoƙarin naga na mallake shi matuƙar baifi ƙarfina ba, hankaina ma tashi yake idan naga abu mai kyau na neman suɓuce min. wannan dalilin har yasa mahaifiyarmu ke min adu'ar Allah ya rangwanta min gudun kar wataran son kyau ɗin ya cutar da ni. ta in da muka banbata da Aaliya kenan a halayya bayan zafin rai. Major Kirista ne shi to amma a acikin arnan ma shi na dabanne, yana tsarin halitta da kyau taimakar wanda Allah yaywa rahma da samun hasken musulunci, ga duk macen da ta ɗora ido akansa zata so ace ta mallake shi domin ba shi da makusa sai ta ɓangaren addini, ta ko'ina Major yayi, kafin haɗuwata da shi fuskar Aaliya nake sawa a gaba nayi ta kallo ina jin daɗi saboda nasan duk wani abu da zan gani me kyau ya biyo bayan kyan halittar da muke da shi, to amma da na haɗu da Major sai lamarin yasha banban. duk da irin ƙarancin shekaruna a lokacin nasan mene SO domin an rainemu ne a gidan da ake wanzar da So, a kallo ɗaya zuciyata ta tabbatar min da ta kamu da Son Major. har naje lambu na zauna ina shaƙatawa hoton Major bai bar haskawa a cikin ƙwayar idona ba tamkar yana gabana, a san da Aaliya tazo kirana cewar Abi yace muje zamu gaisa da abokansa ba ƙaramin daɗi naji ba, saboda tun ganina da major nake neman dalilin da zai sa in samu kusanci da shi, har kasa controlling kaina nayi Aaliya da ta gane tayi ta tsokanata. kwanan su Major biyu a gidanmu kuma a wannan kwanaki na sami shiga a wajensa, kasancewar duk safiya ya kan shigo ɗakin motsa jiki kuma muma muna zama a ciki a irin wannan lokacin tare da Abi. nasan cewar shi ɗin Babban mutum ne dan ya ajiye kamata, to amma ko kaɗan hakan bai haneni kwaɗaituwa da shi ba, kuma har na kanji zuciyata na kishi kamar zata zama in to pieces idan naji yana waya da iyalinsa, a yanda ya ɗaukeni yake kula dani har ya kan sumbaceni kamar yanda ya lura al'adar gidanmu ce hakan, yana min ne duk a matsayin ƴa da yake kallona a wajensa, bai san a tawa zuciyar
🏠