NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 126 of 223

e harbawa tamkar zuciyarta zata faso waje, murya a cikin kuka tace,"ko ba komai ni mahaifiyarki ce, ki tuna wannan a mahanga ta addininki...". ban bari ta ƙarasa ba na shaƙi wuyanta lokaci ɗaya ta kama kakari,"bari na ƙarasaki tun yanzu, ke har kina da bakin da za kiyi min nasiha, ki gama jin daɗin iskancin naki sannan kizo kice za ki min nasiha, gaba ɗaya ba ki fi ƙarfin na kiraki da karu...". sauran maganata ta katse, jina da ganina suka ɗauke na wucin gadi, cikin sakannin da ba su haura ɗaya ba na haɗa hankalina da tunanina na dawo cikinsu, sannan na buɗe idanuwana tangararau suka bar ganin ƙyallin wutar da ta haska a cikinsu, duk ta dalilin azababban marukan da Ya Kabiru ya bani ta duka ɓangaren fuskata, da kuma wanda Ya Amadu ya dawo min da shi bayan ɗaukewar na Ya Kabiru, sai na gigice gaba ɗaya na rasa makama, sai dafe kuncin nawa nayi da nake jin kamar wata jijiya acikinsa na neman tsinkewa. "Ya Amadu har sau nawa za'a dukeni ka hanani yin kuka,? mene laifina a ciki dan na kira matar da ta lalata min rayuwa da sunan karuwa, yanzu shikenan kowa zai tsananeni, kowa zai koma kirana da shegiya..kuma wallahi ba zan janye ƙudurina akanta ba ko da me za'a min, sai dai in Allah ne ya ɗau raina, kuma na faɗa ɗin Karuwa, ai idan batayi karuwancin ba zata samar da ni ta ƙazamar hanya ba". ƙaton kutufo ya kuma sauka a bakina, halshe da haƙorina suka haɗe wuri ɗaya, jini ya shiga zuba. na ɗago ido na kalli Ya Kabiru, huci yake da jajayen idanuwansa da suka sauya launi su ka rikiɗe zuwa na wata halitta a cikin halittar dabbobi. da kakkausar murya ya ke faɗa min,"billahillazi la'ila ha'illahuwa idan bakinki ya ƙara furta wata magana anan wurin sai na sa ƙafa na mitstsikeki dan ubanki, shashasha mahaukaciya....Amadu saketa". kallonsa kawai na ke da mamaki nace,"dole kace nayi shiru tun da kai igoyoyin uku na aure ne suka samar da kai, ba zaka ji irin zafin da ni nake ji ba, shi yasa ba zaka damu ba, to wallah a yau banga me hanani magantuwa ba duk faɗin duniyar nan". maganar na ke ci gaba da faɗa a san da tuni yasa ƙafa ya fyaɗeni na zube ƙasa, kan yasa hannu ya jani kamar wanda ke jan wasu kaya har zuwa zaure, ya buɗe ɗakinsu me uban duhu babu wutar nepa, ya jefani a ciki sannan yasa mukulli ya rufe. duk kururuwar da nake akan ya buɗeni na fita ɗaukar fansa amma sam yaƙi, illa ma buɗewa da yay ya dawo ciki ya ɗaureni da igiyar shanyar da ya ciro. nabi bayansa da ido ina kallon yanda yake goge ƙwallarsa. amma ban fasa jaddada masa ba, sai dai idan bana numfashi ne kaɗai zuciyata zata ƙi aiwatar da ƙudurinta akan Akila da Tosin, insha'Allahu sai nasa sun zubar da hawaye fiye da wanda nake yi, wannan alƙawarina ne, kuma nasan wace zuciyata ba zata taɓa rissina akan hakan ba. daga can zaure na jiyo Yagana ta shigo gidan tana faɗin,"ai wallahi tunda Adawiyya taje tace min wai Mairo tayi shaye-shaye tana ta wasu surutai marasa kan gado nasan zai yi wuya idan ba SIRRIN ƁOYE ne ya fito fili ba. oh oh na shiga uku ni Rakiya, a garin ya hakan ta faru?, wa ya sanar da ita cewar ita shegiya ce duk wannan rufa-rufar da muka dinga yi, kai munafiki bai ji daɗin halinsa ba, dole sai da aka samu wanda ya faɗawa yarinyar nan ita ƴar zina ce, to Allah ya isar ma ta, ke kuma ki bar kuka muje ɗaki...ina Mairon ta ke?". "shegiya kuma Ƴar zina!". kalmomin suka ƙara maimaituwa a cikin kunnena, "Akila kin cuceni". na fada tare da kifa kaina akan gwiwoyina ina fashewa da matsanancin kuka. duk bidirin da ake tsakanin Yagana da Ya Kabiru akan ya fito da ni ina jinsu. *Plss Comment&Share.* [7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *HalimaAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* _Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._ *33)* Yagana ta gyara ɗaurin zani ta gyara zaman mayafi ta fuskanci Kabiru da kyau sannan tace,"Kabiru, ka buɗe min ɗakin nan yarinyar nan ta fito, shin da wanne kuke so taji?, memakon ku lallasheta sai a ƙarke da kulleta, tsakani da Allah wannan ai ba kyautuwa bace...ka buɗe dan Allah". ya kaɗa kansa ya juya ya fi ce bai ce da ita komai ba, tabbas ya riga ya sani a irin taurin kai na Mairo kamar kafirunal ula babu abin da zai dakatar da ita daga abin da tai niyya a wannan lokacin, shi yasa ba zai buɗeta ba ko da kuwa zata mutu aciki ne, in dai taurin kaine ba ita kaɗai ta iya ba, shi ma ya iya, kuma zai iya rantsewa ya takata ya dame. ganin ya fice Yagana ta juyo cikin gida jiki a mace kamar wadda akaiwa duka, ba don komai ba sai dan yanda cikin ƙanƙanen lokaci wai har wannan maganar ta baza gari dan abin takaici. ƙofar gidansu maƙil jama'a kowa na tofa albarkacin bakinsa, hatta Malam da ya fito zuwa masallaci kasa fita yay sai dawow
🏠