a yay.
"amma dai wallahi anji kunya, a haka kamar ta Allah ashe fir'auna a zuci ne. ni dai zaman haukar nan naki dama ba tun yau na dasa masa ayar tambaya . ai yanda Marigayiya ta dinƙa ƙumbiya ƙumbiya da ke na soma shan jinin jikina, to tunda asiri ya tonu sai kizo ki fi ce ki bar mana gida ki koma inda aka koroki dan ba za kija sunan gidanmu ya ɓaci ba. ina dalili haka kawai babu dangin iya ba na Baba. da ma Allah ba azzalumin bawansa bane, muna cikin gida an munafurcemu an ɓoye mana ai dole Allah ya saka mana".
Kulu tai mutuwar tsaye tana duban Amarya da mamaki, sai dai ko kaɗan bataga laifinta ba. duk da cewar a zatonta ma ko Zulai ce zata tanka ma ta to amma ita bata ce komai ba sai ƴan habaice-habaice da ta hau yi, shi ma kuma da Malam ta ke.
Yagana ta kama hannunta suka wuce ɗakin Gwaggo, tare da cewa Amadu idan ya idar da sallah ya faɗawa Malam tana nemansa. Yagana tasa gefen mayafinta tana gogewa Kulu hawaye, wacce zuciyarta ke gab da bugawa a halin yanzu saboda wani abu da ta ke ji yana taso ma ta. "ki bar kuka Kulu, ƙaddara ce a rubuce ta ke kuma babu wanda ya isa ya kauce ma ta, matuƙar kinyi imani to ki karɓeta a duk yanda tazo miki. Amadu ya sanar min da irin ɗibar albarkar da shashashar yarinyar can tayi, kiyi haƙuri ranta ne ya ɓaci kuma akwai ƙuruciya akanta dole ai ma ta uzuri, gani za tai koma mene laifinki ne kuma da gangan kika aikata, kafin ta fahimceki dole sai ki fuskanci ɓacin rai". Kulu ta saka hannu ta goge hawaye kan tace,"Yagana ni yanzu tashin hankalina ɗaya ne, idan ba'a riƙeta ba tabbas sai ta aiwatar da abinda ta faɗa. wannan ƙazantar har ina...". tai shiru na tsawon daƙiƙa saboda kukan da ya ci ƙarfinta."Allah ya jiƙan Yaya da ma ta faɗa, sai abin da na gani. kuma tun farko laifinmu ne da bamu nuna mata cewar nima uwa ce ba wai abar ƙyama ba, ta yanda ko ƙaƙane zata ji ƙaina a zuciyarta". Yagana ta shafa bayanta,"kinga komai fa zai zama da sauƙi, yanzu kawai dan tana kan dokin zuciya ne. da zarar ta huce shikenan zata tuna cewar ke ɗin nan kece dai Uwa, Uwar gaske da ake nufi bata wasa ba, Uwa me daraja". Sallamar Malam da Amadu ta karkata hankalinsu garesu, Yagana ce kawai ta iya amsawa, su ka nemi wuri suka zauna, daga ba ya kuma Kabiru ya shigo shi ma har lokacin jikinsa bai bar rawa ba saboda ɓacin ran da ke tare da shi.
"ina Adamu". Yagana ta kira sunan Malam. "na'am". "yauwa kana jina ai, yanzu tun da anzo kan wannan gaɓar, to zaman Kulu a tare damu ya ƙare. da ma duk dan wa akeyi?, dan ita wadda ba'aso ta sani ne, to ja'irar yanzu taji komai ta kuma san wace ita. saboda haka kamar yanda muka alƙawaranta cewar duk ranar da Mairo ta girma mu kai ma ta aure to za ki faɗa mana inda iyayenki su ke mu maidaki garesu, to kana taka Allah na tasa ga shi yanda muka tsara ba hakan ce ta kasance ba. saboda ni anawa ganin tun wuri a gobe-goben nan ki shirya mu wuce mu tafi inda kika fito, dan ci gaba da zamanki anan babu abin da zai jawo miki fa ce tsangwama daga mutanen gidan nan da jama'ar gari...Adamu kana ina?". Malam ya ƙara amsawa,"gani nan Yagana". "to me kace?". yace,"ehh hakan shine dai-dai, wannan shi ne ma abin da ya kamata ayi tuntuni". Yagana ta kaɗa kai,"yauwa, to yanzu ke ina ne garinku?". "ni ƴar ƙasar Qatar ce". "ina ne kuma haka?". Kabiru yace,"can ƙasar larabawa ce, daga inda nake zaune bamu da nisa". Yagana ta wani zabura ta dafe ƙirji tare da waro ido,"kai dan manzon Allah?". "ƙwarai kuwa Yagana". Amadu ya faɗa. sai ta waiga ta dubi Kulu,"Kulu da ma wannan hasken naki na larabawa ne?, kai jama'a ni Rakiya inda raina nata ganin abin mamaki, to garin ya haka ta kasance, me ya jefoki wannan ƙasar tamu?". Malam da ke gefe ya bata amsa da,"Qaddara". Yagana ta jinjina kai da cewar,"ƙwarai sai ita ɗin kuwa, amma abin da mamaki, Kulu to dama kuna da ƴan'uwa ne anan ko kawai kurciyar da aka miki ne ta saukeki anan bichi?". Malam ya ƙara ce ma ta,"ai Yagana wannan kiristan ɗin da Mairo ta faɗa hannunsu san da ta ɓata shi ne yay ma ta cikin". da Yagana ta doka wani uban salati sai da ƴan tsakar gida suka ji, ta zabura ta miƙe tsaye tana karkaɓe zani, "kirista!, yo dama ke kirista ce shi ne har da danƙarawa kanki Hauwa saboda son zuciya. amma kuwa wannan mata ba ki ji daɗin halinki ba, yo ni fa ince ya za'ai musulman ƙwarai suka kasa amsar ƙaddara dan ubangiji ya jarabci ƴarsu da yin cikin shege, wallahi tun a lokacin lissafina ne ya kunce amma nayi ƙoƙarin in ce muje gaban iyayen naki naji ko islamiya ce basu je ba, ashema me ɗungurungun musuluncinma babu bare har ai imani da ƙaddara, taɓɗijam ashe jikar Yesu ce ke". sai da tayi shiru sannan Malam ya sami damar cewa,"Yagana bafa wai ita ce kirista ɗin ba, shi wanda yay ma ta fyaɗen shi ne kirista". tayi guntun tsaki,"to me maraba?, kirista ai ɗan uwansa kirista kamar yanda musulmi sai ƴar'uwarsa musulma". ta fuskanci Kulu da cewa,"to kinga Allah tun da dai anzo ga haka, ki tashi tun daren nan ki kama hannun ƴarki ku tafi, tun ubanta beji kuna n