NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 124 of 223

a Mairo tasan cewar ita shegiya ce, ta san da cewar an samar da ita ta hanyar zina ne bada aure ba, ta kuma san cewar ni da Marigayiya bamu ne iyayenta ba. lokacin da bana nunfashi kaɗai na yarda Mairo tasan ita ƴar gaba da fatiha ce ita, amma ba yanzu da na ke raye ba, saboda haka batun aurenta da Kabiru da kike magana na soke shi, insha'Allah idan Allah ya bamu tsawon rai gobe zan ɗaura ma ta aure da Al-Mustapha, in yaso daga baya yasan yacca yay ya sanar da iyayen nasa". sai kuma ta ƙara fashewa da kukan da ya fi na ɗazu, a yanzu kuwa muryarta ta gama dakushewa, domin da ƙyar ta ke fita,"a'a Malam, aurenta da wanda kake ikirarin zaka bata shi ma kuskure ne. idan har da gaske ɗan gidan Major Tosin ne to babu aure a tsakaninsu, domin Major shi ne silar zuwansu duniya ta ƙazamar hanya, hanyar da ba aure". sai naja ƙafata da naji ta daskare, na jingina da jikin garun ƙofar ɗakin, gaba ɗaya kunnuwana sun kasa yarda da abin da suka ji, na sulale na zube a ƙasa. muryar Kulu kuma naci gaba da shiga kunnena,"Major Tosin Afafa shi ne mahaifinta, dattijun da babu imani a cikin zuciyarsa, shi ne silar komai Malam, shi ya zama mafarin koma...na shiga uku ni Akila, ban san ta yanda Hussaina zata karɓi cewar ita ɗin shegiya bace". tamkar saukar tsawa akan dutse cikin duhun dare, tamkar kaɗawar guguwa acikin iska, haka nake jin maganar acikin kaina. _Mairo shegiya ce, Mairo ƴar gaba da fatiha ce, Mairo an haifeta ne ta hanyar zina, kuma wani kafiri can daban shi ne ubana, ni Mairo!._ sai kawai na tsinci kaina da ƙwalla wata uwar ƙara tare da buga kaina ajikin garu, domin na farka daga wannan mummunan mafarkin mara kai mara gindi. *Comment&Share.* [7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE* _Shafin Gaba Ɗaya Sadaukarwa Ne Ga Masu Sharing Wannan Book Ɗin, Alkhairin Allah ya isa gareku._ *32)* dukkan wata ma'ana ta tashin hankalin ta gaba fitowa ajikina, a yau ɗaya rayuwata ta sauya, tabbas idan aka tambayeni tarihin rayuwata da wannan shafin zan fara, ta kansa zan soma. yanayin da nake ciki da ni da wanda aka tsamo daga cikin teku bamu da maraba a wajen jiƙewa illa shi ruwa ne ya jiƙa shi, ni kuma zufa ce ta jiƙani sharkaf. tun da na daki kaina da bango naji zafin a jikina na tabbatar da abun da kunnuwana suka ji ba'a mafarki bane, zahiri ne. na koma kamar wadda aka sassaƙa aka dasa a ƙofar ɗakin Baba, babu motsi sai numfashin da shi ma na ke zuƙo shi da ƙyar, idanuna sun kaɗa sunyi jajur. murfayen idanuna su ka haɗe su ka rufe su na fatan daga haka shikenan ba za su ƙara buɗewa ba su gansu a wannan duniyar ba. hoton rayuwata gaba ɗaya ya shiga haskawa cikin idona, yayin da agefe ɗaya maganar Kulu ke ci gaba da shiga cikin kunnuwana. "Malam in har dai wannan Sojan da ƙasa ke ji da shi ne Major Tosin Afafa to wallah ba zan maka ƙarya ba shi ne mahaifinta, Malam shi ya yaudareni da cewar zai musulunta bayan ya gama dasa soyayyarsa a zuciyata at long last yazo ya yaudareni yaci amanata yay min ciki, a gabansa na haifesu, akan idonsa, da shi aka karɓi haihuwarsu, amma saboda zalunci bayan zuwansu duniya yace ba zai iya karɓarsu ba. shi ne har ya ɗaukesu wai zai kai gidan marayu suyi rayuwarsu a can gudun kar sunansa ya ɓaci, jin hakan yasa na ƙanƙame Hussaina da ke hannuna dan Hassan na hannunsa a lokacin, nace idan ya rabani da namijin ba zai rabani da macen ba, ba zai yiwu duka su tashi a tutar kafirci ba, bai bi ta kaina ba, balle ya tausayawa halin da nake ciki yasa ƙafa ya wuce ya barni. shi ne har ku ka zo ku ka sameni a  wannan asibitin, Malam Hauwa ba shi ne sunana ba Akila shi ne asalin sunana, ni ba ƴar nigeria bace ƴar ƙasar Qatar ce, mahaifina shi ne sarkin ƙasar. yanzu ban san ya zanyi ba, ban san da wani irin kalami zan faɗawa Hussaina ta yarda cewar bada son raina na haifesu ta wannan hanyar ba". kukan da ya ci ƙarfinta yay dai-dai da ɗaukewar wuta a zuciyata, sai kuma wasu hawaye na daban masu zafi suka shiga sauko min, kukan da ke riƙe a bakina ya suɓuce, bakina kawai naji yana furta,"Ya Allah kabi min hakkina akan Akila da Tosin, ba zan taɓa yafe musu ba, dan sun cutar da ni...Allah ka ɗauki raina na huta da rayuwa ma gaba ɗaya, karka bari na ƙara kwana a duniyar nan dan zan iya ɗaukar...". maganar ta katse daga bakina dalilin toshe min baki da Ya Kabiru yay, wanda ban san da zuwansa ba sai ganinsa nayi tsugune a gabana. "me yay zafi haka?, Mairo rashin uwa ai ba hauka bane. dan kawai kin rasa mahaifiyarki sai hankalinki ya nemi ya gushe, har ta kai kina furta kalaman da za su fidda ke a addininki, haba karki raunana imaninki mana. ƴaƴa dubu nawa ne suka rasa mahaifiyarsu, ni ma fa kaina bani da mahafiyar nan a raye...". sai yay shiru a san da Baba da Kulu suka fito daga ɗakin, jikinsu a sanyaye, ta gefen idon na ke kallonsu. ya miƙe tsaye daga gabana, ni kuma Baba ya kira sunana,"Mairo". ban amsa ba sai jan hanci da nayi. "Mairo tashi muje daga ɗakin Gwaggonki". nace da shi,"Baba ka kirani da sunana na ainihi mana. domin
🏠