NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 123 of 223

h sai ya nemi wani yay masa bitarsa. kuma bai manta ba da faɗin Malam da ke ce masa,"duk lokacin da ka ji wani al'amari ya cunkushe maka, ka kasa nemawa kanka mafita, to ka karanta Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahlan, wa anta taj'alu-l-hzana idha shi'ta sahlan. ma'ana Ya Allah! Babu wani abu mai sauƙi sai abin da Ka sanya shi ya zama mai sauƙi, kuma Kai kana sanya tsanani idan Ka so ya zama sauƙi". tashi yayi yay azamar shiryawa ya suri keys ɗinsa ya fita, kowa na zaune a parlo a san da ya sauko ƙasan, bai kula kowa ba ya fice sai raka shi da idanuwa da suka yi da mamakin sauyawar da yay cikin kwanakin nan. **** kamar yanda Kulu bata so fitowata ba, haka nima ba'a son raina na fito ba, dan har cewa tayi zata je taiwa Baba magana nace babu ruwanta karta shiga lamarin da bai shafeta ba, na riga na amince ba auren dole za'ai min ba. a zaure muka haɗu da Adawiyya itama zata fita ta tambayeni,"ina za ki da tsakar rana haka?". a harzuƙe nace da ita,"ki shaƙeni sai na faɗa miki". "Allah ba ki haƙuri". ta faɗa tana kyaɓe baki, na harareta da faɗin,"da haƙurin ta mutu sadaƙar nawa kika bani, ni kaucen a hanya ko na bi ta kanki wallahi". babu shiri ta kauce na wuce. daga gaban gidanmu na hango arniyar motar tasa baƙa sai sheƙi ta ke, na ƙarasa inata faman ɓata raina kamar na kurma ihu. da kansa ya buɗe min wai na shigo ciki, ni kuwa nace babu inda zan shigo ni ba ƴar iska bace, idan yana iya fitowa ya fito, in bai iyawa na koma becouse i have alot to do. murmushi yay sannan ya buɗe ya zago daga ɓangarensa zuwa inda na ke, da yake da yamma ne idon mutane duk a kanmu, kasancewar an daddawo daga kasuwa, kuma duk banji daɗin tsayuwar ba, na haɗiye haushina nace da shi,"faɗi da sauri". oho na manta ba bahaushe bane, sai da naji yay shiru na dube shi ina zabga masa harara sannan na tuna, dan haka cikin yaren da zai gane me nake nufi nace,"yau kuma ina sarƙan cross ɗin?". sai yay murmushi yace min,"ina Al-Mustapha ina sarƙan cross, sai kace wata Gift a baya".ya faɗa da sigar tsokana, dan haka na jiyo ina ƙara haɗe fuska cike da tsiwa nace,"ni kar ka ƙara dangantani da wani Gift idan ba haka ba kuwa zanyi maka ɓarin mahaukaciya, wa ya san ma da zuciyar da ka bar ƙazamin addinin naku, Gaskiyar Yagana ma da tace Uwar bari ka gani". a wannan karan kam siririyar dariya yayi kan yace,"ai ba saboda wani na karɓi musuluncin balle asa naji haushi na sauya ra'ayi...ba wannan ya kawoni ba, zuwa nayi ki bani shawara saboda ke ɗin me kifin basira ce". nace,"aikuwa dai kayi farar dabara, dan babu abin da zai sa na bika na zauna acikin arna, saboda haka ka san da cewa in an ɗaura a gidanmu zanci gaba da zama, idan haɗuwarmu da kai ta zama dole ma ke gaisawa ta waya". "idan baki bar min tsiwa ba zan cafe wannan ƙaramin bakin nan naita kissing ɗinsa har sai jamaa sun taru a wurin nan". na sa ke ɓalla masa harara nace,"iskanci dama ai ba baƙonka bane". yana kallona da wani makirin murmushi yace, "nan gaba kaɗan ai za ki so iskancin kema". wani haushinsa ya tuƙeni, dan haka na bar masa wajen na ɗauki hanyar gidan Yagana, saboda kar ma na koma gida Baba ya saito ni, yau gaba ɗaya ma sallah ce kawai ta ke fito da shi waje, gidan kuma ba kowa Kulu ce kawai, Innata da Inna Zulai duk sunje anguwa yara kuwa duk sun tafi makaranta, sai Sadiya da Adawiyya da ban san inda tsinannan yawonsu ya kaɗasu ba. ban dawo gida ba sai bayan an idar da sallar magriba, har lokacin gidan shiru babu kowa, Kulu ma ba ta ɗaki sai nayi zaton ko banɗaki ta shiga. dan haka na wuce ɗakin Baba sai dai ina zuwa ƙofar ɗakin na dakata da shiga a sanda naji murya Baba sama-sama kamar yana faɗa. naja burgi na tsaya jin ya ambaci sunan Kulu yana cewa,"Hauwa wannan hukuncin da kika yanke kan Mairo da Kabiru babu inda zai je, ba kuma shi ne samun mafitarki ba, illa ƙara dagula lissafin komai, abin da ake gudu kuma yazo ya faru, saboda haka ki kauda ido ki bari na aura mata Al-Mustapha kawai, zuwa wannan lokacin da bayan na mutu sirrin komai zai bayyana zata fi samun sauƙi, tun da da aure a kanta, akan wannan lokacin da take ciki...banda an sami tsaiko daga ɓangaren Al-Muspha da tuni tun azahar na jima da ɗaura musu aure". cikin matsanancin kuka da muryar da ta fara dakushewa Kulu tace,"Malam ni kaina na gaji da ɓoye wannan sirrin, duk da cewar har yanzu bana so Hussaina ta san gaskiyar komai dan bana so rayuwarta ta ƙuntata, amma bani da yanda zanyi, ita gaskiya duk inda aka kai ga ɓoyeta watarana sai ta bayyana kanta...kayi haƙuri ban taɓa ƙin maganarku ba, amma ba zan iya bari Kabiru ya rasata ba, ba zan iya zuba ido inaji ina gani a ɗaura ma ta aure da wani ba bada Kabir ba, na riga nayi masa alƙawarin aurenta, ba kuma zan iya saɓa wannan alƙawarin ba". sai tayi shiru, Baba kuma ya ɗora da faɗin,"to ni ban yarda ba, ban kuma amince ba in har na isa kamar yanda kike cewa, in har ina da iko akan ƴarki to ban amince da wannan alƙawarin naki ba, ki ɓalla shi. dan sai bayan raina kaɗai na yard
🏠